Sashe 107
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana shigowa part ɗin nasu, da sauri ya wuce ɗakin baba, a nan ya isko su Ayla sai faman shasshekar kuka suke, kusa da su ya musu sannan ya dubi baba yace "Baba ku dai na damuwa dan basu kashe Rismha ba, sun rufe tane a ɗakin duhu na Queen dan ba zai yiwu su yanka ta yanzu ba, saboda Queen zata yi tafiya zuwa kasar Israel tace ranar da zata dawo ranar take bukatar a mata ferfesun naman Rimsha, yanzu abun da nake so da kai baba, ni dai kaga ba cikakken mutun ne kamar ku ba, rabi mutun rabi aljani nake, shiyasa tsafin su baya kamani, yanzu zan musulunta saboda Rimaha dan mu cetota, ba kunce duk abun da kuka roki Allah ku zai muku ba?" Gyaɗa masa kai baba yayi "To na san dai su Queen ba zasu bari kuyi wani abun addini a nan ba, zasu rufe muku baki, ku rinƙa roka mana Allah a ranku nasan zai ji kukan mu, amma akoi wani abu ɗaya da nake so ka sani, zan gwada karfin tsafi na na tsinke sarakunan da aka ɗaure Rimsha da su, daga nan zan fitar da ita daga ɗakin zuwa nan, to ina son ka sani dole da tsafi zan yi wannan kuma ina son ka roka mana Allah da ya kawar wa da Queen tunanin cin naman Rimsha, su kyale ta su manta da ita" sosai baba yaji daɗin zancen duna, farinciki fal ransu baba da Mustapha suka rinƙa sawa duna albarka suna masa fatan alkhari da fatan nasara
Har ya miƙe zai fita, sai kuma ya dawo yace "Baba kafin muyi duk wanna aiki fa sai mun fara mantar da su wace ce Rimsha idan ba haka ba, muka ɗauko ta muka dawo da ita ma mun kira mutuwar mune gaba ɗayan mu dan dukkan mu zasu zo su kashe mu, yanzu zanje mayi aikin mantar da su komai shiyasa nace kuyi mana addu'a, sanna ba lallai na iya kai labari ba, dan tsafin su yafi nawa karfi, kuma idan nayi kuskure suka kama ni to wlh nasan kashe ni kawai zasu yi, dan haka tun yanzu muyi bankwana, zan iya mutuwa a kowani lokaci, amma ba zan mutu ban fitar da Rimsha daga fadar Queen ba" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin, sai daɗi su Ayla suke ji Rimsha zata dawo, sai addu'a suke mata a ransu.
A ɓangaren Rimsha kuwa, wani ɗaki ne mai bala'i duhun gaske suka kai ta, baka iya ganin komai a ɗakin saboda tsananin duhun dake ɗakin, ga wani fitinannen wari da karnin bala'i dake tashi a ɗakin, ga shi ɗakin ba'a zama sai dai tsayuwa kasan cewar kasan wajen wasu kifiyoyi ne masu bala'i kaifi da tsini a suke a wajen, iya in da suka tsayar da ita, iya wajen ne babu wayan nan kifiyoyi masu tsinin bala'i wadda suke iya fasa nama har kashi, sanna sun ɗaure ta da sarkoƙi masu bala'i karfi, sarka ne wadda aka yi shi da dafaffiyar karfe wadda babu wani abun da ya isa ya tsinƙa sa, da gani kasan wanna sarka na tsafin sune, farko da suka ɗaure ta da ta gaji da tsayuwa ta matso da kafar ta tana son zama
Tana sako kafar ta kasan wajen wayan nan kifiyoyin suka cake mata tafin kafar ta har ciki kusa da kashin kafar ta, kan kace me jinin ta ya fara malala a wajen, Allah ma yasa bata ida sauke kafar ta a wajen ba shiyasa wayan nan mayun kifiyoyi basu mata illaba sosai ba, ta gaji da tsayuwa ga yinwa da kishin ruwa, ga bala'i duhu gaske, gashi yanayin É—aurin da suka mata dole ta gaji dan sun buÉ—e mata hannu ne suka mata É—aurin cros É—ayan hannun ta yayi gabas É—ayan kuma yayi yamma, kafafun ta kuma sun haÉ—e su waje guda saboda wayan nan kifiyoyin, ba halin tayi wani motsin kirki, tayi kuka har ta godewa Allah, ga bala'i zufa da ke damun ta, saboda É—akin babu hanyar da iska zata shiga sosai,
Tun tana iya kukan gajiya da yinwa da kishin ruwa har ta hakura ta fawwalawa Allah lamuran ta, dara daran sleeping eyes nata sunyi luhu luhu saboda kuka, duk sun kunbura sunyi jawaur da su, babban tashin hankali na biyu bata iya kiran sunan Allah, da zarar tayi yunkurin kiran sunan Allah sai Queen ta shaƙe mata maƙogwaran ta tayi ta fama tana shan azaba tana kuka, sai bayan wani ɗan lokacin sanna Queen ta sake ta, saboda wahalar da take sha wajen furta sunan Allah yasa ta dai na yunkurin furtawa ma kwata kwata, tayi shiru ta hakura tana kiran Allah'n a ranta, Allah sarki baiwar Allah, duna kuwa yana can yana kokarin fitar da ita da tsafin sa, dan shima abun ya sha kan sa yafi karfin tunanin sa, domin shu'umancin Queen ya wuci tunanin mai tunani.
Wannan kenan mu leƙo Washington DC mu dawo
💞 WASHINGTON DC💞
4:00am
Tsaye Romeo yake a balcony bedroom nasa ya goya hannun sa a saman kirjin sa ya zubawa garin nasu ido, yayin da iska dake kaɗawa yana ta watsa masa dark black curly hair sa kasan cewar bai ɗaure gashin nasa ba, jikin sa sanye da Ripped Jeans blue da Round neck polo shirt fara kal kamar yanzu ya ciro ta daga kwali, kasan cewar rigar nasa mai ƙaramin hannu ne hakan ya bada damar bayyanar murɗaɗun damatsan hannun sa, wayan dake cike kamar zasu fashe saboda ɗaga barfe da yake sosai, fuskar nan tasa kamar an aiko masa da sakon mutuwa a ɗaure take tamau babu alamar ya san menene dariya, hannun sa na ɗaure da diamond watch na su na Triplets, sai faman cizan lallausan lips nasa yake, alamar wani tunani yake
yana yin yadda iskan nan ke kaÉ—a masa wanna dark black curly hair nasa abun gwanin ban sha'awa, domin har fuskar sa gashin ke bazo masa, Brady na kwance daga É—an nesa da shi kusa da wata yar karamar pool dake wajen, sai kallon cikin ruwan Brady yake, yanayin nasu dai gwanin burgewa da ban sha'awa tare da É—aukan hankali mai kallo.
Almost 30mins yana tsaye a wajen shiru kamar ba shi a wajen, wayar sa dake É—aure saman wata haÉ—aÉ—iyar karamar bed na kwanciya ka huta dake kusa da pool É—in ne ta fara kara, tamkar bai ji ringing É—in wayar ba yayi shiru, bai yi wani motsi da zata nuna yaji ringing É—in ba, wayar ta katse kira na biyu ya shigo, haka kawai ya tsinci kan sa da jin yanayi mara daÉ—i a jikin sa, slowly ya juyo ya nufi in da wayar take, yana taku irin na jaruman maza, gently ya É—auki wayar yana bin screen É—in da kallo, heartbeat wato Michael shine sunan da ya bayyana a kan screen É—in wayar, ganin sunan Michael yasa yaji wani irin yanayi mara daÉ—i ya karu a jikin sa, a nitse yayi picking call É—in tare da kara wayar a kunnen sa yayi shiru yana sauraron Michael É—in.
"Hello lion" shiru Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, ci-gaba da magana Michael yayi dan idan da sabo sun saba, kuma yasan Romeo É—in yana jin sa "Lion I'm feel like I'm not feeling fine, tun É—azun ina jin jiki na yana min zafi zuciya na yana bugawa da sauri sauri gaba na yana faÉ—uwa kamar ba lafiya ba, na rasa meke min daÉ—i yanzu zan bar white house in dawo gida kawai" shiru Romeo yayi na É—an lokaci kafin yace "okey come back now" to Michael ya amsa da shi, a tsanake Romeo ya katse kiran tare da mai da wayar ya ajiye saman wannan bed É—in, ya koma in da yake tsaye ya tsaya tare da zura hannayen sa a aljihun wandon sa, yayi shiru yana tunanin meke damun Michael.
Tsayuwar 20mins yayi a wajen wayar sa ta sake fara rururi, shiru yayi yana jin yana yi mara daÉ—i a jikin sa, har wayar ta katse bai É—aga ba, kira na biyu ya shigo, haka kawai ya tsinci kan sa da baya son É—aukan kiran, shikuwa mai kiran nasa ya nace kamar dama yasan halin Romeo baya É—aukan kira da wuri idan a ka masa, musamman idan yana wani abun sai ayi ta kiran sa ba zai É—auka ba har sai ya gama abun da yake yi, baya haÉ—a abubuwa biyu lokaci guda a nitse yake yin komai nasa, ko tunanin wani abu yake aka kirasa tofa koma wanene mai kiran dole ya hakura har sai ya gama tunanin sa sannan.
Ganin mai kiran nasa yaki dai na kiran ne yasa ya juyo gently ya nufi wajen wayar, dan ya kai 10 miss call mai kiran ya masa.
Tyrone Shine sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar, lumshe dara daran ido sa yayi nan take zara zaran eyelashes nasa suka kara bayyana gwanin burgewa, a hankali ya sake buɗewa idon a kan screen ɗin wayar, gently ya kai hannun sa kamar bai son taɓa screen ɗin yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnen sa yayi shiru bai yi magana ba
Daga ɗayan ɓangaren Tyrone yace "Oga we are done the mission kuma munyi waning, mun kashe kowa dake wajen, sai dai akoi wani abu ɗaya da yake ɗaure mana kai" shiru Romeo ya ɗan yi kafin yace "What is this?" Cikin sauri Tyrone yace "Your watch sir, bayan mun kashe kowa, muna kokarin tattara bayanai da wasu evidence mun samu wani watch a wajen irin na hannun ka sak kamar shi ne ma" zaro blue eyes nasa waje yayi har sai da suka kara kwalli saboda zaro su da yayi
Da É—an karfi yace "What?!!" Sorry sir kawai Tyrone yake faÉ—i "Ku kawo min watch É—in gida yanzun nan" ya faÉ—a tare da sauke wayar daga kunnen sa ya nufi hanyar komawa cikin bedroom nasa, daga nan ya fice daga bedroom É—in gaba É—aya ya sauka palon kasa.