Sashe 96
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Faɗuwa kasa Amarya tayi tare da dafe cikin ta tasa ihu makircin tana birgima, har sai da baban Sadiq mijin hajiya ya fito daga ɗakin amarya, da sauri yayo gunsu yana faɗin "Wani ɗan tsinanniyar ya taɓa ki" duk da Jehan bata san me ya faɗa ba ta fahimci kamar zagi yayi dan haka sai tace "hy Old man be careful don't angry me" da yake baban Sadiq kai ɗin fanko ne babu komai a cikin ta sai mugun ta da jahilci da bala'i, sai bai san ma me Jehan ta faɗa ba, kawai wajen amarya ya nufa abun sa, yana ta surfa ruwan bala'i.
Nan amarya ta kwashi karya da gaskiya ta faÉ—a masa, har da ce masa Jehan da Sadiq sun ce zasu kashe ta da daddare, dan haka ya kore su daga gidan nan, Allah sarki maman Sadiq baiwar Allah nan take idon ta ya cika da hawaye dan tasan tsab baban Sadiq zai iya korin Sadiq daga gidan, itama dai maman Hanan idon nata da hawaye, dama kuma ita hawayen tun É—azun yake idon ta saboda hayakin itacen da take kokarin hurawa ya kama yaki, saboda itacen É—anyune.
Shi kan shi Sadiq sai da yaji wani iri dan bai son nisa da maman sa, kuma idan baban sa ya kori su Jehan yanzu ina zasu je, basu da kowa basu da komai.
Shi kuwa baban Sadiq sai wani cika yake yana batsewa yana lallaɓa amaryar sa yar gold yana bata hakuri, shegiya Naira, kuɗi sun haukata baban Sadiq Allah ka rabamu da iyaye masu son duniya.
Cikin kukan makirci amarya tace "Wlh ba zan zauna a gidan nan da wayan nan yaran ba, dole su bar gidan nan, marina fa wannan mayyar yarinyar tayi, kuma wanna shegen yaron Sadiq har da ce mata, wai ta ƙaramin wani marin dan bani da kunya ya tsaneni kuma sai ya kashe Ni, ni shegiya ce, ba dai irin zagin da basu min ba" Allah sarki Sadiq bawan Allah zaro ido waje yayi, yana mamakin kalaman amarya na sharrin da take musu, ita kuwa Jehan tana tsaye ne kawai ta zuba musu ido amma ba wani abun da take ganewa a maganganun nasu.
A fusace baban Sadiq yace "Yanzu kuwa zasu bar gidan nan, yan iskan yara, ai daman ba ƴaƴan albarka bane, wlh ba wanda ya isa ya taɓa ki ya zauna lafiya, ku fice min daga gida, daga ku har iyayen naku ban son ganin kowa" wayyo Allah kuɗi ta rufewa baban Sadiq ido baya ji baya gani sai zancen amarya ne kaɗai ke shiga masa kunne.
Nan fa Sadiq da maman sa suka shiga bawa amarya hakuri, ita kam Jehan tana tsaye.
Ganin maman Sadiq ta tara hawaye a ido ne yasa Jehan ta fahimci a koi matsala, dan haka sai ta matso tana tambayar maman Sadiq meke faruwa suke kuka.
Maman Hanan dake cikin Kitchen ita ce ta fito, kasan cewar ta ɗan yi karatu zuwa Jss 2 sai ta yiwa Jehan bayani cikin kwaɓaɓɓiyar turancin ta
Ba laifin duk da turancin na maman Hanan sai a hankali, amma Jehan ta fahimtar, dan haka sai ta ɗago kai ta kalli Sadiq kafin ta mai da kallon ta kan baban Sadiq dake ta surfa uban bala'i, karo na farko a rayuwar ta da taji ba daɗi dan zatayiwa baban Sadiq rashin kunya, amma bata da zaɓi dole ta koya masa hankali dan ta lura bashi da hankali.
Duk wani Hausar da ta iya ranar sai da ta tattaro shi dan tayiwa baban Sadiq magana yadda zai gane, cikin fushi ta fara magana "Babu in da Sadiq da maman sa zasu je, idan ma baka son ganin su a gidan ne, tofa sai dai kai ka fice daga gidan, dan sune da gidan yanzu, ke kuma stupid wlh ina nan gidan babu in da zanje sai na baki tarbiya tun da iyayen ki basu baki ba, da kake cewa mu fita maka a gida, haya muka biya ka, kuma munyi da kai sai after 1 year dan haka sai 1 year ta cika zamu bar gidan nan, da bana son gidan ka amma yanzu dan na baku tarbiya kai da wanna stupid ɗin dole zan zauna a nan, islamikali baka isa ka kori Sadiq daga gidan nan ba, maman Sadiq dai kana da damar ka koreta, amma ban da shi, islamikali sai dai kai ka fita ka barmusu gidan ba dai Sadiq ya fita ba, kuma idan kayi wasa wlh sai fushin Allah ya hau kan ka, a kan cewa da kake zaka kori ƴaƴan cikin ka daga gidan ka, mu kuma da muka kama haya, zaka iya kai mu court, a nan ne zakaga asalin yadda ake duniyan ci, amma fita gida bazamu fita ba, ina binka ta lalama ne because of your son, Sadiq is a nice person, if not wlh dana sanya ka kayi regretting abubuwan da kake wa bayin Allah nan, ke kuma stupid daga yau a gidan nan idan kika sake shiga harkan wani ko wata a cikin gidan nan wlh I will make you regret" ta kai karshen maganar tare da jan tsaki, ta juya zata wuce ɗakin maman Sadiq, a fusace Amarya ta jawota har sai da tayi baya zata faɗi, cikin fushi ta juya ta damko wuyar amarya ta shaƙe ta da karfi, rai a matukar ɓace tace "Ke na lura baki san magana ta hankali ba, bari ma miƙi da yaren ku na marasa kunya ta hakan zaki fi gane wa" hannu baban Sadiq ya kai zai mari Jehan ɗin, da sauri Jehan ta kauce tare da sakin wuyar amarya, ta juyo a fusace za tayiwa baban Sadiq tsawa, idon ta ya sauka kan face ɗin Sadiq, dogon tsaki taja kawai tasa kai ta wuce ɗakin maman Sadiq.
Amarya anji shaƙa sai zaro ido take ta kankame wuyar ta, bin bayan Jehan Sadiq da maman sa sukayi suka bar baban Sadiq da amarya a wajen, itama maman Hanan wuce wa tayi abun ta ta kyalesu nan wajen.
Kuka amarya tasa tana faÉ—in "Wlh gidan mu zan tafi ba zan zauna da kai ba, kuma karka kuskura naga kafarka a gidan mu, in dai ba ka kori wayan nan yaran ba" baban Sadiq anji kunya yarinya karama ta tsaya tana tsara masa magana har da gargaÉ—i da sharaÉ—i, yarinyar da Sadiq ma ya fita a shekaru, amma saboda son abun duniya, jikin sa har kerma yake yace "Yanzu kuwa zan kore su dan Allah kiyi hakuri ki dai na zancen komawa gidan kun nan, idan kika tafi ina zan sanya kai na" ya kai karshen maganar tare da nufan kitchen ya É—auko itace daga cikin murhun maman Hanan, kai tsaye ya nufi É—akin maman Sadiq, Jehan na zaune kusa sa yar katifar maman Sadiq shi kuma Sadiq yana zaune ta bakin kofa saman wata yar kujera, ita kuma maman Sadiq tana zaune saman katifar.
Kamar wani mahaukaci haka baban Sadiq ya faÉ—o É—akin yana faÉ—in "Kuzo ku fice min daga gida ko yanzun nan na kashe ku É—aya bayan É—aya, yan iskan banza marasa albarka, yarinya uban ta ya sai muku gidan da zaku tsugunna saboda rashin albarka ku sata a gaba kuyi ta duka kamar an kawo muku jaka, to wlh baku isa ba, ko kuzo ku wuce ku fita ko kuma in make ku da icen nan.
Miƙewa sukayi dukkan su jikin maman Sadiq har kerma yake, Jehan kuwa shiru tayi tana tunanin yadda zata ɓullo wa baban Sadiq, can kome ta tuna, tace "Baban Sadiq we are so sorry zuwa gobe zamu barmaka gidan gaji, kuma kuɗin hayan ma da muka baka mun barmaka kyauta gobe da safe zan kara maka wani kuɗin ma" nan fa baban Sadiq ya fara dariya yaji an basa kuɗin hayan kyauta, kuma za'a kara masa wani, a tunanin sa abun da Jehan ta faɗa masa haka ne, bai san halin Jehan ba ne.
Sai washe baki yake ya fito daga ɗakin tare da yin wurgi da itacen hannun sa, ya karisa gaban amarya, yaje ya lallaɓa ta itama ya bata baki, da kyar ta yarda a kan gobe su Jehan zasu bar gidan, ta wuce suka koma bedroom nasu.
Kallon Jehan Sadiq yayi yace "Me yasa kika cewa baba haka?" Guntun tsaki Jehan taja kafin tace "I'm sorry to say baban ka yana bukatar a gyara masa zama da kyau, kuma dole muyi hakan, yanzu dai ka kira Yusuf da Sha'aban, cikin dare irin 1 na dare kuyi dressing irin na manyan aljanu, ku shiga ɗakin baban naku, sai kuyi kamar ɓarayi ne ku, kada ku bari ya ganku, koda kun boye fuska kada ku yarda ku haska jikin ku da torchlight ya ganku zai iya gane ku idan ya ga jikin ku, ku tabbatar kun zane fuskokin ku ya zama irin na Magicians, sai ku shiga room ɗin, ku shaƙe murya ya zama irin na aljanu, ku masa barazana a kan idan ya sake shiga harkan wani daga cikin gidan nan sai kun dawo kun kashe shi, haka zaku masa zaku samu zaman lafiya da shi, ko bai zauna da ku dan Allah ba, ya zauna da ku dan tsoron aljanu karsu kashe sa" tayi maganar duk a kwaɓe sai haɗe words take, amma ba laifi Sadiq ya fahimci hausar nata.
Jinjina kai yayi kafin yace "Anya kuwa hakan zai yiwu? Baba fa wlh bayi da tsoro" "try it, zai yiwu" Jehan ta bashi amsa tana komawa ta zauna, to kawai Sadiq yace mata amma cikin zuciyar sa yana É—ar É—ar yadda abun zai kasance.
Kamar yadda Jehan ta basu shawara haka suka yi, ta saman cilip É—in palon amarya ta baya suka shiga, sunyi dressing kamar wasu bokaye duk sun shafe fuska da toka da gawayi kamar ba lafiya ba, haka suka cire cilip É—aya suka shige.
Kai tsaye wajen baban suka nufa, sai sharan barci yake saman gado amarya mai laushi, ya buÉ—e bakin nan kamar ka tsula masa fitsari a ciki, sai minshari yake