← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 126

Sashe 59

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

babu ko sallama Jehan ta faɗo palon sai kwaɓe fuska take kamar wadda taga kashi ko wani abun kyamar. "My Jehan lafiya? Daddy ne ya tambaya yana kallon face ɗin ta, zama tayi gefen sa tana faɗin "Daddy ina kewar School ne" shafa kan ta yayi yana faɗin "To ai next week zaku koma ko? Gyaɗa masa kai tayi kafin tace "Daddy yau azumi saura kwana nawa?" Cikin sauri Rimsha tace "Remain 12 days fa" "did I ask you?" Cewar Jehan tayi maganar tana hararar Rimsha ɗin, murmushi Rimsha tayi tana faɗin "Sorry ASP Jehan or DPO or commission" turo baki Jehan tayi tana kokarin yin magana suka ji sallamar mai gadi, miƙewa daddy yayi ta nufi kofar palon yana amsa sallamar, kallon Gwaggo mum tayi kafin tace "Da alama barkama ya san da zuwa mai gadin nan fa" murmushi gwaggo tayi tace "Ni dai ba ruwa na kun fi kusa ai" mum na kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa "Mum i need to see your previous pictures before you got married to my dad nan take face ɗin mum ta sauya, nan take taji ba daɗi taji zuciyar ta na mata ciwo Jehan ta tuna mata baya, shiru tayi bata yi magana ba.

Da sallama daddy ya dawo palon hannun sa ɗauke da carton irin na turo sako daga kasar wajen nan, a tsakiyar palon ya ajiye, da sauri Jehan ta miƙe ta kariso wajen tana faɗin "What is this daddy?" Miƙewa zaune Rimsha tayi ta zubawa daddy dara daran sleeping eyes ɗin nan nata ba tare da ta je wajen ba.

Buɗe kwalin daddy yayi ya fara fito da kayan yana faɗin "Kaya na saya muku daga Dubai" ya kai karshen maganar tare da fitowa da Jehan wasu kayan masu kyau na yan kwallo dan Jehan a koi ta da son kayan yan kwallo sosai, daddy na kokarin yin magana Jehan ta ansa kayan daga hannun sa tana dariya ta wuce ta haye sama ta nufi bedroom na su dan taje ta gwada, girgiza kai kawai daddy yayi ya ci gaba da fito da kayan, ita dai Rimsha ta zuba masa dara daran sleeping eyes nata tana kallon yadda yake fitar da kayan, ɗago kai yayi yace "My siha close your eyes, i want to surprise you" ba musu ta ta rufe idon na ta, wani leda ya ɗauko daga cikin kwalin ya nufe ta, ya zauna gefen yana faɗin "now open your eyes" da sauri ta buɗe idon nata dan ta ƙagu ta ga me daddy zai mata surprise a kai, miƙa mata ledar yayi yana kallon face nata, cikin zumuɗi ta ansa tare da buɗewa

a sukwane ta miƙe tsaye tana faɗin "What? Daddy am I dreaming or not?"

Sosai daddy ke murmushi dan bashi da wani burin da ya wuce yaga farincikin yayan sa, wan nan murmushi dake kan face É—in Rimsha ya fi masa abubuwa kaso 80 cikin É—ari na rayuwar sa.

Fito da kayan Rimsha tayi tana ta dariya kamar bakin ta ba zai rufu ba, kyakkyawan dimple nata sai motsawa yake ga open teeth nata dake tsakanin fararen hakwaran ta kamar gonar audiga, cikin zumuɗi ta zuje zip ɗin jacket ɗin ta sanya a jikin ta tana faɗin "daddy ai na ka samu irin jacket ɗin GAR dan Allah" "Saya na yi mana, My siha daga Dubai na sai miki saboda son da kike wa guy ɗin shi ne na ga kuma yana yawan sanya irin jacket ɗin shiyasa na ɗauki hoton na tambaya wurare daban daban da kyar na samu a Dubai, na ɗau wajen 2 weeks ina neman jacket nan company company, su kan su company da suka buga jacket ɗin na tuntunɓe su ta number su na WhatsApp, amma sai suka ce min gaskiya iya shi kaɗai su kayiwa shi ya kawo sample suka masa dan haka ba zasu iya yi min ba, wan nan ma na hannun ki ba sak irin nashi bane copy ne babu irin na sa shi kaɗai suka bugawa" shiru Rimsha ta ɗan yi kafin tace "Daddy to shi ma copy ɗin yana da tsada ne? Dan naji a Tv sun ce Jacket ɗin na shi na da tsada sosai, gashi kuma yana da su kala kala, sai dai duk design ɗaya ne color ne daban daban" jinjina kai daddy yayi kafin yace "Hmmm My siha kuɗin da na sayi jacket nan ba zai faɗu ba ke dai kawai ki saka irin jacket na GAR ɗin ki ba sai kin ji kuɗin copy ɗin ba ma" juyawa tayi ta kalli mum kafin tace "Mum ya min kyau?" Mum da gwaggo har suna gaɗa baki wajen cewa "Ya miƙi kyau over Rimsha sai dai ya miki yawa sosai, Jacket ne har kasa gaskiya ki ajiye sai kin kara girma" make kafaɗa tayi tana faɗin "Ni ko yana ja a kasa ma ni sai na sa" shi dai daddy sai murmushi yake abun sa burin sa ya cika tun da Rimsha da Jehan sun yi murna, wuce wa ita ma Rimsha tayi ta nufi bedroom na su da jacket ɗin sanye a jikin ta wadda ya kai ma har idon sahu na kafar ta.

Fito da sauran kayan daddy yayi ya bawa gwaggo nata san nan ya bawa mum nata wadda ya kasance irin ɗaya ne dana gwaggo Dubai jallabiyas ne masu kyau da tsada, shi ma ya sai wa kan sa Dubai jallabiya na maza masu kyau da tsada, miƙewa yayi da na shi ya wuce bedroom na shi, miƙewa ita ma mum tayi tabi bayan sa, ita kuma Gwaggo ta wuce bedroom nata dan taje ta ajiye kayan.

"Washington DC*

*08:00 am*

Zaune suke gaba É—ayan su a palon kasa, Micheal, James, Jay, ko wan nen su kan shi na kan wayar sa yana latsawa yayi da shi kuma daddy yana hira da uncle Herry.

A buge John ya shigo palon kwata kwata ya manta da Romeo ya dawo, Sanye yake da Bluetooth a kunnen sa, jikin ne sa sanye da wando crazy irin na shararrun yan duniya nan, yau yayi kitso bibbiyu ta gefe da gefen kan sa, yayin da jikin sa ke sanye da t-shirt baka mai zanen horo da jan kala a gaban, hannun sa wuyar sa duk sanye suke da chain na maza masu kyau da tsada, kallo É—aya zaka masa ka san yau a cike da iya shege yake,

taku yake ta baya baya ya shigo palon yana tafiya yana girgiza kai da jiki yana bibbiye wakar da yake ji daga ta cikin Bluetooth ɗin, kasan cewar su basa jin wakar da yake ji sai dai wanda yake bibbiyewa suke ji sai hakan ya musu ban bara koi saboda wakar yan china yake ji, shi dai Jay kallon tsantsar mahauakci ma yake masa, dan wakar da yake bi ɗin ma basu taɓa jin irin ta ba, idan yayi taku ɗaya sai ya tsaya ya tiki rawar sa iya son ransa kafin ya ci gaba da tafiya, gaba ɗayan su sun zuba musa ido suna kallon sa, ba karamin tausayi ya basu ba, dan da alama yau wine ɗin nasa tasa ya manta da Romeo ya dawo, shi ko ko ajikin sa dan daman mayen son rawa da waka ne kamar Michael Jackson, kai tsaye saman bene ya nufa ko kallon in da suke bai yi ba.

Dai dai lokacin Romeo ya fito daga part na shi jikin sa sanye da wando jeans guntu zuwa gwiwar sa sai riga fara mara nauyi mai karamar hannu, yau ma kamar kullun ya É—aure dark black curly hair sa da ta sha gyara sosai sai kyalli da kamshi take, ya É—aure ta a bayan sa, kaÉ—an ya zubo masa ta gaba goshin sa kasan cewar gashin gaban goshin nasa ya É—an yanke ta bata kai tsawon na bayan sa ba, hakan yasa bata iya kai wa ya haÉ—a da ita ya É—aure shi yasa ko ya É—aure gashin na shin nasa wan nan na gaban goshin bata shiga ya É—aure da ita sai ta zubo masa a kyakkyawar face na shi, hakan kuma ba karamin kyau yake kara face na shi ba, kamar kullun yau ma a koi face mask a face nashi, wan nan daddaÉ—ar fitinanniyar kamshin perfume nashi ne ya kai wa su Michael karo a hanci hakan ya sasu É—agowa a sukwane kuma a tare har da su daddy, dan ko ina kamshin perfume É—in ya gauraye gaba É—aya duk girman palon, tun ma bai shigo cikin palon ba

a sukwane su Michael suka kara nitsuwa kowa ya ajiye wayar sa dake hannun sa suka zubawa John dake rawa yana tafiya yana tinkarar Romeo dake kokarin sauko wa kasa, ganin John na zuwa a buge yasa Romeo tsayuwa ya zuba masa dara daran blue eyes na shin masu ɗaukan hankali nan yana kallon sa, duk wata halitta mai rai dake cikin palon sai da ta nitsu tsit ka ke ji ko numfashi a hankali suke fitar wa dan gudun shiga matsala, shi ko John sai kaɗan kai da hannu yake yana tafiya yana wani bouncing, ya sanya hannun sa ɗaya ya rinƙo wandon sa ta tsakiya dai dai sai tin gaban sa irin yadda gayu keyi, zuba masa ido gaba ɗaya palon suka yi yayin da shima Romeo ya zuba masa ido yana kallon gudun ruwan sa

John bai an kara ba sai ji yayi ya daki kirjin mutun sai da yayi baya yayi tangal tangal ya faɗi kasa, a sukwane ya ɗago kai cikin muryan yan maye yace "Who is this?" kara waro ido sa waje yayi yana kallon Romeo, sai dai kash saboda shaye shayen da yayi ta sa bai gane ko wanene a wajen ba hakan yasa ya ja dogon tsaki tare da banko uban ashar yana kokarin miƙewa

Raɓawa ta gefen sa Romeo yayi a nitse ya nufi hanyar fita ba tare da yace komai ba, har su James suna haɗa baki wajen cewa "Good morning Lion" jinjina musu kai yayi ba tare da yayi magana ba, ya wuce ya nufi waje
Chapter 59 · 0% Book details