← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 126

Sashe 115

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren Abbi da daddyn Jelly kuwa, ko da Abbi yaje yaji abun dake faruwa, sosai hankalin sa yayi mugun tashi, ya shiga damuwa fiye da tunanin mai tunanin, bai yi kasa a gwiwa ba, ya ɗauko daddy dan su dawo Kaduna tare har sai angane in da Jelly take, idan ba haka ba barin daddy shi kaɗai babban haɗari, sannan Abbi ya sake hurawa jami'an tsaron Kano wuta akan su kara kokari wajen neman Jelly, shiyasa ma basu baro Kano da wuri ba sai karfe 4 na yamma, dan sunyi ta zarya tsakanin police station da gida, duk da daddy bai da lafiya amma sai da ya dage yayi ta bin Abbi, tare sukayi ta zarya, daga karshe suka kama hanyar Kd, Abbi yana jin kamar zai yi kuka, yaso faɗa wa su Imran amma daddy ya hana shi, yace ya bar su su rubuta Exam nasu cikin kwanciyar hankali da nitsuwa, to Abbi yace sannan ya hakura da zancen faɗa wa su Imran ɗin har sai sun dawo.

A ɓangaren Jelly kuwa, yau dai anyi Sa'a da kan ta tayi jika jikan ta wato wanka bata fita ba sam, duk jikin ta sabulu da kumpa, Hajiya Turai tana palon bata ma san Jelly ta shiga wanka ba, yau ra'ayin kanta kawai tayi, da kan ta tayi wankan.

Tana fitowa daga toilet É—aure da towel ta nufi gaban mirror kamar yadda taga hajiya na mata, ita da kan ta sai sosa jikin ta wajen bayan wuyar ta take, saboda ta lapka sabulu a wajen kuma bata wanke ba, sai sosa wajen tare.

Tana zuwa gaban mirror ta hau labta mai a kan sabulu da kumfa, gashi mai É—in ma har da na gashi ta tabka dayawa dayawa, a takaice dai duk wani mai dake Wajen mirror sai da ta labka a fiskar ta zuwa jikin ta, sai kwailin take, har wani kyalli fatar ta keyi, fuskar ta taji mai har yana É—iga

Akan mai É—in ta É—auko Foundation da beauty blending ta fara labkawa shima, bayan ta gama ta É—auki kwalli ta saka a kasan idon ta, kamar wata dodo haka ta zama, bata sa lipstick ba dan yau taji bata ra'ayi, fiskar nan nata yayi wani faw kamar jan kosai ko in ce kamar an É—aye fatar biri, ga wajen idon ta yayi bakin kirin da kwalli, baka ganin komai a fiskar ta sai idon ta farare tas, idan ka haÉ—u da ita da daddare sai ka suma saboda tsoro, ta labka mai a saman labkakken sabulu da kumfa ga Foundation abun ba'a cewa komai.

Bayan ta gama lafke lafken kwalliyar ta sai ta wuce wajen drawer kayan sawar Hajiya, dan duk wannan tsiya a bedroom É—in Hajiya akayi shi, sai faman haÉ—a zufa take saboda uban mai da ta labka wa jikin ta.

Tun bata karisa wajen drawer ba ta cire towel É—in jikin ta tayi wurgi da shi saman bed, taje ta buÉ—e drawer kayan Hajiya, abuna farko da ta fara cin karo da su shine breziya da pant, É—auko pant É—in Hajiya tayi, ta É—ago shi sama tana kallo, kara zaro ido tayi, a sukwane ta kalli waist nata wato kugun ta, taga pant É—in Hajiya wargajeje gari guda, irin ta biyar sai su shige cikin pant É—in, sai jujjuya pant É—in take wai ko zata samu wajen rage masa girma

Da dai taga ba wajen rage masa girma, sai ta dura shi haka nan, dukka kafofin ta a site É—aya ta haÉ—e su, wato a kafan pant É—aya, sauran jikin pant É—in da ya mata yawa kuma sai ta tattara ta É—aure kamar mai É—aure alale, ta cusa cikin ta saman kugun ta, sannan ta É—auko breast, tayi shiru tana tunanin ya ake sawa, dan tabbas tana ganin shi a jikin Hajiya, sai dai koko É—aya na breziyar Hajiya dai'dai yake da ya É—auke breast nata dukka biyu, tashin sense, haka ta saka abun ta, koko É—aya a breast nata É—ayan kuma a cikin ta, abun gwanin ban dariya, ga fuskar kamar an É—aye fatar biri sai turo baki take.

Sake sanya hannun ta tayi cikin drawer ta ɗauko wani shaddan Hajiya fari tas, yaji aiki sosai ɗinkin half gown da zani, rigar kawai ta sanya wadda yazo mata har idon sahu na kafar ta, dan Hajiya Turai irin hamshaƙan matan nan ne, ga tsawo ga kiɓa, ta ko ina masha Allah, a gefen faɗi kuwa, Jelly kamar tsinke ta zama cikin rigar Hajiya, abun gwanin ban dariya, kayi dariya har cikin ka yayi ciwo.

Bayan ta gama duk wannan shirye shiryen nata, ta fito ta nufi palo da zumuÉ—in ta zata je ta nunawa Hajiya yau tayi abun arziki da kan ta.

Hajiya na zaune a palo tana shan black tea É—in ta, Kamar daga sama Jelly ta faÉ—o mata babu ko sallama, duk kiba irin na Hajiya ganin Jelly bai hana ta tashi a É—ari kamar siririyar mace ba, idan ana zancen cetan rai wake ta wani zancen kiba, to wannan ma hakane domin a tunanin Hajiya aljana ce, sai faÉ—in innahu min sulaimanu wa innahu Bismillahirrahamanin rahim, a guje Hajiya fa ta zura tayi babban palon kasa tana ihu yau ga aljana a palon ta,

Ganin Hajiya ta zura a guje tayi waje ne yasa Jelly tayi tunanin kila wani abun tsoro Hajiya ta gani, ita ma ai sai ta kwasa a kuje tabi bayan Hajiya tana ihu dan kar abun tsoron da Hajiya ta gani ya kama ta, bata san itace abun tsoron ba

Hajiya kuma ganin Jelly na bin ta da gudu sai tayi tunanin Aljanar ke binta, dan haka sai ta kara karfin ihun ta dan jama'ar gidan su kawo mata ɗauki, ga firskar Jelly yasha daɓa daɓa da kayan make up sannan gashi ta sanya farar shadda, kuma burgujeje ya mata yawa, tana yawo a cikin kayan, ya kuke ganin abun zai kasance?.

Da gudun gaske Hajiya Turai ta faɗa ɓangaren su Afnan, tana gudu tana ihu, a palon part ɗin su ta isko Afnan da Maman ta suna zaune, ganin Hajiya Turai a guje yasa suka miƙe suna faɗin "Ke Hajiya Turai me hakan, zaki shigo mana ba sallama, bamu san... Basu kai ga karisa maganar ba Jelly ta faɗo cikin palon da gudu, Subhanallah zokaga yadda ake gudun cetar rai, Afnan uwar rashin kunya, tuni ta watsa a guje tayi cikin ɗakin ta ta banko kofa,

karo na farko a rayuwar Afnan da ta fara kiran sunan Allah data ga bone, ita kuwa maman Afnan É—in, tsabar tsorata rungume Hajiya Turai tayi tana faÉ—in "Na shiga uku na lalace ki taimake ni Hajiya Turai, karki bari Aljanar nan ta kama ni" ita kan ta Hajiya Turai neman tsira take maman Afnan zata wani ce ta taimake ta, ture maman Afnan tayi ta bi bayan Afnan da dugu ta shige É—aki, aiko itama maman Afnan bata yi kasa a gwiwa ba ta rufa musu baya, ita ma Jelly bin su da gudu tayi dan a tunanin ta wani abun tsoron suke gudun wa.

Jelly na shiga É—akin Afnan, suka fasa ihu a guje suka sake bazama waje, still itama Jelly tabi bayan su tana kuka.

A takaice dai yau Jelly tasa gaba É—aya familyn Abbo sun haÉ—u waje guda, wayan da basa shiri basa ko ga maciji yau sun haÉ—e waje guda saboda Jelly, dan ba wani part a cikin gidan dasu Hajiya turai basu faÉ—a da gudu suna ihu ba, duk kuma in da suka shiga sai yan part É—in sun rufa musu baya suyi ta gudun cetan rai tare.

Daga karshe dai tsakar gida suka koma suna yar tsere da Jelly, suna gudun ta, ita kuma tana gudun abun da suke gudu, domin a ɗaukan ta wani abun suke gudu, Allah sarki Hajiya Turai gata da ƙiba sosai haka Jelly tasa baiwar Allah nan ta rinƙa tikan gudu kamar mahauniya sai haki take tana mumfashi sama sama.

A wannan yanayin na yar tsere da suke da Jelly Nawid ya shigo cikin gidan same su, dan yana ta horn ba wanda ya buÉ—e masa gate, dan mai gadin ma dayake mara hankali ne irin kauyawan nane wai sai ya É—auko sanda yana bin Jelly zai make ta, idan kuma ta juyo ta kalle sa, sai ya fasa ihu ya shige bayan flowers.

Nawid dai yaga tashin hankali dan kuwa ya rasa me ma zai yi, tsayuwa kawai yayi yana kallon yadda iyayen nasa da kannen sa har ma da yayyun sa mata ke gudu suna ihu, tun shigowar sa kallo É—aya yayiwa Jelly ya gane ita É—in ce, abun da bai ganeba shine gudun me iyayen nasa keyi, dan shi bai ga abun da suke wa gudun ba, saboda yaga Jelly É—in na binsu ita ma tana gudun, gashi dukkan su sai ihu suke har da ita Jelly, shine abun ya kulle masa kai ya rasa me suke wa wannan gudu da ihun

Afnan uwar rashin kunya yau tayi gudu ne har ta godewa Allah, gashi kuma sai addu'a suke aljananan wato Jelly taki ɓace wa, sai gudu suke daga masu kiran, ya Allah ka kawo mana ɗauki sai masu faɗin, Ya Rahman bayin ka suna cikin halin a ula'e, addu'a kala kala yau sun zuba shi, wasu ma basu san me suke faɗe ba kwata kwata saboda tashin hankali, duk abun da yazo bakin su suke faɗe.

Shiru Nawid ya tsaya, sai da ya ga Hajiyar sa na kokarin zubewa kasa saboda gajiya sannan ya karisa wajen da sauri, cikin tsawa yace "Wai me hakan ne? Meke faruwa ne?" Ya kai karshen maganar tare da riƙo Hajiya Turai, sai faman nuna masa Jelly Hajiya Turai take da hannun ta ta kasa magana, kallo Jelly yayi kafin ya dawo da kallon sa kan Hajiya "Ummi me babyn kuma tayi yau kike gudun ta? Ko dan tayi wannan kwalliyar ne" sai lokacin Hajiya Turai ta waro idon ta da kyau ta kalli Jelly da kyau, daman su sauran yan gidan basu san Jelly ba bare su gane ta, dan bata taɓa zuwa part ɗin kowa ba, kullu tana tare da Hajiya
Chapter 115 · 0% Book details