← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 126

Sashe 8

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

```Jahan```
Tana tafiya tana yamutse fuska tana kallon dattin unguwar kasan cewar Anguwar talakawa ne sosai akoi datti ta ko ina kallon banza ta fara yiwa mutane dake wucewa a harabar unguwar duk in da ta wuce sai ta tufar da yawu ko ta toshe hanci.
Tun daga É—an nesa ta hango su Sadiq da wasu samari saannin sa suna buga kwallo dogon tsaki taja kafin tace "Dirty people" ta kai karshen maganar tare ta tufar da yawu a ranta tana faÉ—in "Allah ya kiyaye naci abincin da su Goggo zasu girka da ruwan gidan su kazaman yaran nan" Ta shagala cikin tunani da zancen zuci bata ma san ta iso wajen su sadiq ba sai ji tayi kwallo ya bugeta a kafaÉ—a da karfi har sai da tayi tangal tangal kamar zata faÉ—i kasa, a zafafe ta juyo tana kallon matashin da ya bugo kwallon, matashi ne mai jini a jiki yana da É—an kiba da tsawo wadda akalla zai kai 24 to 25 years.
Kallon banza mata shin mata kafin yace "Ke ki wuce ki bamu waje kinzo kin tsayawa mutane a waje" Bata ma fahinci me ya faɗa ba ta dai fahimci faɗa yake mata, A kule ta fara magana cikin harshen turanci "Kai banza kazami idan ban da kai wawa ne ma taya za'ayi kuzo kuna buga ball a kan hanyar wuce wa jibeka wani katon banza da kai cikin yara duk kafi su girma kazo kana shiga cikin yara ko kunya baka ji" ta kai karshen maganar tare da jan dogon tsaki fusata iya fusata matashin nan ya fisata kasan cewar yana jin turanci sosai a fusace ya nufota gadan gadan tana tsaye ko motsi ba tayi ba sai ma kallon rai ni da take masa,.Yana iso wa wajen ta bai yi wata wata ba ya ɗaga hannu zai wanka mata mari cikin sauri Sadiq ya rike hannun sa yana faɗin "Haba Fadil me yayi zafi zaka yi yunkurin marinta" Fadil na ƙoƙarin yin magana muryan Jahan ya katse su cikin harshen turanci tace "Lallai kuwa wani kaza mi da kai ne kake yunkurin taɓani aiko da kayi kuskuren marina da baka sake mafarkin marin wata ba da kayi nadamar zuwan ka duniya" A fusace Fadil ya kwace hannun sa daga rikon da Sadiq ya masa yana kokarin kai mata mari Sadiq ya sake rike sa yana faɗin "Ki tafi in da zaki je kiyi hakuri" kallon banza tayiwa Sadiq kafin tace "I can't go anywhere please ka sake shi ya mare ni idan ba shi da hankali wani wawa kazami da shi sai wari yake" tayi maganar da kwabaɓiyar hausar ta, ta kai karshen maganar tare da tufar da yawu tana yamutse fuska, a fusace Fadil ya ture Sadiq har sai da yayi baya baya ya faɗi kasa cikin zafin nama ya ɗaga hannu zai mare ta

Share fisabilillah 👏

To Masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai

💋Star Lady💋

💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞

Mai bukatan karanta book É—in*TRIPLETS* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number 09162620621 ban da kira please

STAR 🌟 LADY..✍️

*💋The beginning💋*

Episode 3

....cak ta riƙe hannun sa tana tsaye ko alamar tsoro babu a idon ta bare shakkan sa cikin fushi ya sanya kafar sa yana kokarin kwashe kafar ta ta faɗi kasa batayi wata wata ba ta wanke masa fuska da mari cike da izza tace "Da Jehan kake magana first born a wajen...sai kuma tayi shiru tare da wurgi da hannun sa da ta riƙe tana jan tsaki ta wuce ta nufi hanyar shiga gidan su Sadiq mamaki ya hana Fadil motsawa daga in da yake ya dafe kumatun sa yana kallon ta har ta shige gidan su Sadiq shi kan shi Sadiq dake baje a kasa mamaki ya hana shi miƙewa sai zancen zuci yake "ƴar ƙaramar yarinya kamar wan nan har ta iya sa hannu ta mari namiji babba kamar Fadil babu shakka ko tsoro a idon ta wace ce wan nan yarinyar gaskiya ina son sanin wace ce ita dan wannan irin ƙarfin gwiwar da ƙarfin halin nata ba haka kawai ba daman kuma yan unguwar nan suna ta magana a kan su akan basu yi kama da talakawa ba to suwaye su wace ce ita?" haka Sadiq yayi ta jerowa kan sa tambayoyin da bashi da amsar su shi kan shi Fadil tambayar da yake wa kan sa kenan wace ce Jehan da har zata iya marin sa babu ko shakka bare ɗarɗar, gaba ɗaya matasan dake wajen suna buga kwallo sun sha mamakin Jehan ba kaɗan ba kasan cewar sun san halin Fadil bai da wasa yana da zafin rai ga cinzali da mugunta dayawan ƴan unguwa suna tsoran sa yau mace ta mare sa a gaban jama'ar unguwa tab yarinya kin shiga uku sai dai muce Allah ya jikan ki.
Chapter 8 · 0% Book details