← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 126

Sashe 101

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wanna yanayi Mustapha yazo ya same su, dan yanzu yana zuwa suyi ta hira da duna sun zama kamar friend, yana zama Rimsha ta miƙe tana faɗin "Ina zuwa Ayla bari na je ɗaki na ɗauko apple na najiya" to kawai suka amsa mata da shi, sannan ta wuce ta bar wajen, su kuma suka ci-gaba da hiran su.

Tazo zata shiga ɗakin nasu, sai taga yar siririyar hanya daga ɗan gefen ɗakin nasu, Rimsha da karambani tace bari ta leƙo taga menene a wajen, ɗan karamin hanya ne, ga wani fitinanniyar wari bala'i dake fitowa daga wajen, haka ta kutsa ta wajen tare da toshe hanci ta tana lallaɓawa saɗaf saɗaf kamar wata ɓarauniya har ta kai karshen hanyar, ba tare da su duna sun ankara da ita ba, suna ta hiran su

ko da taje karshen hanyar sai taga ba wani abu a wajen sai wani katanga mai É—an tsawo daya musu katanga, ma'ana ya raba su da wan can part É—in.

Kamar a kafarki taji kafar ta ya tsunduma cikin wani abun, cikin tsoro a hankali ta kai kallonta kasa, nan taga wani irin jini mai bala'i kauri da yauki, cikin jinin duk guda gudan naman jikin mutun, ta wani gefen ma har da kashi ɗan adam, ɗago idon ta tayi a razane ta kalli gefe gefen wajen da kyau, gaba ɗaya kashin kwarangal na mutane ne, ga kuma naman jikin mutun wadda bai gama murmushe wa ba, kasan wajen wani daskararren jini ne mai balai wari, ga kuma wani sabon jini na malala a saman wannan daskararren, da alama yanzu ake zubar da wannan jinin, wani mugun tsoro ne ya dira mata a ranta lokaci guda, nan take jikin ta ya fara ɓari, wani irin wahalallan yawu ta haɗiye da kyar, nan take idon ta ya rena fata, wani gumin wahala ya fara karyo mata.

Amma saboda fitina irin na Rimsha sai da ta kama katangar nan har da yar tsallen ta, ta leƙo, dan ta dage sai taga daga ina jinin nan ke fitowa.
Nan fa idon ta suka gane mata abun da kwakwalwa ba zai É—auka ba, wani mahaukacin ihu ta fasa tare da sakin katangar, kamar zararriya haka ta bazama ta fito daga wajen, a guje su duna sokayo kan ta, saboda ihun ta da sukaji

Tun da yaga ta in da ta fito yace shikenan kuma mawuyacin abune yau Rimsha ta rayu a gidan nan, ita kuwa sai ihu take kamar wata zararriya, tunani duna ya shigayi ya zai yi ya kuɓutar da Rimsha daga sharrin su Gujungu, dan yasan definitely wayan nan magicians dake wajen zasu biyo bayan ta dan sun jiyo ihun ta, kuma tabbas bazasu barta da rai ba, dan ba'a ganin sirrin su a rayu.

Sai ihu Rimsha take da alama ta fita hayyacin ta, dan ta razana sosai da abun da ta gani, jin takun sahun jiga jigan magicians É—in ne yasa duna kara tsorata dan yana ji a ransa sai dai yau ya mutu amma ba zai iya bari su É—auki Rimsha ba, takun magicians É—in sai kara kusan tosu yake, duk in sukayi taku É—aya, sai kasa da katanga sun girgiza saboda girman su da larfin bala'i irin nasu.

Sai zaro ido duna yake, kasan cewar yasan duk bala'i sa su Gujungu wato masu gadin fadar Queen sun fisa bala'i, ko su Barbushi basu isa su tinkare su ba bare kuma shi, banda Queen ba mai iya ja da su Gujungu a gidan, manya manyan jiga jigan magicians ne masu ji da larfin É—aga mota kamar yar baby da hannu É—aya, tsabar girman jikin su da karfin su, idan suka taka kasa, sai katangar dake wajen ta girgiza, hakan yasa mafiyawancin É—akunan gidan da dafaffun karafuna a kayi su katanga É—ai É—ai ne a gidan, dan katanga ba zai iya É—aukan karfin takun su Gujungu ba rushewa yake.

Jin sun kusa isowa in da suke ne, dan ga alamar sautin takun kafar su da kuma amshin kasa nan ya kara karuwa, tsabar tsorata duna bai san lokacin daya batar da Rimsha da tsafin saba, a baya yayi alƙawarin ba zai sake amfani da tsafin ba, saboda Rimsha ta nuna masa tana tsoro kuma bata son hakan, idan har zai ci-gaba da amfani da tsafin to gaskiya ba zata ci-gaba da yi masa magana ba, shiyasa yace mata ya dai na ba zai sake ba, amma yau bashi da zaɓi dan Rimsha ta taɓo gidan rina ta tsokalo gindin dodo bala'i da yafi karfin su, shiyasa ya ɓatar da ita gaba ɗaya daga wajen

Bayyanar su Gujungu a wajen ba karamin haukata kwakwalwan yan gidan gaba É—aya yayi ba, banda duna da ya saba ganin su, ba wanda kwakwalwan sa bai haukace ba a gidan sai Mustapha, saboda su Gujungu sun fi su Barbushi a muni uban ni su Barbushi ne, sanna a girman jiki sunyi biyun su Barbushi, sai dai basu da tsawo, gajeru ne, sai bala'i faÉ—i shiyasa kofar shiga wanna wajen nasu ma faÉ—in sa ya kai 2 miter dan su iya shiga da fita, amma duk da haka a takure suke, saboda girman jikin su, hancin su kawai ya kai girman kan bil adama, idon nan nasu bazai ganun wa É—an Adam ba, ka fafun sunan ya kusa faÉ—in fridge, munin su kawai zai iya sanya É—an adam zuciyar sa ta buga ya mutu, babu ko É—igon imani a tattare da fuskokin su bare tausayi, basu fitowa kullun suna wanna part din nasu suna aikin sarrafa wa Queen ganganjikkin É—an Adam da sauran ayyuka.

Tun kafin su iso daman duna ya koma asalin halittar sa na Magicians, Ayla da kausar tuni sun sume a wajen, shikuwa Mustapha, kamar mahaukaci haka ya bazama yayi É—akin da ya samu a buÉ—e ya shege, haka sauran yan gidan da basu suma ba, suma duk É—akin da suka samu kawai shiga sukayi dan cetan ransu, kuma basa hayyacin su.

Duna na tsaye har suka ƙariso wajen, Gujungu ne ya fara tambayar ina wadda ta leƙa su take, cikin yaren su na matsafa, da muryan sa mai doɗe kunnen ɗan adam ya daina ji gaba ɗaya, nan fa duna ya fara musu kame kame na cewar bai ganta ba, wani mahaukacin kururuwa Gujungu ya sa wadda yayi sanadiyar tada guguwa mai karfi gaske bakin kirin kamar bakin hayaki na itacen damuna, jijjiga jikin sa yayi tare da ɗaga kofatan kafa ɗaya zai sauƙe a kan Ayla, duna yayi saurin kwanciya kasa ya shiga tsakanin su, kafar Gujungu ya sauka ma shi a cinyoyin sa ta baya

razanannen ihu mai bala'i sauti duna ya sake mai razana kwakwalwar duk wani halitta mai rai, kan kace me cinyoyin duna sun rugurguje har kashin sa sai da suka rugurguje saboda takun kafar Gujungu fa ba wasa ba.

Wucewa su Gujungu sukayi suka nufi cikin gidan dan neman Rimsha, shi kuwa duna sai ihu azaba yake na cinyar sa da ta daddage, haka suka wuce zuwa tsakar gidan dukkan wadda suka samu a kan hanya ya suma bi ta kan sa suke su wuce, duk kuma wanda suka sauƙewa wanna gofaton kafar nan tasu, tofa namar sa daga'daga yake ya daddage, wasu ma har lumewa cikin kasa suke idan suka take shi, banda jini ba wani abun dake malala a tsakar gidan, sai fantsala musu a fuska da jikin jinin yake, amma da yake yan datti ne ko ajikin su basu damu ba.

Bayan sun tsaya a tsakiyar gidan ne suka fara jawo duk wata halitta dake cikin gidan suna fito da su, da tsafin su, sai dai kagan su fiw sun jawo mutun waje ya fito, haka suka jawo Mustapha ma fiw ya fito kamar iska, har da baba suka fito da shi, duk a tsakar gidan suka tara kowa, kafin su juya idon su ya koma kalar na tsafin su, wato light green, da tsafin nasu suka fara neman in da Rimsha take a cikin gidan, domin kuwa madubin Queen ya nuna musu babu Rimsha cikin wayan da suka tara a wajen, sai zazzaro ido suke suna jujjuya idon nasu gwanin ban tsoro da tashin hankali

Bayan Mustapha da duna da baba ba wata halitta mai rai da ta rage tana cikin hayyacin ta a gidan, har ita Rimsha ɗin da duna ya ɓoyeta bata cikin hayyacin ta, mai iya kallon su Gujungu ido huɗu kuma ya iya rayu bai mutu ba, tofa sai mai tsawon kwana kuma mai karfin imani, irin dai mutanen part ɗin su Rimsha, dan sune masu imanin gidan, tun da har suka iya wace part 1 suka wuce part 2 suka zo nan to tabbas sune jiga jigan masu imani, dan mai raunin imani baya iya tsallake wa su Barbushi.

Can cikin duhu É—akin duna idon tsafin su ya hango musu Rimsha tana kwance tana ihu, da karfi, Gujungu ya fisgota, da tsafin sa zuwa tsakar gidan

Saƙabo ne ya wage wanna gabjejen bakin nasa ya fara ɓaɓɓaga dariya irin nasu na gunguma gunguman matsafa, nan take gidan ya ɗauka da karfin sautin dariyar tasa, juyawa sukayi, suka nufi hanyar da sukabi suka zo, da tsafi suka fara jan Rimsha tana bin su a baya daga kwance, Allah sarki jikin ta sai kukkujewa yake a kasa tana ihu kamar ranta zai fita....

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞

TRIPLET'S💞

💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)

*GargarÉ—i*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_

WhatsApp me for more information 09162620621

Episode 32-33

Saƙabo ne ya wage wanna gabjejen bakin nasa ya fara ɓaɓɓaga dariya irin nasu na gunguma gunguman matsafa, nan take gidan ya ɗauka da karfin sautin dariyar tasa, juyawa sukayi, suka nufi hanyar da sukabi suka zo, da tsafi suka fara jan Rimsha tana bin su a baya daga kwance, Allah sarki jikin ta sai kukkujewa yake a kasa tana ihu kamar ranta zai fita.
Chapter 101 · 0% Book details