← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 126

Sashe 116

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin Jelly ce da gaske yasa Hajiya Turai ta sake jikin ta tana faɗin "Ruwa a taimaka min da Ruwa" ba ita ka ɗai ba masu bukatar ruwan suna dayawa a wajen, mafi yawancin su sun baje a kasa suna a basu ruwa, girgiza kai Nawid yayi ya riƙo hannun Hajiya, da kyar da kyar take ɗaga kafar ta, suka wuce ciki, har sun ɗan yi nisa, ya juyo ya kalli Jelly dake tsaye, da hannu ya mata alama da tazo su tafi, da yar gudun ta ta kariso wajen sa suka shige cikin palo tare, su kuwa sauran sun baje a kasa suna ta neman agajin ruwa, mai gadi ma ya fito daga maɓoyar sa wato bayan flowers ya koma bakin gate yana faɗin "Amma wannan abu bai min daɗi ba, naso na make shagiya ta mutu, amma ba komai akoi gobe ma ai sai na make ta ta mutu ɗin" sai surutan sa yake shi kaɗai kamar wani zararre.

Hajiya Turai suna shiga palon su, ta haye saman sofa mai zaman mutun 3 ta kwanta tana mai da numfashi, ruwa Nawid ya ɗauko mata mai sanyi a fridge ya bata tasha sannan ya wuce bedroom nasa, kusa da ita Jelly ta zauna tana kallo a Tv ko a jikin ta, Hajiya kuwa ta lumshe ido tana sauke mumfashi wahala, dan yau ta wahala fiye da tunain mai tunani, kun dai san yadda gudun mai ƙiba yake to hakane.

Kun dai ji halin da Jelly ke ciki na saka mutanen gida motsa jiki, yanzu dai muje mu leƙo Washington DC mu dawo kafin nan kila Hajiya tayi barci ta huta, sai ta tashi tayiwa Jelly ɗin ku wanka...

💞WASHINGTON DC💞

James yana fita wajen Romeo kai tsaye word room ya nufa, zaune ya isko Musharraf, abun ku da na'urori na zamani sha yanzu magani yanzu, idan kana da kuÉ—i ba abubuwan da ba za'a maka ba, saboda kayan aiki na zamani da Dr William jacop yake da shi hakan yasa kafar Musharraf yayi saurin samun sauki, sai dai baya iya tafiya sosai kaÉ—an kaÉ—an yake É—ingisa kafar, amma yana iya tashi da kan sa ya zauna, kuma yana samu kulawa sosai a wajen dad da James, su kaÉ—ai ke kula shi a gidan, shima dad dan bai san Musharraf Musulmi bane da ba zai kula shi ba.

Gefen Musharraf ɗin James yazo ya zauna yana faɗin "Uncle are you feeling?" Murmushi Musharraf yayi kafin yace "My son I'm getting better" "what do you want to eat today uncle?" Sosai Musharraf yaji daɗi cike da matikar kaunar James yace "Gaskiya ina son cin miyar steew da akayi da kifi, da kuma shinkafa" okey James yace lafin ya miƙe ya ɗauko wa Musharraf kujeran tura mara sa lafiya wayan da ke da matsalar kafa

Kamar baby haka James ya É—aga Musharraf ya É—aura sa saman kujerar yana faÉ—in "Muje ka ga gida, yau dai ka É—an fita waje" sai murmushi Musharraf yake yaji daÉ—i sosai dan dama ya gaji da zama a É—akin.

James da kan sa ya turo Musharraf suka fito, kai tsaye palon kasa ya nufa, su dad gaba É—ayan su suna palon kasa suna zaune suna hira har da Michael mai barci ma ya taso yayi joined nasu.

Suna ganin Musharraf suka É—aure fuska, musamman uncle Herry da Tga da John, Jay ne yace "Kai James who is this man?" Dan su Jay kwata kwata basu san da zaman Musharraf a gidan ba, atakaice James ya faÉ—a musu waye Musharraf da kuma zaman me yake a gidan, nan fa suka ce basu yarda ba dole Musharraf ya bar gidan nan yau, a kai shi hospital ayi jinyar sa a can ba dai a gidan nan ba, kallo Michael James yayi kafin yace "Kana tare da su Michael? Kana son uncle ya bar gidan na?" James ya tambayi Michael ne dan yasan idan Michael yace baya son Musharraf ya zauna a gidan tofa ko zai mutu sai Musharraf ya bar gidan, dan lion ba zai yarda da zaman Musharraf ba muddin Michael baya so, amma idan Michael yana so to ya samu daman da zai tinkari Romeo ya neman wa Musharraf takardan izinin zama a gidan.

Romeo yana da wata ka ida, ko wani irin mutun ne yazo gidan zai zana to fa ba zai yiwu ya zauna ba sai da takarda izinin zama gidan, misali yanzu idan daddy ya kawo abokin sa yace to ga abokin sa zai ɗan zauna da su a gidan, tofa sai ya sa hannu a takarda dan gidan su tana da takardan zama a cikin ta, ma'anar takardan nan kuwa, shine, misali bari ayi gwari gwari, idan bako yazo zai zauna dasu, Romeo zai tambaye sa zaman shekara nawa zai yi, idan yace shekara ɗaya, to Romeo zai rubuta a takardan sa, shekara ɗaya mutunmin zai yi, sai ya baka ka sa hannu, kana sanya hannu to ka dawo karkashin kulawar Romeo ko fita zakayi sai da izinin sa, dan shi baya yarda da mutane shiyasa, ba zai bari ka rinƙa fita da shiga gidan ba, sannan kuma baka isa kace zaka tafi wannan shekara ɗayan bata cika ba, baka isa ba, kome zai faru sai wannan shekaran ta cika, amma babban abun daɗin shine in dai ka samu takardan zama a gidan tofa kana cikin tsaro, dan Romeo zai kula da rayuwar ka duk in da zaka je zai iya sanya sojiji su raka, dan ka sanya hannu a takarda kamar ka zama ɗan gida ne, sai dai fa samun takardan izinin zama a gidan nasu ne, babban tashin hankali dan basu ma son bako, bare har ya samu wannan takarda, amma in ka samu lafiya Lou.

Shiru palon yayi suna jiran amsar Michael, ya amince Musharraf ya zauna ne ko kuma bai amin ce ba, hannu Michael ya miƙa wa Musharraf yana faɗin "James is my blood, i love him more than everything in my life, duk abun da James yake so ina son shi dan haka uncle ɗin James kayi zaman ka tare da James ɗin ka" nan fa Tga ya bugi kirji yace uban kuturu yayi kaɗan bare na makawo, ba zai taɓa yarda ba dole Musharraf ya bar gidan.

Miƙa hannu Musharraf yayi sukayi shaking hand da Michael, shi kuma James ya wuce ya haura sama ya bar Michael da Musharraf suna hira, su kuma su Tga suna surfa bala'i dole Musharraf ya bar gidan, kamar gidan su.

Part É—in Romeo James ya nufa dan yaje ya nemawa Musharraf takardan izinin zama a gidan, ko da ya shiga bedroom É—in Romeo sai yaga kamar Romeo na barci, ganin haka yasa sai ya juya a hankali zai fita, kamar daga sama yaji sexy voice É—in Romeo yace "James" da sauri ya juyo still idon Romeo a lumshe sai dai ba barci take ba

Da sauri James ya koma kusa da shi ya zauna yana faɗin "Please my lion wata alfarma nazo nema" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba, ci-gaba da magana James yayi dan yasan Romeo na jin sa sarai "Ina son ka bawa uncle na wadda na buge da mota takardan izinin zama a gidan nan dan su Uncle T da uncle Herry sun takura masa wai sai ya bargidan nan, ni kuma bana so ya tafi yanzu dan ya faɗa min bai da kowa" sai lokacin Romeo ya waro dara daran fararen idon sa tal kamar audiga masu ɗauke da kwayar ido blue, shiru ya ɗan yi kamar ba zai yi magana ba, sai kuma gently yace "Ba dai kai da Michael kuna son zaman shi a tare da ku ba?" Da sauri ya gyaɗa kai yana faɗin "Of course numa so" da hannu yayiwa James nuni da cikin drawer mirror sa, akan ya ɗauko takardan, cike da zumuɗi James yaje ya ɗauko takardun ya dawo ya miƙa masa, karɓa yayi ya ciri guda ɗaya ya miƙawa James ɗin yana faɗin "Ka kai masa ya karanta doka idan yayi agree fine ya sa hannu ka kawo min nima na sa hannu" da sauri James ya karɓa ya nufi waje.

Har lokacin sai surutu su Tga suke a kan lallai Musharraf ba zai zauna a gidan ba, ganin James ya dawo riƙe da takardan izinin zama a gida ne yasa sukayi tsit kamar babu kowa a palon, dan sun san lion ya amince kenan basu da wani bakin magana kuma, James kan ko a jikin sa yazo ya miƙawa Musharraf takardan yana faɗin "include we need your signature here" karɓan yar takardan Musharraf yayi ya fara karanta dokokin kamar haka, shekara nawa zaka zauna, hannu Musharraf ya miƙawa James a kan ya bashi bairo, ba musu James ya ciro bairo daga gaban rigan Tga ya miƙa masa, haushi kamar Tga ya shaƙe su daga James ɗin har Musharraf ɗin duk su mutu.

Wajen da aka rubuta shekara kawa zakayi, haka kawai Musharraf ya tsinci kan sa da rubuta 4 years bai yi tunain me zai je yazo ba, kawai ya damɓara shekara huɗu, doka ta biyu, idan ka sa hannun rayuwar ka ta zama a karkashin kulawar lion kuma sai abun da yace zakayi, Musharraf ya damɓara yes ba wani tunani, na uku, babu fita daga gidan nan babu zuwa ko ina sai da izinin lion, nan ma ya damɓara yes ya yarda kenan, na huɗu, baka isa kace zaka bar cikkin familyn William jacop ba har sai wannan shekaru da kace zakayi sun cika, nan ma ya damɓara yes, daga karshe ya sanya signature wato sa hannun sa, ya miƙa wa James, sai daɗi James yake ji ya wuce ya mayarwa Romeo takardan ya karɓa ya sa hannu sannan ya bawa James ɗin ya mayar in da ya ɗauko,

Su uncle ba karamin haushi sukaji ba wannan ma basu san cewa Musharraf musulmi bane wata kila idan sun sani sai kisa kawai zasu masa, dan haushi.

James na dawowa Palon ya wuce kitchen yaje ya sanar da sojojin dake musu girki a kan suyi miya da kifi yau, sun sha mamakin jin abun da James yace, amma basu da wani zaɓi abun da yan gida keso shi suke girka musu.
Chapter 116 · 0% Book details