Sashe 122
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbi da kan sa ya kira Akila a waya ya haɗa ta da daddyn Jelly, sai murna Akila baiwar Allah mai kaunar yan uwan ta, sosai ta rinƙa dariya har da hawaye jin daɗi, ko da ta tambayi daddy ina Jelly sai yace mata tana barci, Akila bata ji daɗi ba taso yin magana da jelly amma haka ta hakura tace wa dad zata kira gobe da safe dan su gaisa da jelly, to kawai dad yace mata zuciyar sa na kuka, a pannin su Imran ma Abbi ya haɗa su da dad, da suka tambayi Jelly dad yace tana barci, Imran kamar zai yi kuka yace wa dad shikenan sai da safe zai kira, shima ya kusa dawowa saura masa kwana biyar, sosai daddy ya masa Addu'a da fatan alkhari, daga haka sukayi sallama, kowa ya kwanta, asuba ta gari.
Washegari kuwa tun karfe 7 su Umaisha suka shirya dan su bar gidan da wuri kar dad ya tashi barci ya hana su fita da kalar kayan da suke son sawa, Umaisha bata cika saka riga da wando taje school ba, sai dai tasa atamfa ko lace amma yau da gangan ta saka riga da wando wadda suka kama ta sosai duk dan tasa Akil yaji ya tsane ta yaji haushi tun da yace mata yana shigowa Kaduna gidan su zai fara zuwa gashi kuma da bala'i kishi, ita kuma Aafia yau doguwar riga na kanti tasa, kasan cewar rigar jikin ta kamar roba yake hakan yasa ya kamata sosai, duk wani sura na jikin ta ya bayyana, haka suka fito sauri sauri kamar marasa gaskiya suka fice, sukaje kowacce ta shiga motar ta suka bar gidan suka nufi school.
A ɓangaren Aunty kuwa lokacin da Abbi ya samu labarin juna biyun ta ba karamin murna bawan Allah nan yayi ba, sai dai abun da basu sani ba, su suna nan suna murna Aafia da Rufee suna can suna shirya yadda za'a zubar da ciki , wannan shine cakwakiya muje dai zuwa dan ganin yadda wannan rikici zai kare.
Daddy kuwa kwata kwata bai ji daÉ—in zaman gidan Abbi ba, dan yadda Aafia ke masa baya jin daÉ—i, ji yake kamar ya koma Kano ko kuma ya tafi gidan su Imran wato gidan babban ya'yan su dan ko ba komai Imran da Akila suna kaunar sa, amma kuma idan ya tuna yadda yayan sa wato Abbi yayi tattaki daga nan Kd har Kano yaje ya É—auko shi, sai yaji kamar idan yace zai bar gidan bai yiwa Abbi adalci ba, hakan yasa ya hakura ya danne zuciyar sa ya ci-gaba da zaman hakuri, dan zama da su Aafia sai ka dangana da hakuri in ba haka ba zuciyar ka zata fashe.
Mu leƙo Jehan mu dawo
💞KATSINA💞
Ba karamin daɗi Jehan taji ba ganin yadda jikin mum ya fara kyau har wani cool murmushi take sake wa, shima Sadiq yaji daɗi sosai sai addu'a yake ta zubawa mum gwaggo na amsawa da Amin, yau sai karfe 9 na dare sannan su Jehan suka baro asibiti saɓa nin kullun da suke dawowa da yamma, yau saboda murnan anyiwa mum aiki jikin ta ya fara kyau yasa basu kamo hanyan dawowa da wuri ba.
Bayan sun baro asibiti, suna tafiya suna yar hira suka nufi bakin hanya dan taran abun hawa, basu kai ga isa bakin hanya ba, wasu mata sa irin ɓata garin nan suka tare su hannun su rike da sanduna irin goran nan, sai warin sigari wato taba suke da alama wasu daga cikin suma a buge suke
Tsawa suka dakawa su Jehan a kan su kawo wayoyin su da kuÉ—in dake jikin su, ba karamin tsorata Jehan da Sadiq sukayi ba, har wani fitsari Jehan take ji yana kokarin zubo mata,
Amma saboda karfin hali irin na Jehan sai ta ɗaure fuska tace "Kai nima fa yar daban nan ne ta bugawa a jarida kuma idan baku sani ba ku sani yaya na ƙasurgumin ɗan daba ne na gaske, shine kamar ni kan war sa zaku tare kuce na baku waya ta to wlh sai na faɗawa yayana kuma duk in da kuke sai ya nemeku ya muku yan kan rago" kasan cewar dukan su basa cikin hayyacin sosai, zokaga yadda ake shiga tashin hankali, har kasa wayan nan yan iskan gayun suka duka suka fara bawa Jehan hakuri dan tsoron kar ta faɗawa ya'yan ta dan yanzu ma bala'i dake cikin garin Katsina kawai ma ya ishe su inaga kuma ta sake faɗawa yayan nata abun ai ba zai yi kyan gani ba, su daman irin yan iskan nannen masu neman kuɗin sayan sigari da wiwi kawai ba dan wani abu suke tare mutane su musu kwace ba.
Jehan manya Jehan DPO an samu dama har da ja musu kunne da yi musu last warning a kan idan ta sake jin sun sake yin wani abu makamancin haka tofa kamar a kunnen yayan tane ne, sosai suka mata alkawari a kan bazasu sake ba, shidai Sadiq bawan Allah yanzu Jehan ta dai na bashi mamaki ma ya fawwalawa Allah lamuran sa yana bin Jehan a duk yadda ta bi da shi, sai dai É—an zaman sa da ita yasa shima ya fara cire tsoro a ransa, yanzu yana jin jarunta har cikin jinin jikin sa.
Niko nace tab aiko baka san itama duk burga bace a fili amma daga ta ciki har fitsari take, gara maka ma ka ci-gaba da jin tsoron ka dan ba ilimi gare kaba karka je ka taɓo abun da ya fi karfin ka kasha dukan mutuwa a banza, ita Jehan akoi ilimi sai ta karanci yana yin mutun take yanke masa irin hukuncin da zata masa, kai kuma ba ilimi kawai zaka afkawa abu hmm akoi matsala!!!.
Sallamar guys É—in Jehan tayi sannan tace "Muje Sadiq" sai godiya guys É—in ke mata tare da fatan alkhari na dole, wannan shine idan ba kayi sharan masallaci ba kayi na kasuwa.
Suna tafiya a hanyane kafin su kai bakin titi Sadiq yace "Jehan me yasa zaki yi karya? Meyasa zaki danganta kan ki da yan daba?" ba tare da ta kalle saba tace "Akoi wuraren da yin karya ya halatta wadda idan kayi su baka da laifi har gaban Allah, ciki kuma har da wanda nayi yanzu, kayi karya domin ka kare rayuwar ka, zaka iya karya dan ku zauna lafiya a gidan ka, zaka iya karya dan ka sulhun ta mutane biyu da suke faɗa ko gaba, to a nan in da suka far mana nan kaga ai bumu da mafita dole mu musu abun da hankalin su zai kama, a yadda suke yan iskan garin nan, ba Allah da annabi zaka faɗa musu ba, domin bazasu saurare ka ba, dan ba hanyar Allah suke ba, amma idan ka faɗa musu kana da wanda ya fisu zama ɗan kwalta zasu nitsu ga misali dai ka gani, ko wani ɗan adam akoi direction ɗin da yake tafiya a kan sa, to kai ma dan ku zauna lafiya kasa ya yarda da abun da kazo masa da shi sai ka ɗauki direction ɗin da yake kai kaima ɗin, ba wai zakayi hakan dan kazama irin sa ba ko dan ka saɓawa Allah no a'a zakayi hakan ne dan kasa ya fahimci abun da kake nufi koda bai yi niya ba, yanzu yadda suka tare mun nan kana tunani idan shekara zamuyi muna ce musu dan Allah zasu hakura su kyale mune?" Girgiza mata kai yayi alamar a'a, kasan cewar yanzu Jehan Hausa ya ɗan fara zama zam zam a bakin ta tana ɗan yi magana da Hausa sosai tana ɗan kwaɓawa da English nata
Ci-gaba da magana tayi "Yauwa ashe ka gane ko kwana zamuyi muna haɗa su da Allah baza su kyale muba, dan ba aikin Allah suka fito yi ba, saboda babu in da Allah yace ɓarawo yaje yayi sata, hasalima sai dai in da yake sanar da mu hukuncin da za'a wa ɓarawo mai cin hakkin bayin Allah, ajiye wannan zancen muje in da nake so ka fahimtar ko dan ɓacin rana wata rana, aduk lokacin da wasu yan iska suka tare ka, ka nitsu sosai ka duba yanayin su a kan wani tsari suke, misali kaga wayan nan yadda suka tare mu ai sun nuna mana su yan daba ne, shiyasa na musu amfani da sunan ɗan ta'adda wato baban yan daba, amma idan ka duba kaga cikakkun yan iska ne masu son iskanci kamar ni mace ai nuna musu zan yi iskancin nima nake so kamar yadda mukayi da Farooq sai ka rabu da su lafiya ba tare da sun maka illaba, koda sun karɓa maka wani abun ba zasu maka illaba" shi dai Sadiq bin ta kawai yake da to domin wani Hausar a kwaɓe take wani kuma tana saka turanci
Shiru ya ɗan yi kafin yace "Jehan aina kika san yan daba ne ma? Ke da lokacin da kuke tare da daddy kullun kuna gida baku san wahala ba baku fita waje" guntun tsaki taja kafin tace "Na san shi mana a media before ai ina da waya kuma ina hawa net" shi dai Sadiq tun da ba sanin net ɗin yayi ba sai yayi shiru bawan Allah bai taɓa riƙe karamar waya bama bare babba, sun tsaya suna ta hira sai wucewa taxi suke saboda dare, da kyar suka samu wani suka tara zuwa gida.
Koda sukaje gida basu ci abinci ba dan sunci a asibiti da gwaggo wadda Jehan ta sayo musu, karatu kawai Jehan ta koyawa Sadiq da Hanan har da Yusuf kamar yadda suka saba, Sadiq yana son karatun sosai shiyasa ya mai da hankalin sa sosai yana É—aukan abun da take koya masa musamman fannin addini yana kokari sosai yana mayar da hankali.
Sai karfe 11 na dare sannan su Sadiq suka yiwa maman su da Jehan sallama suka fito, har bakin kofar É—akin maman Hanan suka raka Hanan sannan suka wuce É—akin su shida Yusuf Sha'aban kuma baya nan yaje garin maman sa duba ta