← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 126

Sashe 123

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Sadiq suna fita Jehan ta tashi taje tayi wanka Allah sarki yanzu har ta saba da wanka da ruwan sanyi, bayan tayi wanka ta fito ta dawo ɗakin maman Sadiq, already maman Sadiq ta jima da yin barci abun ta, kayan barcin ta ta ɗauko riga mai laushi da dogon wando ta saka a jikin ta ta ɗauki mayafin lulluɓa da maman Sadiq ta bata ta kwanta ta lulluɓe jikin ta, sai bayan ta kwanta sai ta tuna kamar basu yi Sallah ba, tana kokarin miƙewa sai kuma ta tuna ashe sunyi a asibiti, addu'ar barci kawai tayi ta kwanta, ta lumshe ido tana tunanin Rimsha tana hawaye kamar kullun har barci yayi awon gaba da ita.

Asuba ta gari. Mu leƙo Washington DC mu dawo

# 💞WASHINGTON DC💞

80:00am

Slowly ya waro dara daran blue eyes nasa masu ɗauke da barci, kasan cewar idon nasa akoi alamar barci bai isshe shi ba, sai idon nasa ya kara kyau dan yayi yanayi da sleeping eyes, wani azaban duka kirjin sa tayi lokaci guda wadda yasa yaji barcin ta watsake ta sake sa, miƙewa yayi zaune a tsakiyar gadon ya dafe saitin faffaɗar kirjin sa, da sanyayyar murya mai bala'i daɗi da kwatar da hankali mai sauraro yace "Meke shirin faruwa da nine" dan bai taɓa jin makaman cin wannan bugun zuciya ba a tattare da shi, shiru ya ɗan yi na ɗan lokacin kafin ya yaye bargon jikin sa a hankali ya zuro zara zaran kyawawan fararen kafafunsa kasan bed ɗin sannan ya miƙe ya nufi toilet.

Wanka yayi ya fito ya shirya cikin wani haÉ—aÉ—en jeans mai bala'i kyau da tsada launin baki da High neck sleeve shirt launin blue kasan cewar rigar ta kama jikin sa sosai, hakan ya bayyanar da kakkafar suran kirjin sa, faffaÉ—ar kirjin nan nasa abuÉ—e take sosai cikan damatsan hannun sa yasa faffaÉ—ar kirjin nasa ta kara buÉ—e wa sosai, har wannan bul bul É—in breast nasa kana iya hangowa saboda kama shi da rigan tayi, ba karamin kyau kayan suka masa ba, kamar dan shi akayi su, Winter Sports Hat ya sanya a kan sa, bayan ya É—aure dark black curly hair sa, ya fito yayi kyau over ita ma hulan ta masa kyau sosai, sai dai ya bar wannan É—an guntun gashin gaban goshin nasa a waje bai shigar da ita cikin hulan ba, fuskar nan nasa a É—aure take kamau kamar kullun sai dai na yau ma tafi na kullun, dan ina ga yau idan sukayi ido huÉ—u da mai karamain zuciya nan take zuciyar zata buga ya mutu awajen saboda tsoron yadda fuskar lion tayi yau abun ba'a magana ya wuci tunanin duk wani mai tunani, sai tashin fitinannen kamshi yake, hannun sa na É—aure da diamond watch nasu na Triplets, kyawawan kafafun sa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal wadda a kalla kuÉ—in sa ya kai $76000, kasan cewar takalmin launin baki ne sai yayiwa farar kafar sa bala'i kyau, wayar sa da kuma laptop na sa ya É—auka ya nufo waje, yana taku irin na manyan jarumai, ko baka gan shi ba kaji sahun takun sa kasan cikkaken namiji ne mai jini a jika kuma lafiyayye kakkafa ne ke tinkaro ka.

Lokacin da ya fara sako kafar sa a benen sauƙowa palon kasa, ji kake tsit duk wani halitta mai rai dake cikin palon ya nitsu tsit sun sha jinin jikin su, wasu daga cikin bodyguards kam jikin su har kerma yake saboda tsoron sa,

John, Jay, uncle Herry, Tga, gaba É—aya suna palon kasan, sun zauna kamar masu jiran wani abun kowannen su yana ta faman latsawa waya cikin kwanciyar hankali, lokacin da kamshin perfume na lion ya kai musu karo a hancine yasa sukayi saurin ajiye wayoyin nasu suka nitsu suna satar kallon sa ta kasan ido dan shi baya son yawan kallo, sai yaga kamar wani abu kake kallo a jikin sa hakan yasa idan ya kama ka kana kallon sa sai ya maka hukunci mai tsanani.

wucewa yayi ko kallon in da su John suke bai yi ba ya nufi hanyar ficewa daga palon, har suna haÉ—a baki wajen rige rigen É—aga masa gaisuwa, bai amsa gaisuwar ko É—aya daga cikin suba dan dama ba amsawa yake ba sai dai ya É—aga musu hannu dan magana na masa wuya, to yau kam ma ko hannun basu samu arzin ya É—aga musu ba dan hankalin sa kusan baya tare da shi.

Dai dai zai fita palon yajiyo muryan dad da Michael har suna haÉ—a baki wajen tambayar sa ina zai je, juyowa yayi yazo ya rungumi daddy tare da mannawa daddy kiss a kumatu kasa kasa yace "I need your prayer my dad" daddy sarki saurin razana ya É—auka yaki Romeo zai tafi nan take jikin sa ya fara kerma cike ta tsoro yace "Where are you going my lion?" Kasan cewar sun san halin dad sai bai faÉ—a masa abun dake faruwa ba ya basar da maganar ta hanyar cewa zai je wajen friend na sa ne dad karya damu kawai ya yi musu addu'a, ajiyar zuciya dad ya sauke kafin yace zai faÉ—awa pastor ya musu addu'a, wucewa Romeo yayi zai tafi, sai kuma ya sake juyowa ya shafa kan Micheal dake tsaye yana kallon su, shi dai Michael duk da ba ilimi gare saba yasan ba lafiya ba, dan yana ji hakan a jikin sa, daman kuma ko ciwon kai É—aya daga cikin triplets yake tofa sauran sai sunji a jikin su, hakan yasa yau tun da suka tashi barci zuciyar Romeo ke bugawa da karfi karfi, shi kuma Michael yana fama da faÉ—uwar gaba da kasala wadda ta haifar masa da ciwon kai, sai Allah kaÉ—ai ya san shi kuma James me yake ji.

Wucewa Romeo yayi cikin sauri ya fice daga palon, yana fita rundunar jinga jibgan sojojin sa suka fara sara masa, sunyi layi a bakin kofar palon da alama jiran fitowar sa suke.

Wuce su yayi ba tare da yayi wani alama ma da zata nuna ya gansu a wajen ba, kai tsaye wajen shirga shirgan motoncin da aka jera musu ya nufa, motoncin manya manyan masu numfashi, na sojoji guda 8 sai wata dan kareriyar motar fara tas har wani kyalli take kirar Bugatti La voiture wadda a kalla kuÉ—in ta ya kai $18.7 million, jikin motar kawai abun kallo ne dan ta tsaru iya tsaruwa, idan ka shiga cikin motar nan sai ka rantse da Allah a cikin manya manyan haÉ—aÉ—un palo irin na manyan shuwagabannin kasa kake, saboda haÉ—uwa irin na cikin ta, kujerun motar irin manya manyan kujerun nan ne masu mumfashi wadda suka amsa sunan su kujeru, har wani lotsawa ciki suke idan ka zauna a kan su, sai wani fitinannen kamshi mai bala'i daÉ—i ke tashi daga cikin motar nan, saboda ansan mamalakin motar ma'abocin son tsabta da kamshi ne shiyasa komai nasa yake kasan cewa mai kamshi da tsabta.

Da taku irin na jarumai sadaukan yaki ya nufi motar, yayin da jibga jibgan sojojin sa ke take masa baya

Wani jibgegen katon Baturen soja fari tas da shine yayi gudu ya sha gaban lion ya buÉ—e masa gidan baya na wannan farar Bugatti La voiture noira, gently lion ya shiga cikin motar ya zauna, dan shi komai nasa a nitse yake yin sa, daki daki yake bin komai

Sai da wannan sojan ya É—aga hannu ya sara masa sannan ya rufe kofar motar

Ji kake dip dip sojojin sa suka nufi motoncin su da gudu suka haye saman bayan motoncin nasu, wannan sojan daya buÉ—e wa lion kofar mota ya shiga, shi ya ja motar lion É—in.

A tare motoncin suka tashi suka nufi gate É—in fita gidan, duk in da suka wuce sara musu sojojin dake tsakar gidan suke.

Suna fita wajen gidan suka saki jiniya kamar yaki zasu tafi, abun da ya sa basu saki jini tun a cikin gida ba, saboda daddy, yana jin jiniya zai ruÉ—e yace yaki Romeo zai je ko wani wajen, shiyasa suka bari sai da suka fita waje sannan suka saki jiniyar.

Duk wata mota ko abun hawa dake hanya kaucewa suke su bawa tawagar jerin kwanon motocin The general of the army hanya, wasu ma jiniyar kawai suke ji tun daga nesa, tun bai iso su ba suke sauka daga kan titi da abun hawan su su bada hanya

Ko da tawagar motocin suka zo wajen fitillar bada hannu, a sukwane mai kula da fitillar wajen ya basu hanya dan su wuce dan yasan ma ko bai basu hanya ba ba tsayuwa zasu yi ba, dan in tawagar motocin The general of the army suka tinkaro waje tofa sai dai ku ku hakura sai sun wuce.

Cikin kwanciyar hankali yake danna laptop nasa ga sanyin Ac na ratsa shi, sai faman cizan lallausan laɓɓan sa yake, ga lips ɗin nasa ya kara yin jawur kamar yasa lipstick saboda ciza su da yake, duk wannan latsa laplop da yake hankalin sa na can duniyar tunani ina James yaje, dan shi har yanzu yaki yardan wa zuciyar James criminal ne, duk lokacin kuma daya tuna James sai yaji zuciyar sa ta bada dum dum ya rasa me matsalar, kokarin sake bin diddigin layin James yayi abun mamaki sai yaga layin a kashe bayan a kashe ma an soketa daga hanyar sadarwa gaba ɗaya, cike da tashin hankali ya ciro wayar sa ya fara kiran layin, kwata kwata layin an suke ta, zaro idon sa waje yayi yana tunanin meke shirin faruwa ne, taya za'ayi ace an soke layin James gaba ɗaya bayan jiya da daddare lafiya lou layin take, to me ya faru da James ɗin?.

Yana cikin tunani bai san lokacin da suka isa *Dulles International airport* ba sai da yaga jibga jibgan sojojin sa sun kewaye motar sa da manyan bindigun su, sannan ya farga, sojan daya tuƙo sane ya fita ya buɗe masa kofar motar suka tsaya cirko cirko suna jiran fitowar sa
Chapter 123 · 0% Book details