← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 126

Sashe 73

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI TAALA WA BARKATUHU JAMA'A INA MUKU FATAN ALKHARI DA FATAN CIN MA BURI NA ALKHARI, MASU MIN MAGANA A KAN CEWA BAI KAMATA ROMEO YA RINƘA YIWA IYAYEN SA TSAWA HAKAN NAN BA, BAI KAMATA YA RINƘA YIWA MUM ƊIN SA HAKAN NAN BA, INA SON KU SANI FAƊAKARWA NAKE BA KARA ƁATA TARBIYA BA, IDAN KUKA YI HAKURI A HANKALI ZAKU JI MENENE YASA YAKE MUSU HAKAN, KOMAI NADA DALILIN SA A RAYUWAR NAN, SO PLEASE KU KYALENI HAKA NAN, BUGU DA KARI KUMA KARKU MANTA FA SHI ROMEO BATURE NE, KUN SAN TURAWA YADDA SUKE WANI LOKACIN MA ƳAƳA SUKE KOMAWA MASU MULKI A GIDA, IYAYE SU KOMA KARKASHIN SU, SAN NAN KUMA KARKU MANTA SHIFA ROMEO KIRISTAR NE BA MUSULMI BANE, MU MUSULMAI MUNE MUKA SAN DARAJA IYAYE DA GIRMAMA SU, AMMA YAWANCIN KIRISTOCI BASU SAN WANNAN BA FATAN KUN FAHIMTER, KU CI-GABA DA BIBIYA A HANKALI KOMAI ZAI WARWARE MUKU, NAGODE*

💞TRIPLET'S💞

https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo

*THE BEGINNING*

💞STAR LADY💞

WhatsApp me for more information 09162620621

Episode 23

A tare su dad suka koma suka zauna, dad ya tsorata sosai, duk da cewa baya son mum, amma bai son a kashe ta, ya fi son dai tayi nisa dasu ne ta bar su su samu peace of mind, shi kuma James a fusace ya haura sama yabi bayan Romeo da Michael.

Zaune bakin lallausan katafaren gadon Romeo ya isko Michael, sai faman turɓune fuska yake, while shi kuma Romeo yana tsaye gaban mirror, karasawa cikin bedroom ɗin James yayi, tare da zama kusa da Michael ɗin yana faɗin "Sorry My tiger, how are you feeling now?" Yayi maganar cike da kauna da kuma tausayin ɗan uwan nasa, kasan cewar shi Micheal a baya an taɓa masa aiki a ƙwaƙwalwar sa saboda wata matsala da ta taɓa faruwa da shi a baya, shi yasa sometimes idan ya birkice ba mai iya shi sai Romeo, kuma wannan dalili yasa gaba ɗaya gidan sukafi son shi saboda tausaya masa da suke, ko shi James ya bugi Michael ɗin ne cikin fitar hayyaci, baya hayyacin sa lokacin, badan haka ba da ba zai bugesa ɗin ba,

karisa hayewa saman gadon Michael yayi ya gyara kwanciyar sa yana faɗin "Please James i need hot coffee" yayi maganar a shagwaɓe, dukan wasa James ya kai masa a kirji yana faɗin "You make me thinking" lumshe ido Michael yayi ya buɗe tare da kara shagwaɓe murya yace "Thinking for what?" Hararar wasa James ya masa kafin ya miƙe yace "I'm coming let me bring the coffee for you first" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga room ɗin, duk abun da suke Romeo na jin su amma kamar bashi a ɗakin, yana tsaye gaban mirror yana faman latsa waya da alama sako yake turawa mai muhimmanci,

Jim kaɗan James ya dawo hannun sa riƙe da kyakkyawar cup mai ɗauke da hot coffe sai tiriri yake, yana fitar da hayaki, gefen gadon ya zauna yana faɗin "stand up please" kara turɓune fuska irin na shagwaɓa Michael yayi kafin yace "I don't need a coffee again" zaro ido waje James yayi lallai Michael ya raina masa wayyo yaje ya kawo coffee ɗin ne dan iskanci kuma zai ce bai so,
shi kuwa Michael lumshe brown eyes ɗin sa yayi abun sa kamar mai barci, hannu James ya kai kamar zai kai masa duka, sai kuma ya tuna da ya bugesa ɗazun kuma yasan wannan bugun da ya masa ma Romeo ba zai kyale sa ba, sai ya tuhumesa a kan me yasa zai bugi Michael, amma sai in Michael ɗin baya nan, dan Romeo baya yiwa ɗaya daga cikin su faɗa a gaban kowa, duk wanda yayi laifi a cikin *TRIPLET'S* ajiye sa yake shi kaɗai ya masa faɗa, tuna hakan yasa James ya miƙe ya fice da coffee ɗin a hannun sa ya mai da in da ya ɗauko.

Shi kuwa Michael daga lumshe ido yayiwa James barcin wasa sai abun ya zama da gaske barci ya É—auke sa, ko da Jame ya dawo room É—in Michael ya riga da yayi barci, kwanciya yayi shima a gefen Michael É—in yana jiran yaji Romeo yace me yasa zai bugi Michael, shima daga kwanciya ba jimawa barci tayi awon gaba da shi, basu san time da Romeo ya fice daga bedroom É—in ba sun yi barci, Michael yana barcin ma sai sauke ajiyar zuciya yake cikin barci saboda zafin zuciya irin nasa.

NIGERIA

KADUNA

Kai tsaye gidan sa mutumin nan ya wuce da Jelly, irin gidan nan ne na matasa yan ci rani masu cike da É—akuna,
kamar matar sa haka yaje ya sanya key ya buɗe bedroom nasa yana faɗin "Shiga mana" make masa kafaɗa tayi a shagwaɓe tace "No daddy na ya hana ni shiga room ɗin kowa, kawai ka ɗauko min bag ɗin ka bani in tafi gidan su yaya Imran" da dai yaga taki shiga ɗakin ta lalama sai ya zare mata ido yace "Ki shiga ko na yanka ki da wuƙa" dariya Jelly tayi kafin tace "Ni rago ne da zaka yanka ni?" Ƙasa yayi da murya baya son yi mata da karfin sauran matasan da suka rage basu fita ba wato yan zaman banzan nan su jisa shi yasa ma bai shigar da ita ta karfin tsiya ba yake bin ta a hankali ya sami ta shiga, tana shiga shikenan sai ya ɗaure ta ya toshe mata baki yayi raping ɗin ta niyar sa kenan, amma ina Jelly taki shiga ta kafe a kan lallai daddyn ta ya hana ta kuma bazata ki bin maganar daddyn taba

Ganin da gaske taki shiga ne yasa ya kara kasa da murya yace "Muje ciki kici abinci" turo baki tayi kafin tace "A'a ka kawo min abincin waje" "Ke ni sa'an kine? Zaki shiga ne ko dai sai na ɗaga ki na shigar da ke" kallon sama da kasa ta masa kafin tace "Tun da ka dage na shiga room nan nasan ba alkhari bane a ciki dan daddy na duk ya koya min irin wannan haka Aunty Zuwaira mai aikin mu ma ta koya min karna yarda da maza, kuma ni ba jahila bace babu in da zanje, I'm 14 years now duk irin wannan abun na sansu ɗan iska kawai katon banza kazami" ta kare maganar tana murguɗa masa baki, duk shagwaɓa irin na Jelly tana da wayyo da kuma ilimi sosai duk abun da take tana sane gata bata barin ko ta kwana ba'a mata ta kyale, kana mata abu tun da zafin sa zata rama.

Damko yar hijabin school nasu dake jikin ta yayi yana kokarin turata É—akin, ihu ta fasa tare da cire masa hijabin ta kwasa a guje tayi waje ta barsa rike da hijabin a hannu.

gudu take sosai dan a tunamin ta ya biyo bayan ta, bata san lokacin da ta hau saman titi ba saboda tsoro, bata ankaraba wata dankareriyar mota kirar *falcon Supernova* ya kwashe ta, nan take ta baje kasa bata suraba, kan ta ya fashe sai jini ya fara malala kamar kogi, bata numfashi kamar ta mutu, a sukwane ma tukun motar ya taka birki tare da fitowa da sauri, ya buɗe gidan baya na motar, wata babbar mace ce ta fito daga cikin motar, irin hamshaƙan Hajiyoyin nan ne wadda nera ta zauna musu sosai, sanye take da dankareriyar swiss lace pink color mai bala'i kyau da tsada, ɗinki riga da zani kasan cewar ba yarin ya bace ta manyan ta sosai, wuyan ta da hannun ta ta musu kwalliya da gold masu tsada, yayin da idon ta ke manne da farin glass (medicated glass)

Cikin sauri Hajiyar nan ta kariso wajen da Jelly ke kwance cikin jini, kan kace me jama'a sun taru a wajen, kowa sai salati yake, cikin sauri Hajiyar tace "Dan Allah ku taimaka ku samin ita a mota mu wuce asibiti da ita" tayi maganar a ruÉ—e, da sauri jama'ar wajen suka taimaka a ka sanya Jelly a mota, Hajiya ta koma cikin motar, da gudu driver ma ya koma cikin motar, ya kunna motar ya figeta da wata mahaukaciyar gudu suka nufi hospital.

💞Aafia💞

Zaune suke saman gadon su bayan sun dawo daga school, sai faman latsa wayoyin su suke, yayin da ita Aafia a zuciyar ta take shirya yadda zata ɓullo wa yar aikin da Abbi ya kawo da wuri ta koreta a gidan, Aunty ta fara aiki dan ita ya dace da tayi aiki a cewar su, suyita ɓata mata aikin har Abbi ya gaji ya koreta ya sake ta, sai ayyana hakan Aafia take a ranta tana latsar wayar ta

da sallama mai aikin ta shigo bedroom É—in nasu hannun ta rike da plate mai shake da fruits, duk cikin su ba wanda ta amsa mata sallamar,
Baiwar Allah bata damu ba ta wuce ta ɗaura musu plate ɗin saman table ɗin dake bedroom ɗin san nan ta dawo gaban gadon ta duƙa cikin sanyin murya tace "Aunty ina wuni" kamar ba dasu take ba sun yi banza da ita kamar basu san da zaman ta a wajen ba, shiru ta ɗan yi, a tunanin ta basu ji ba ne sai ta sake cewa "Aunty ina wuni" tsawa Umaisha ta daka mata "ke mahaukaciyar ina ce? Ki fice mana daga bedroom dan Allah, bamu buƙatar gaisuwar!!!" baiwar Allah jikin ta har kerma yake ta mike ta fice daga bedroom ɗin cikin sauri.

Dogon tsaki Aafia taja kafin tace "I hate that girl kuma dole ta bar gidan nan, Halima ita zata ci-gaba da aiki dan ita ce yar aiki da ta dace da yi mana aiki " "same here" Umaisha ta faɗa tana kwaɓe fuska tana turo baki, dai dai lokacin kiran Akil ya shigo wayar ta
Chapter 73 · 0% Book details