← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 126

Sashe 4

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga É—aki ta ajiye wayar saman yar gadon su ta É—auki É—an karamin hijabi ta shifiÉ—a dadduma ta tada Sallah abun mamaki a nitse tayi sallar tare da karanta manya manyan surori a Qur'ani irin su suratul Yusuf da Aaraf a nitse tayi sallar nata sai dai hijabin nata ne bai gama rufe mata hannu ba a haka tayi Sallar.
Bayan ta idar ta ɗaga hannu sama tayi addu'a mai tsawo sanna ta shafa ta mike ta cire hijabin ta mai da saman trolley ta tare da naɗe daddumar ta ajiye saman hijabin nata ta ɗauki wayar ta, ta fito waje nan tsakar gida ta isko mum da goggo sun tasa abinci a gaba sun kasa ci dukkan su sun buga uban ta gumi suna tunani ga wayar mum a gefen ta kirar I phone 13 ta kunna wutar wayar tana haska musu wajen. Kallon Abincin Jehan tayi shinkafa'ce da miyar steew da naman rago yaji ganye irin su lettuce cucumber cabbage da dai sauran su dogon tsaki taja ta nufi hanyar fita gidan babu hijabi" Jehan ina zaki je? Cewar mum "mum I'm feeling hungry kuma ni gaskiya i can't eat this dirty food I want to go and withdraw money from my Account to buy something that I will eat" "Jehan karki kashe kuɗin cikin Account na kin nan saboda bamu san me gobe zata haifar ba kiyi hakuri ki ci abincin nan yau kam kinji? Cewar mum kallon goggo Jehan tayi tana faɗin "ni gaskiya I can't wallahi" "Ok naji bazaki ci ba na yarda amma karki fita da daddaren nan kinga yanzu ma bamu ga Rinsha ba ko? Ki bari na je na ciro kuɗin na sawo miki ko me kike son ci" girgiza kai Jehan tayi kafin tace "No mum bana so, ki zauna i will go by myself" tana kai karshen maganar ta fice da sauri mum na faɗin "To ki dawo ki sa hijabi" ina kan mum tayi magana ma Jehan ta fice abun ta kallon mum goggo tayi tace "Maryam kiyi hakuri kici Abincin ki kinji ko?" girgiza kai mum tayi tana faɗin "Aunty Aisha ba zan iya cin Abincin ba bakina ba daɗi ina Rimsha take? Wani hali take ciki? Hannun su wa take? Mutane na gari ne ko na banza? Taci Abinci ne? ko bata ci ba? Wanna tunani ba zai barni na iya cin Abinci ba Aunty A'isha" dafa kafaɗar ta goggo tayi cikin tausayin uwa da ƴa tace "Na sani Maryam dole ki shiga tashin hankali muma muka shiga tashin hankali bare ke amma ki daure ki ci Abinci nan In Sha Allah babu abun da zai samu Rimsha zata dawo gare mu cikin koshin lafiya" da kyar mum ta iya cewa "Aunty A'isha ina ji ajikina duk in da Rimsha take bata lafiya tana cikin tashin hankali da damuwa" "A'a Maryam ki dai na faɗin hakan ki mata Addu'a domin Addu'ar Uwa bata faɗuwa haka kasa banza kinji? Yanzu dai dan Allah kici abincin" miƙewa Mum tayi ta nufi ɗaki tana faɗin "Aunty A'isha sai da safe ba zan iya cin komai ba" ta kai karshen maganar tare da shigewa ɗaki dafe kai goggo tayi tana salati da ambaton sunan Allah a ranta. Tana kokarin miƙewa Jahan ta shigo gidan babu ko sallama, kusa da goggo tazo ta miƙa mata ledoji biyu farare masu ɗauke da takeaway da drinks a ciki ta wuce da leda ɗaya ɗakin ta in da sabo goggo ta saba tun da su kazo garin nan Jehan bata cin Abincin da suke girkawa sai dai taje restaurants tayo musu takeaway kuma bata taɓa saya ita kaɗai guda huɗu take saya kullun goggo tasha ruman mamakin ganin yau ta sayi guda uku sai daga baya ta tuna ashe Rimsha bata nan, jiki ba kwari goggo ta mike taje ta rufe musu kofar gida sanna ta dawo ta wuce ɗakin mum saman gado ta isko mum kwance kamar mai barci ajiye mata wayar ta da kuma leda ɗaya daga cikin ledojin da Jehan ta sawo musu abinci goggo tayi, ta juya ta fita ta nufi ɗakin Jahan kasan cewar ɗakuna biyu ne a cikin gidan mum da Rimsha take kwana ita kuma goggo da Jehan zaune a tsakiyar ɗaki ta isko Jehan tana cin abinci fried rice da pepper chicken ajiye nata Abincin goggo tayi ta haye gadon su ta kwanta dan ita ma bata jin yinwa ko kaɗan ɓatan Rimsha ya tsaya mata a rai sosai, Addu'a tayi ta yiwa Rimsha akan duk in da take Allah ya tsare ta da haka har barci ɓarawo yayi awon gaba da ita. Ita kuwa Jehan sai da taci tayi nak sanna ta kwanshe kayan ta gyara wajen dan ita mace ce mai son tsabta bata son datti ko kaɗan. Sai da ta gyare wajen tsab ta sauya kayan jikin ta izuwa na barci ta haye gado kusa da goggo ta kwanta tare switch off na wayar ta ba jimawa barci yayi awon gaba da ita dayake ba tare da Rimsha suke kwana ba sai bata wani damu da rashin Rimsha ɗin sosai ba.

Misalin karfe 1 na dare duniya duk sunyi barci Mum na zaune tsakiyar gadon ta ta kifa kai da gwiwa tana sharar kuka tana cikin matsanancinyar damuwa da tashin hankali ɓatan Rimsha, sosai take kuka damuwa sun haɗu sun mata yawa ga yanayin Jehan ga ɓatan Rimsha har karfe 2 na dare tana zaune tana sharar kuka.
Sai 2:30 ta mike ta É—auro alwala a toilet na É—akin ta tazo ta fara sallah tana kai wa Allah kukan ta.
Kamar yadda ta ga rana haka taga dare dan ta kasa rintsawa gani take kamar Rimsha zata dawo komai dare.

Washegari tun karfe 6 mum ta fita ta nufi gidan su Sadiq yayin da ita kuma Jehan ke sharar barcin ta goggo na fama da Aikace Aikace gida tana kokarin É—unÉ—uma musu abincin daren su na jiya da basu samu damar ci ba dan suci da safen.

Da sallama mum ta shiga gidan su Sadiq yana tsaye a tsakar gida shi da maman sa da alama wani magana suke jin sallamar mum yasa suka juya a tare, ganin mum yasa Sadiq ya ɗan saki murmushi yana faɗin "Sannu da zuwa Mama ina kwana?" "Lafiya lou babana" kallon Mum Maman Sadiq tayi cikin mutuntawa tace "Sannu ki da zuwa yanzu Sadiq ke faɗa min abun da ke faruwa na ɓatar ƴarki Allah sarki Allah ya bayyana ta" da sauri mum tace "Amin ya Allah" "Mama bari na kira su Sha'aban muje mu duba gidajen masu anguwanni ko Allah zai sa mu dace muga yarinyar" "To Sadiq Allah Ubangijin yasa ku ganta Allah ya bada Sa'a" "Amin" Sadiq ya amsa da shi sanna ya dubi mum yace "Mama ki koma gida zamu dubata gidajen masu anguwanni da dai duk in da ya dace" girgiza kai mum tayi cikin sauri tana faɗin "A'a babana muje tare ba zan iya zama a gida ba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba". Ba yadda Sadiq bai yi da Mum akan ta koma gida ta jira su ba amma taki har Maman Sadiq ta sa baki amma mum taki haka Sadiq ya hakura suka tafi cikin jin kunya ya jera da mum suka fito ya shiga ɗakin su dake zauren gidan ya kira Sha'aban da Yusuf suka fito suka jera a tare suka fice daga gidan.

Gidajen masu anguwanni suka fara zuwa suna tambaya, duk in da suka je ace musu ba'a ganta ba sunje gidajen masu anguwanni 5 amma shiru shiru ba labari mum ta gaji iya gajiya dan bata saba tafiyar kafa ba ga yinwa da take ji tun jiya da rana rabon ta da Abinci amma saboda tana da yakinin za'a iya ganin Rimsha ko da a hanya ne yasa ta danne duk wani abun da take ji ta jure ta cigaba da bin su Sadiq. Duk in da Sadiq yake tunanin za'a ga Rimsha sunje amma shiru daga karshe sai ya yanke shawarar suje su kai wa malamai kuÉ—i afara yi musu addu'a. Haka kuwa akayi malamai biyar mum ta rabawa dukka kuÉ—in hannun ta akan ayiwa Rimsha saukan Al Qur'ani mai girma sanna tayi sadaka da É—an kuÉ—in da suka rage mata, jiki ba kwari ga gajiya da yinwa suka juya suka dawo anguwar su cikin mutunci da girmama juna sukayi sallama dasu Sadiq ta wuce gida da kyar take jan kafar ta duk kafar nata sun kunbura sun yi ja.

Da sallama ta shigo gidan a tsakar gida ta isko Jehan da goggo suna zaune goggo tayi jugumi tana tunani, ita ma jehan tana zaune gefe ta buga nata tagumin, ganin mum yasa sukayi saurin miƙewa Jehan ta fasa kuka tana faɗin "Mum whare is my Rimsha?" "Maryam ina Rimsha ɗin take?" Cewar goggo wuce wa mum tayi ta zauna saman tabarma tana mai da numfashi kamar zatayi kuka cikin sauri goggo ta koma ta zauna tare da dafa kafaɗar mum tana faɗin "Maryam ki faɗa mana ina Rimsha kar ki sa zuciyar mu ta buga" shiru mum tayi tana mai da numfashi ta kasa magana.

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai

💋Star Lady💋

Share fisabilillah 👏

💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞

Mai bukatan karanta book É—in*TRIPLETS* daga farko har karshe yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number 09162620621 ban da kira please

STAR 🌟 LADY..✍️

*💋The beginning💋*

Episode 2
Chapter 4 · 0% Book details