← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 126

Sashe 104

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya kariso wajen su yana faɗin "Lafiya Hanan me ya same ki?" Cikin kuka Hanan ta fara yi musu bayani "Wani Alhaji ne dake yawan zuwa wajen nan sayan awara, yaya Sadiq ba ka san shi ba? Wannan mai farar ƙatuwar motar nan?" Gyaɗa mata kai Sadiq yayi yana faɗin "Eh na san shi me ya faru? Wani abun ya miƙi ne?" Ci-gaba da magana tayi tana kuka "To daman yace yana sona kuma ni bana son shi, kullun idan yazo nan ba sayan awara yake ba, kune kuke ganin kamar awara yake saya, hira kawai yake zuwa sai in ya tashi tafiya ya bani kuɗi, to ni bana karɓan kuɗin sa, ce masa nake bana so, yayi ta haɗani da Allah naki karɓa dan ni tsoron masu kuɗin nan nake, watarana baba yazo wucewa sai yaga Alhajin yana bani kuɗi naki karɓa yana roƙana na karɓa, shine da baba ya ga haka sai yayi sauri yazo shi ya karɓe kuɗi daga hannun Alhajin ba tare da an bashi ba, ya fara washe baki yana zubawa Alhajin godiya, Alhajin ya fito zai masa faɗa akan me yana bani kuɗi shi kuma zai wani sanya hannu ya karɓa, sai nayi saurin cewa Alhajin baba nane, shine Alhajin ya kyale sa ya kara masa wani kuɗin ma har da wani cewa baban ki kam ai baban nane, tun daga lokacin da baba yaga motar Alhajin yazo zai zo ya zauna a zaure yana jiran Alhajin ya bani kuɗi ya tafi shi kuma yazo ya karɓe kuɗin, ni wanna dukka bashi ne damuwa ta ba, damuwata shine kullun idan Alhajin yazo sai ya rinƙa yimin maganar banza, wai in munyi aure a ranar farko zai bani ciki, idan na nuna masa bana son maganar sai yace ai yana son ya koyamin yadda akayi ne tun yanzu dan na iya kar sai munyi aure naje na kasa yi masa abun da yake so, kuma sai ya rinƙa cemin ya kamata na rinƙa binshi muna fita zuwa hotel, ko gidan sa, bashi da wata magana sai na banza, idan nace bana so sai yace zai faɗa wa babana ina zagin sa, kuma kasan halin baba tun da Alhaji na basa kuɗi duk abun da Alhajin ya faɗa masa yarda zai yi ya haukai ya zauna ya kamani ya min duka, saboda tsoron hakan yasa kawai nayi shiru ina sauraron maganganun banzan da Alhajin yake faɗamin, jiya da daddare Alhajin yazo lokacin kuna cikin ɗakin mama kuna hira, baba yasa na fito dan muyi hira da Alhajin, dana fito Alhajin yace na shiga motar sa muyi hira naki, yace dole na shiga ai shi mijina ne tun da baba ya bashi aure na, kuma idan ban shiga ba sai ya faɗawa baba, ina tsoron ya faɗa wa baba shine na shiga na zauna, haka ya rinƙa taɓa min kirjina yana wasa da su har da gaba na ya rinƙa sa hannun sa yana wasa da shi, har yanzu sai zafi suke min, da kyar ya barni na dawo cikin gida bayan ya gama wasa dani, na rasa wazan faɗa wa, tunjiya da daddare nake kuka yau da zazzaɓi na tashi, babban abun da ya sake sani kuka yanzu, shine ina fitar da wanna murhun zan fara tuya, sai ga Alhajin yazo, wai jiya yaji daɗi kuma ya kasa barci na tayar masa da hankali dan haka na shirya anjima zaizo ya ɗauke ni, muje gidan sa mu ɗan huta, ina cikin faɗa masa ba zanje ba sai ga baba yazo zai shiga gida, da yaga Alhajin shine yazo suka gaisa, nan fa Alhajin yace masa wai yace zaizo ya ɗauke ni muje shopping ya sai min kayan arziki nace bana so, shine baba ya mare ni, ya rinƙa faɗa wai dole nabi Alhajin ko kwana ma yace zamuyi ba sai maje mayi ba, bare kuma kaya kawai zai saya min mu dawo, dan munafurci irin na Alhajin nan sai bawa baba hakuri yake wai baba ya dai na yimin faɗa baya so ana yiwa matar sa haka, sanna ya ciro kuɗi dayawa ya bawa baba ya shiga Motar sa ya tafi yana faɗin karfe ɗaya na rana zaizo ya ɗauke ni, baba kuma kuɗin ne kawai damuwar sa, yana karɓan kuɗi ya wuce cikin gida yana faɗin dole ma ta bika ai shegiya mai kashin tsiya arziki na bin ta tana gudu, abun yamin ciwo shiyasa nake kuka dan nasan idan nabi Alhajin nan wlh shikenan zai rabani da mutunci na" ta kai karshen maganar tare sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Ba laifi Jehan ta fahimci abun da ta fahimta a zancen Hanan É—in, ta gane in da zancen nata ya dosa, duk da cewa wasu abubuwan bata gane su ba, É—ago ido Jehan tayi ta kalli Sadiq.

Kara zaro ido tayi tana kallon Sadiq ɗin, lokaci guda kamannin sa sun sauya, idon nan nasa sunyi jawur zuciyar sa na tafasa ji yake kamar yaje ya shaƙe baban sa ya kashe sa dan haushi, tunani yake a ransa yanzu yana cikin gidan nan jiya wani katon banza yazo yana matse masa kanwa, wani ihu yayi kamar mahaukaci cikin fushi yace "Aina Alhajin yake?" Ita ma Hanan ba karamin tsorata da ganin Sadiq a haka tayi ba, dan tasan Sadiq mutun ne mai hakuri ga murmushi ba zaka taɓa ganin fuskar sa a ɗaure ba, duk damuwa da matsalar da gidan su ke ciki, kullun cikin murmushi yake.

Murya a dashe saboda kuka da tayi Hanan tace "Nima ban san in da Alhajin yake ba" a fusace Sadiq yace "Jehan tun da kin san hanya kije wajen aikin kawai, idan kin taso ki wuce asibiti, ni zan tsaya a nan ba yace karfe ɗaya zaizo ya ɗauke taba, to zan jirashi, idan kinje hospital ki gaishe min da gwaggo da jikin mum sai da yamma zan zo in ɗauke ki mu dawo" miƙewa tsaye Jehan tayi kafin tace "Yaushe ake tashi daga restaurant ɗin?" Shiru ya ɗan yi kafin yace "Inaga ku yan safe karfe ɗaya zaku tashi, sai yan yamma su karɓe ku, amma dai in kinje ki kara tambayar Ibraheem" jinjina kai Jehan tayi kafin tace "Okey koma karfe nawa ake sallamar mu, ni dai by 1 dole zan dawo, dan inason in bawa Alhajin nan capital warning" tsabar bakin ciki da ɓaci rai sun hana Sadiq bawa Jehan amsa, dan ji yake kamar zuciyar sa zata buga saboda haushin abun da Alhajin nan yayiwa Hanan.

Komawa Jehan tayi ta tsuguna ta gogewa Hanan hawaye, tana bata hakuri tare da mata alkawarin ba zasu bar Alhajin ya É—auke taba.

Sai da ta tabbatar Hanan tayi shiru sanna ta yiwa Sadiq sallama ta wuce bakin hanya dan tarar abun hawa ta wuce restaurant, yau asibiti ma sai ta taso daga restaurant zata biya ta can, gashi sai tunanin mum take, dan an shiga da ita É—akin da za'a mata aiki.

💞SUPER RESTAURANT💞

Tana shigowa kai tsaye reception wajen Ibraheem ta nufa, tun daga nesa Ibraheem ɗin ya hangota, ganin bata sanya uniform nasu ba yasa ya ɗaure fuska ya ɓata rai sosai, dan yasan ogan su ba zai yarda da rashin sanya uniform ɗin ba.

Tana karisowa wajen sa tun bata yi masa magana ba yace "Ina uniform naki? Me yasa baki saka ba?" ÆŠaure fuska sosai ita ma tayi kafin tace "Ai tun jiya na faÉ—a maka ba zan sanka uniform É—in ba, au kai daman ka É—auka wasa nake maka, to idan ma baka sani ba ka sani ni Jehan bana faÉ—an abun da nasan ba zan aikata ba, garama kasani tun yanzu idan nace ba zanyi abuba tofa da gaske nake ba zan yi shi bane" tsabar haushi Ibraheem bai san lokacin da ya É—aga hannu kamar zai mare ta, sai kuma ya dakata yana wani huci, yariya yar karama kamar wanna ta tsaya tana faÉ—a masa magana, gently tace "Ya ka dakata? Ai da ka marenin ina ga zai fi" shiru Ibraheem yayi yana mai dana sanin taimaka mata da yayi.

Ganin yayi shiru ne yasa tace "Menene aiki na? Ka faÉ—a min naje na fara yi dan ina son tafiya gida karfe É—aya dai dai" zaro ido yayi yana kallon ta da mamaki, wato ita ma zata yanke wa kan ta hukunci ga lokacin da zata tafi cab lallai aiko aiki dole na koyawa yarinyar nan hankali.

A fusace ya buÉ—e baki zai yi magana, wayan dake gaban sa saman table ta fara kara, dogon tsaki yaja tare da sa hannu ya É—auki wayar, irin wayar nan ne da ake ajiyewa saman table wadda costumers ke kira dan bukatar abu. Picking na call É—in yayi tare da kara wayar a kunnen sa.

Jim kaɗan ya ajiye wayar ya ɗago ya kalli Jehan yace "Kije room 22 akoi wani costumer da yake bukatar ma aikaci ɗaya" rai a ɓace tace "to me zan masa" mai da wayar yayi ya ajiye yana faɗin "Idan kinje ai koma menene zakiji" guntun tsaki taja ta wuce ta tafi ta bar Ibraheem da binta da ido yana mamaki.

Ko da taje bakin kofar Room 22 É—in sai da taja dogon tsaki kafin tayi knocking na kofar, bugu É—aya tayi aka buÉ—e kamar daman jira ake.

Wani Alhaji ne kato bakin kirin da shi gashi da katon ciki, yana sanye da gajeren wando, kaya ya miƙo mata yana faɗin "Wanki ne zaki min" zaro ido tayi ta kalle sa kafin ta kalli kayan dake hannun sa yake miko mata, singlet and boxers ne, dawo da kallon ta kan face nasa tayi a kule tace "Yanzu saboda baka da hankali nice zan wanke maka shot naka? Ko kunya baka ji ba kato da kai, hauka nake zan wanke wandon kato kamar ka, tab lalai to Jehan dai ba za tayi wanna kazantar ba sai dai wata, daman wanna aikin shine aka kawo ni nayi, to wlh ba zata saku ba, ba zan iya ba"
Chapter 104 · 0% Book details