Sashe 105
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashin hankali zaro idon mutumin yayi kafin ma yayi magana, Jehan ta sa kai ta wuce ta bar wajen, da sauri mutumin ya leƙo da kan sa waje yana kallon ta, mamaki ya sa ya kasa komawa cikin ɗaki, a ransa yana faɗin "wannan yar yarinyar dai a shekaru da wuya ta wuce sha bakwai tsawo ne kawai gare ta, shine zata cemin katon banza, anya wannan a gaban iyayen ta ta taso kuwa, anya ta samu tarbiya, to wlh ba zan zauna a hotel ɗin nan ba, basu san darajar costumer ba, har ma'aikaciya tana da bakin cewa costumer ba zata yi masa abun da yake so ba, tab lalai da sake" da wannan tunani ya koma cikin ɗaki ya ɗauki waya ya sake kiran Ibraheem,
Ita kuwa Jehan kai tsaye wajan sauran ma'aikatan tan restaurant É—in ta nufa dan ta tambaye su ko shine aikin da suka zo yi kenan wato wankin kayan costumers.
Da sallama É—auke a bakin ta ta karisa wajen da sauran ma'aikatan ke zaune, har suna rige rigen amsa mata sallamar nata, sunga kyakyawa, dan Jehan akoi farinjini na fitar hankali, duk in da taje sai an so ta, haka itama Rimsha
Sai wani washe baki ma'aikatan suke suna É—aga mata gaisuwa, ita kuwa kara É—aure fuska tayi kafin tace "dan Allah zaku iya faÉ—a min aikin me muka zo yi a nan?" Kallon kallo suka fara yiwa junan su, lallai wato wanna ma bata san aikin da ya kawo ta nan ba tab akoi cakwakiya.
Ɗaya daga cikin sune ta miƙe ta dafa kafaɗar Jehan ta fara yi mata bayanin irin aikin da ya kawo su nan "Wanke wanke, shara, mopping, kai wa mutane abinci idan suka zo ci, sanna kaiwa yan ɓangaren hotel abinci room nasu idan suka buƙata, wasu costumers ɗin zasu buƙaci mu musu wanki su biya mu, wanna ma yana daga cikin aikin mu, sanna dole ki san ta yadda zakiyi wajen kontarwa da costumers hankali har suji daɗin wanna restaurant ɗin gobema su dawo cin abinci, dole ki koyi sakin fuska da murmushi dan jawo ra'ayin costumers su sake dawowa cin abinci, danna dol.... Bata kai karshen maganar ba Jehan ta dakatar da ita ta hanyar cewa "Ya isa haka, da yake sayata sukayi ba ai dole su ce nayi kaza nayi kaza, to wlh ni idan ba kaiwa costumers abinci ba, ba wani aiki da zanyi a nan, dan ni Ibraheem bai cemin da Hotel ba iya restaurant yace min, kuma a restaurant ɗin ma iya serving abinci kawai ya cewa iyaye na, dan haka iya shi kawai zan yi" ta kai karshen maganar tare da juyawa ta bar wajen ta nufi wajen girkin restaurant ɗin. Mamaki ya hana sauran ma'aikatan magana, yau sun haɗu da abun da yafi karfin su.
A hanyar ta na zuwa wajen girkin restaurant ɗin ne suka haɗu da Ibraheem, rai sa a matuƙar ɓace, cikin tsawa yace "Ke zonan!!" Ba musu taje "Ke dan uban ki baki da mutunci ko? Baki da albarka ko? Mu rufa miki asiri mu ɗauko ki mu kawo ki nan dan ki samu abun da zaki rufawa kan ki da iyayen ki asiri, shine bai miki bako? Yanzu dan baki da kirki baki da albarka costumer kikaje kikayiwa ɗiban albarka haka eh? Keda muka kawoki dan ki jawo mana costumers shi ne zaki kora mana wayan da muke dasu ko? To wlh baki isa ba dan uban ki, tun wuri kije ki bawa mutumin nan hakuri ki karɓo kayan sa kizo ki wanke idan kina son zaman lafiya kinji na faɗa miƙi!!!"
Tsare sa da wayan nan dara daran idon nata tayi babu ko kyap tawa, har sai da ya kai aya a maganar tasa, sannan gently tace "Ba zan yiwa wani katon banza wanki ba, dan ba wanna aikin mukayi da kai ba, masu sayan abinci kawai zan kaiwa abinci idan sun zo saya, bayan su ba wani aikin da zanyi, sai kuma maganar uniform karka sake min maganar sa dan ba zan saka ba" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi in da take da niyar zuwa wato wajen girkin su.
A fusace Ibraheem ya bi ta ya je ya sha gaban ta, dan yana takamar ya ranta mata 500k ne yasa ya É—aga hannu a fusace zai mare ta, cak ta rike hannun sa, cikin fushi ta É—aga hannu zata mare sa, sai kuma ta fasa saboda ta tuna da cewa ko ba komai ya taimaka musu ya basu aron kuÉ—i gashi yau ana yiwa mum aiki saboda shi, dan haka bai kamata ta masa irin wannan rashin kunya ba.
A hankali ta sake masa hannu sa tare da sauke nata hannun cike da ɓacin rai tace "Ina ganin mutuncin ka amma kana neman ka kaini bango, ka kiramin ogan naka zanyi magana da shi, domin kuwa bashi da iko dani, daga yanzu ba zan sake yin magana da kai ba, da ogan ka zanyi magana, dan na lura duk wanna hargagan da kake kana yin sane dan tsoron kar ogan ka ya maka faɗa a kan ban sanya uniform ba dan sauran su, to ni ka kiramin shi bari na masa bayani da baki na, a kan cewa ba zan saka uniform ɗin ba, kuma iya kai abinci zanyi, sanna shawara da zan baka shine, ka daina jin tsoron wani ɗan adam kamar kai, kaji tsoron Allah kaɗai, idan kana jin tsoron Allah tofa babu wani ɗan adam da zai baka tsoro ko ya maka wani abun da Allah bai kaddara maka ba, bana son hayaniya amma kana son sani cikin ta, bana son yawan magana shima kana sani yi, please ina ganin girman saboda taimakon da ka mana, dan Allah ka fita harka ta!!!" Tana kai karshen maganar ta wuce ta bar Ibraheem yayi mutuwar tsaye a wajen, yau ya ɗauko wadda ta fi karfin sa
Share fisabilillah ðŸ‘
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪
💞Star Lady💞
TRIPLET'S💞
💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)
*GargarÉ—i*
_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_
WhatsApp me for more information 09162620621
Episode 34-35
Tana kai karshen maganar ta wuce ta bar Ibraheem yayi mutuwar tsaye a wajen, yau ya É—auko wadda ta fi karfin sa.
Nima dai Jehan tafi karfi na dan haka mu leƙo su Jelly mu dawo.
💞KADUNA💞
Yau dai Hajiya Turai tace ba zatayiwa Jelly wanka ba, dan Jelly ta girma, yanzu ta doshi 15 years amma ba abun da ta iya, saboda daddyn ta bai koya mata ba, komai shi yake mata da kan sa, bata iya komai ba sai shagwaɓa, sai dai daddy bai barta haka ba ya koya mata karatun Alqur'ani mai girma dana boko, Hajiya Turai tayi tunanin kodan saboda ciwon da take ciki ne yasa ta manta har da yadda ake wanka da sauran su, sai dai bata san dama already Jelly kam haka take ba, ciwon ne ya kara haukatata, ta zama asalin shagwaɓaɓiya haka, gashi tun da tazo gidan Hajiya Turai ke kokarin koya mata yadda ake wanka da sauran abubuwa, amma duk a banza domin kuwa ba wani abun da ta mai da hankali wajen koyan sa sai shirme, shi kuwa Abbo shi yake kara ɓata abun, dan kuwa idan Hajiya Turai tace ta koyi abu da kan ta, sai Abbo yace a'a dan Allah a kyale ta, taji da ciwo ne ko kuma taji da takura dan haka su kyale ta ta sha iska, hakan yasa Hajiya Turai wato Ummi bata takura mata da lallai sai tayi abu.
Yauma kamar kullun suna zaune saman dining table suna breakfast suna hira sama sama.
"Abbon Nawid ina son asamin baby a school dan ta É—an koyi wasu abubuwa" cewar Ummi,
Nawid ne ya karɓi zancen da cewa "Eh Ummi haka ne, in ta shiga school zai taimaka mata wajen kara tunatar da ita abubuwan da ta manta a baya, dan ina da tabbacin a baya kafin wannan accident ɗin ya faru yarinyar nan tayi karatu, idan kika lura da yanayin jikin ta, ni wlh ina ganin ba yar gidan talakawa yar malam Shehu wadda aka gaji da ita saboda rashin abinci kamar yadda kuke faɗe bane, da ganin ta Allah kin san wanna renon madara da su Ice cream ce" shiru Ummi ta ɗan yi kafin tace "Haka ne kuma, amma fa ni ina ganin kamar ba yar nan Kd ba ce" Nawid zai yi magana Abbo ya riga sa da cewa "A'a ba za'a sata school ba, kuma ku dai na wani maganganu a kan ta, mu dai Allah ya bamu ƴa kuma mun gode, dan haka ya isa haka, makaranta kuma ba zata je ba, saboda laluran ta ko taje school ba wani abun da zata fahimter kawai ku kyale ta a nan ɗin" shiru Ummi tayi tana tunanin zancen Abbo gaskiya ne, karsuje a garin hira da tone tone har su tono wace ce Jelly suyi sanadiyyar barin ta wajen su, dan haka garama kawai su kyale ta kar ma su sata a School taje ta haɗu da wanda ya santa yaje ya faɗa wa iyayen ta suzo su ɗauke ta kawai a banza gara suyi shiru.
A ɓangaren Nawid kuma tunani yake akan me ya sanya Abbon sa yake yawan damuwa da Jelly haka ne, why kullun baya son a takura mata, baya son gaskiya a kan ta, abun ya fara yawa, amma da yake Ummi soyayyar da take wa Jelly ya rufe mata ido bata fahimci illar abun da Abbo ɗin keyi ba.