← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 126

Sashe 69

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusa da Romeo yazo ya zauna yana faɗin "Good morning My lion" shiru Romeo ya ɗan yi na yan sakanni kafin yace "Morning uncle how are doing this morning?" Fuska a ɗaure TGA yace "I'm fine what of you?" Shiru Romeo ya masa bai sake magana ba, cikin girmamawa Jame da Michael suka haɗa baki wajen cewa "Good morning Uncle" murmushi TGA yayi kafin yace "My Tiger, your eyes is shiny like Tiger eyes" kara lafewa a gado Michael yayi yau da alama yan shagwaɓan nasa suna gaban goshin sane, sai wani narkewa yake yana wani yauƙi

hannu uncle TGA yasa suka fara breakfast tare da Romeo, yayin da shi kuma James ke zaune yana ta aikin serving na su, duk abun da suka nuna sai ya zuba musu

cikin nitsuwa Romeo ke cin abincin sa hankali kwance, kamar bai son taunar abincin haka yake ɗan tauna, shi kuma uncle TGA sarkin sauri komai nasa sauri sauri yake ayi kawai a wuce wajen, ya riga Romeo ma gama cin abin cin, james ya miƙo masa tissue paper ya ansa ya goge bakin sa sannan ya miƙe ya nufi dressing room na Romeo, yayin da shi kuma Romeo yake taunan abincin cikin class da kwanciyar hankali kamar bai son tauna haka yake ɗan motsa lausasan laɓaɓɓan sa.

Jim kaɗan Tga ya fito sanye da face mask a face ɗin sa, sai dai ya gangaro da face mask ɗin zuwa gemun sa bai sanya dukka ba, kai tsaye gadon Romeo ya nufa, cike da so da kauna ya mannawa Michael kiss a goshi yana faɗin "Ilove you my Tiger, take good care of yourself" kamar Tga yace ya kara lafewa a gado haka ya kara rungume pillow yana ɗan turo baki yana kwaɓe fuska, sai hararar wasa James yake masa.

Har Tga ya kai bakin kofar fita bedroom ɗin ya jiyo voice ɗin Micheal can kasa kasa yana faɗin "uncle I'm not feeling fine" "what?" Tga ya faɗa tare da juyowa da sauri, shi kam Romeo ko a jikin sa dan ya san rashin lafiyan me Michael keyi, ya kwashe kuɗin account nashi ne kap ya saiwa friends nasa motoci da wasu abubuwan shine yanzu ya zo ya kwanta ya dawo shagwaɓaɓɓe wai bai da lafiya.

Da sauri Tga ya juyo ya dawo wajen bed ɗin tare da sanya hannun sa saman lallausan kumatun Michael ɗin yana faɗin "What is wrong with you?" "My head" yayi maganar a shagwaɓe kamar zai yi kuka

ɗaura hannun sa Tga yayi saman goshin Michael ɗin yana waro ash eyes nasa waje, James ji yake kamar ya kwashe su da mari dukkan su daga Michael ɗin har uncle T ɗin, dan haushi ma suka bashi, wai duk iskancin da Michael yazo da shi sai su biye masa suna wani lallaɓa sa yanzu uncle ya sani sarai ba wani ciwo dake damun Michael fa ce iskanci irin nasa kawai, amma sai uncle ya biye masa.

Dawo da kallon sa Tga yayi kan Romeo a nitse yace "please my lion ka duba min Tiger kaji?" Cikin sauri Michael yace "No uncle I'm okey now" James bai san lokacin da murmushi ta kubce masa ba, shi kan shi Tga abun yaso sashi murmushi amma sai ya danne, shi dai Romeo ko kallon in da suke ma bai yi ba kamar bai san da mutane a bedroom É—in ba,

Waya Tga ya ciro daga aljihun sa, ya É—an latsa kamar na 2mins sannan ya mai da aljihun na sa ya juya ya nufi hanyar fita,
a sukwane Michael ya miƙe zaune yana kallon wayar sa da ya fito da ita daga aljihun sa saboda yar kara da tayi, da sauri ya diro kasa daga saman gadon ya tafi da yar gudun sa ya haye bayan Tga yana faɗin "Thank you uncle" tangal tangal Tga yayi kamar zai faɗi kasa dan bai yi expecting Michael zai haye masa baya ba

A hankali ya sauke Michael É—in daga bayan sa yana faÉ—in "My Tiger now your okey kenan?" Turo baki Michael yayi ya wuce ya fice daga bedroom É—in daman kuÉ—i yazo nema wajen Romeo tun da ya samu wajen uncle Tga shikenan ai bukatar sa ta biya

wucewa shima Tga yayi ya nufi waje yana faɗin "I'm waiting for you at the garden My lion" jinjina kai kawai Romeo yayi ba tare da yayi magana ba, dai dai lokacin ya kammala cin abincin na sa ya miƙe ya zauna a bakin gadon sa, yayin da shi kuma Tga ya fice daga bedroom, James kuma ya tattare kayan abincin yayi waje da su.

**💞NIGERIA💞**

_👹DAULAR MUTUWA👹_

Cikin wannan ɗakin Rimsha ta kwana, kwanan zaune sukayi, tun tana kuka hawaye na fita har ya dai na fita, yanzu kukan ma ta kasa yi ga bala'i yinwa da kishin ruwa da take ji, sukam sauran yaran sun sume saura yarinya ɗaya, tare sukayi kwanan zaune da Rimsha, gashi Rimsha ta kasa iya ambato sunan Allah sun rufe mata baki, ji take an shaƙe mata maƙogwaran ta, haka ta hakura ta takure waje guda tana jin wayan nan dodannin suna ta gurnani suna ihu a dab kunen ta amma ba yadda ta iya haka ta zauna a kasa cikin dotti, da daskararren jini busasshe, bata da zaɓi dole ta zauna a wajen.

Allah sarki Rimsha renon madara da chocolate dasu ice cream, kwanciyar gadon lausi da Ac a rufu da bargo nai laushi, yau ta kare da kwanan zaune cikin daskararren jini ga wari sannan ga wayan nan dodannin masu razanar wa da É—an Adam kwakwalwan sa.

Washegari sai da rana ya ɗaga sannan magicians ɗin suka zo suka buɗe su, ba ƙaramar razana sukayi ba ganin still Rimsha na cikin hayyacin ta, ita da ɗayar yarinyar, sun sha mamaki sosai, haka suka fito da su suka kai su wani keɓaɓen waje mai kama da gida, yana da girma sosai, a nan suka turasu cikin wani ɗaki suka juya suka koma, suka ɗauki wayan can sauran yaran da suka suman kuma suka tafi da su in da suke yanka mutane.

A hankali Rimsha ta fara rarrafawa a cikin ɗakin ɗan ba zata iya miƙewa ba, saboda yinwan da take ji, kamar a mafarki ta ga kamar halittar mutun zaune an kifa kai da gwiwa, ta kasa gane mace ce ko namiji Saboda idon ta baya gani sosai saboda yinwa da take ji, Dan ma ɗakin nada haske sosai ba kamar ɗakin da a ka fito da su daga cikin shi ba, hakan yasa Rimsha ta iya karewa wan nan halitta kallo, da kyar ta iya rarrafawa a kan gwiwowin ta, ta ƙarisa wajen wan nan halitta wadda ta kasa gane wace halitta ce, babu ko tsoro a rattare da ita ta sanya hannu ta taɓa wannan halitta,

a razane wannan halittar ta ɗago kan ta wadda ta kasan ce....✍️✍️

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

B 💞Star Lady💞

TRIPLET'S

https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo

*THE BEGINNING*

💞*STAR LADY*💞

Mai neman karin bayani yamin magana ta wan nan number 09162620621

Masu tambaya ta ma'anar sunayen danake using dasu a book É—in gasu nan

Names and their meaning

1Ayla Moonlight. 2Aafia Confident .
3Umaisha soft hearted 4 Ayla Moonlight
5 Rimsha means Beautiful or face like moon
6 Jehan meana the world

EPISODE 22

a razane wannan halittar ta ɗago kan ta wadda ta kasan ce mutun ce mace ce yarinyar yar karama, wadda wahala ta mai da ta kamar kashi da rai, duk ta rame ta bushe gaba ɗaya face nata ya rama ga idon ta sun yi manya manyan kamar zasu faɗo waje saboda raman da tayi, a tsorace Rimsha ta ja da baya tana kallon yarinyar nan wadda a shekaru ba zata wuci 14 years ba, baya baya Rimsha ta ja ta koma ta zauna ɗan nesa da yarinyar, a hankali ita ma wan can yarinyar ta rarrafo ta kariso wajen Rimsha ɗin suka haɗu suka zauna shiru, dukkan su sai ƙugi cikin su ke musu saboda yin wa.

Kamar da ga sama sukaji wan nan yarinyar tana faÉ—in "Sannun ku da zuwa Daukar mutuwa, daular da ba wani mai rai da yake shiga ya fita, na jinjina muku da ku ka iya tsallake level 1 da 2 ku ka iso nan na taya ku murna sosai, amma sai dai daga nan babu in da zaku sake zuwa kai tsaye lahira zaku wuce" duk da ba wani Hausa kirki Rimsha ke ji ba ta fahimci abun da yarinyar take faÉ—i, sosai murmushi ya bayyana a face É—in Rimsha jin yarinyar tayi magana da da farko ta É—auka kawai ba mutun bane idon tane ke nuna mata kamar mutun ne a wajen.

Cikin zumuɗi ta rarrafo ta matso kusa da yarinyar ta sanya hannu ta dafa kafaɗar yarinyar tana faɗin "zamu fita In...ta kasa fitar da In Sha Allah ɗin maganar ta tsaya kamar wadda a ka shaƙe, hannu tasa a wuyar ta tariƙe da karfi tana jin yadda wuyar nata ke mata raɗaɗi kamar ana zare jijiyoyin wajen, nan take ta fara hawaye sirara masu ɗumin gaske, ganin haka yasa yarinyar ta riƙo ta tana faɗin "Ki dai na wahalar da kan ki, babu wanda ya taɓa shiga ɗaular mutuwa kuma ya fita, rayuka sun fi a kirga suka zo nan kuma suka tafi lahira kamar ba'ayi su ba, abun da nake so dake kawai yanzu ki shirya daga yanzu kowani lokaci za'a iya samun mai son wani abu daga jikin ki" ita dai Rimsha gaba ɗaya ta kasa magana sai hawaye take masu zafi saboda raɗaɗin da wuyar ta ke mata.

Rarrafowa É—ayar yarinyar ma tayi ta kariso wajen su, suka zubawa Rimsha ido, yayin da ita kuma Rimsha take kokarin ceto muryan ta dan ta samu ta musu magana.
Chapter 69 · 0% Book details