← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 126

Sashe 120

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji kake dip dip, suna dirowa kasa daga bayan motocin su, da gudu wasu suka kewaye Romeo dake tsaye, wasu kuma suka kewaye wannan motar yan ta'addan wasu kuma suka kewaye gaba ɗaya kan titi daga ta in da suke, hannun su na rike da jiga jigan bindigogi wayan da suka amsa sunan su bindiga, wadda baya saɓa saiti in da ka aikashi nan zan wuce kai tsaye, ba irin makaman kananan yan sanda da sojoji bane.

ÆŠaya daga cikin yan sandan ne yace da sojojin "Yauwa wannan shine É—an ta'addan ku kama shi, É—an tada kayan baya ne, yazo ya fara dukan jami'an tsaron mu ya.... Bai kai karshen maganar ba sojan É—aya ya daka masa wani gigitacen tsawa wadda ya sanya gaba É—aya yan sandan dake wajen zubewa kasa a kan gwiwowin su, tsabar tsoro jikin su sai kerma yake

A hankali Romeo ya zame hular kan sa tare da karɓan bindigar ɗaya daga cikin sojojin sa, ya sai ta kwaɗon jikin kwantenan motar yan ta'addan can, ya harbe kwaɗo, kofar ta buɗe

Ji kake dip dip da gudu sojoji biyu suka zo suka buÉ—e masa kofar contenan, yan mata ne cike a ciki duk basa cikin hayyacin su an musu allura fita daga hayyacin su, kallo É—aya Romeo ya musu ya kawar da kan sa gefe ya juya tare da cire hand gloves dake hannun sa ya nufi mota É—aya daga cikin motocin da sojojin sa sukazo yanzu.

Lokacin da Romeo ya cire hulan kan sa kamannin sa suka bayyana tsoro yasa yan sandan dake wajen sume saboda babu wani É—an adam dake cikin birnin Washington DC da baya tsoron Romeo bare kuma su da suka masa laifi har da harbin bindigar hannun sa tab, sun gama sadaukarwa yau mutuwa zasu yi, shiyasa suka fara da suma tun ma basu ji hukuncin da zai yanke musu ba.

Shi kuwa bai bi ta kan su ba ma dan yana da abun yi, motar sojojin sa ya nufa, da gudu jibga jibgan sojoji biyu suka nufe sa, suka buÉ—e masa kofar motar gidan gaba, shiga yayi ya zauna sannan gently yace su kai masa wayan nan yan ta'addan gida zai yi aiki a kan su da kan shi, motar yan ta'addan kuma su kai headquarter su ajiye zuwa da safe yan sandan nan kuma su kira president su sanar da shi ya soke aikin su, dan dukkan su basu san aikin da suke ba.

ÆŠaya daga cikin sojojin sane ya shiga motar ya mata key yaja sa zuwa gida, har cikin gida ya shiga da Romeo, yana yin parking ya fito ya buÉ—e masa kofar motar, gently Romeo ya sako kafar sa waje kafin ya fito gaba É—aya ya nufi cikin gida, shikuma sojan ya juya kan motar ya koma wajen sauran sojojin can dan suyi aikin da lion ya saka su.

Lokacin da Romeo ya shiga bedroom nasa, Micheal na kwance masa saman katafaren gadon sa idon sa a lumshe da alama barci yake, wuce sa Romeo yayi yaje ya yi wanka ya fito ya shirya cikin kayan barci masu kyau da tsada launin sky blue riga da dogon wando mara sa nauyi.

Sai tashin fitinannen kamshi yake ya saki dark black curly hair sa har baya, ya haye saman bed nasa kusa da Michael ya jawo laptop nasa ya fara aikin bincike a kan James.

Number wayar James ya shigar cikin laptop ɗin nasa ya fara kokarin bin diddigin in da James ɗin yake, yasha mamaki ganin number James yana shararin sama niya, kenan jirgi James ya hau zuwa ina to? Shiru Romeo yayi yana mamakin ina James zai je bai sanar da shi ba, kuma dole yasan tafiya zata fita cikin Washington DC, har James zai iya fita cikin garin nan ba tare da sani na ba? Sai jerowa kan sa tambayoyi wadda bashi da amsar su yake, "gaskiya nayi sake na biye musu ina musu abun da suke so, daman dan suje suyi ta tsula tsiyar su a waje ne yasa sukace basa son bodyguards ko sojoji surinƙa binsu idan zasu fita, nayi kuskuren yarda da hakan da nayi" sosai Romeo yake tunani a zuciyar, daga karshe dai sai ya fara binciken wace jirgi James ya hau kuma ina zai je, me ya fitar da shi cikin Washington DC da daddaren nan kuma da jirgin kasuwa abun da basu taɓa yi ba, koda yawon shakatawa su James zasu je wata kasa jet ɗin sa yake badawa a kai su duk in da zasu je dan tsaro, amma yau James ya saci hanya ya hau jirgin kasuwa why.

Duk wani binciken da yayi a wannan daren dan gane ina James ya dosa bai samu damar gane wa ba, dole dai sai da safe yasa sojojin sa su bincika masa a wani airport James ya hau girji dan suji ina zai je, daga nan ya ajiye bincike a kan James ya shiga bincike cikin sauran criminals da basu samu damar halactar taron su James ba dan ya gano ina suke,

Bayan ya kammala wannan binciken ne kuma ya shigar da number motar da ya kama É—azun mai É—auke da yanmata nan, nan ma yayi bincike a kan motar, daga ina motar ta fito ina kuma ta nufa, dan ya san dai ba iya wayan nan yanmatan ne kawai ba, tun da motar ta kwaso wayan nan tofa tabbas ta saba kwasan yanmata ne dole ya san ina ake wannan badakala a cikin garin sa,

Da binciken nasa yayi bincike a wajen bibiyar ɗaya daga cikin driver masu safaran yanmata da suka kama, nan yaci karo da driver'n yana yiwa wani babban likita aiki, ganin yana aiki da likitan yasa Romeo ya fara bincike a kan likitan da kuma asibitin, nan yaga abun da ya tayar masa da hankali, domin kuwa a wannan asibitin ana kawo maza da dama ana cire musu kodar su, da wasu sassa jikin su irin su ido gaban su da dai sauran, ana sanyawa manyan masu kuɗi na duniya, yasha mamakin ganin duk wannan badaƙala da sheɗan ci ace a cikin garin da yake ake yin su, abun ya ɓata masa rai sosai, ji yake kamar ya tashi ya tafi wannan asibitin yanzu, sai dai dare yayi, kashe laptop ɗin yayi ya ajiye saman bedside drawer ya ɗan yi shiru na yan mintoci kamar mai tunanin wani abu, sannan ya kwanta ya ja musu bargo shida Michael yau ko abinci ma bai jin ci saboda tunanin da ya masa yawa meke shirin faruwa da su ne, ina James ya tafi wayan nan abubuwa sun dame sa, hakan yasa yaji baya jin yinwa kwata kwata.

Ko da ya kwata ya kasa barci tunanin James kawai yake, ya rasa dalilin da yasa yake ji a ransa tamkar zai rabu da James, slowly ya waro dara daran idon sa, ya zubawa Michael kallo, sai barcin sa yake bawan Allah hankalin sa kwance bashi da wata matsala, shafa kan sa Romeo yayi sannan ya mai da idon sa ya lumshe yana tunanin ya zasu yi idan akace yau babu James a tare da su, dan tabbas idan abun da yake zargi a kan James ya tabbata shi da kan sa zai harbe James ɗin da bindiga, dan ya kamanta adalci, to ya zasu yi yau idan akace ya harbe James da bindiga ya mutu, tare suka taso kullun suna tare, duk da baya shiga har kan su, yana matuƙar kaunar su fiye da tunanin mai tunani

A wannan dare dai da kyar barci ya É—auki Romeo zuciyar sa cike da tunanin É—an uwan sa.

Asuba ta gari

Mu leƙo Nigeria mu dawo jama'a

# 💞NIGERIA💞

💞KADUNA - GIDAN ABBO💞

Almost 30mins Hajiya ta ɗauka kwance tana mai da numfashi kafin ta ɗago ta kalli Jelly, a hankali ta zuro kafafun ta kasa sannan ta miƙe ta riƙo hannun Jellyn suka nufi bedroom nata tana faɗin "Me yasa kikayi wannan kwaɓen a fuskar ki?" Toro baki Jelly tayi kafin tace "Nifa wanka da kwalliya nayi" shiru Hajiya tayi dan tasan halin Jelly yanzu idan tace zata mata wani magana ko ta mata faɗa idan ta fara kuka sai ta kai dare bata yi shiru ba, gashi bata jin rarrashi ko kaɗan, dan haka Hajiya sai ta rufa wa kan ta asiri tayi shiru taja hannun ta kawai suka wuce toilet

Suna shiga toilet a sukwane Hajiya ta zaro ido ganin lalatan da jelly tayi da sabulai dake cikin toilet É—in

Bokitin dake cikin toilet ɗin Jelly ta ɗauka ta ɗaura shi saman baf ɗin wanka ya ɗebo duk wani shower gel da su toothpaste da su sabulai su man kamshin baki shaving powder duk ta haɗe su cikin bokitin nan ta gauraye su waje guda, da farko Hajiya ta kasa gane menene ma a cikin bokitin sai daga baya data kalli robobin su shower gel ɗin a gefe ne yasa ta gane menene a cikin bokitin, salati tayi ta sanar da Ubangiji yau ga abun da ya fi karfin tunanin ta, tana tsoron yiwa Jelly wata magana, dan in ta kuskura tawa Jelly maganar da bai mata daɗi ba, idan ta fara yi mata ihu har dare bazata yi shiru ba, sai Abbo ya dawo ya rarrashe ta yayi ta yiwa Hajiya faɗa a kan me zata ɓata mata rai.

ÆŠaukan bokitin Hajiya tayi ta fitar waje, dan wayan abubuwa da Jelly ta haÉ—a sai zubarwa, dan har da su makilin na goge baki ta musu asarar makudan kaya masu tsada.

Jelly na tsaye a cikin toilet ɗin har hajiya taje ta zubar da kwaɓen da tayi ta dawo hannun ta riƙe da wani carton na sabulu mai kyau da tsada, ajiye bokitin tayi ta haɗa ruwan wanka sannan ta cirewa Jelly kaya ta fara yi mata wanka

Ba karamin wahala ta shaba wajen wanke fuskar Jelly, dan mai data damɓara kan sabulu ga foundation da kwalli abun ba'a magana, ita kan ta Jellyn sai da tayi kuka wajen wanke mata fuskar nata.
Chapter 120 · 0% Book details