← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 126

Sashe 108

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Palon babu kowa sai fitinannen kamshi air freshener da sanyin Ac dake tashi a palon, ko ina tsab tsab, ga haske ya karaÉ—e ko ina a cikin palon, dan har wutar jikin staircase a kunnen suke, shiyasa palon yayi haske sosai kuma hakan ba karamin kara kawata palon yayi ba.

Saman Sofa set milk color ya nufa ya zauna a saman three-seater tare da jingina kan sa da jikin kujerar ya lumshe dara daran idon sa kamar mai jin barci.

Zaman sa a wajen bai fi minti ashirin ba sai ga wasu jibga jibgan sojoji guda 6 masu jini a jika, jibga jibgan gaske ne masu ji da karfi da lafiya sun ƙoshi da training dan kowannen su ka gani kasan ya karɓi horo yadda ya dace, fuska nan tasu babu alaman imani bare tausayi a ɗaure take tamau, sai wani taku suke a jire, suka kariso gaban sa, sai da suka sara masa sanna suka tsugunna kasa, kasan cewar already yasan da zuwan su sai yayi shiru bai ɗago ya kalli su wanene bane.

Sai da ya É—auki 10mins a haka yana lumshe da ido sa, su kuma suna tsugunne a gaban sa, sannan ya É—ago kan sa tare da waro dara daran idon sa har sai da sojojin suka É—an tsorata

Gently yace "Tyrone where is the watch?" Cikin sauri Tyrone ya zura hannun sa cikin aljihun kakin jikin sa ya fito da watch ɗin ya miƙa wa Romeo, gently Romeo yasa hannu sa zai karɓa, sai kuma ya fasa ya zuwa ba Tyrone dara daran idon nan nasa, masu raza jaruman maza, kasan san cewar su Tyrone sun saba da shi, dan Tyrone ne baban yaron sa na biyu daga Tga ne na farko kenan, hakan yasa Tyrone ya dukar da kan sa kasa dan yasan me ya hana Romeo karɓan watch ɗin

Murya na rawa cikin girmamawa yace "Sorry sir I thought is your watch, that is the reason why ban sanya handkerchief wajen É—auka watch É—in ba kuma ban damu ba nasa cikin aljihuna ina....

Bai kai karshen maganar ba Romeo ya É—auke sa da wata mahaukacin gigitatchen mari mai sanya mutun dai ma jin motsin komai na É—an lokaci, har wasu taurari Tyrone ya gani a face na sa, sai da idon sa suka yi jawur kamar jini saboda marin, abun ka da farar fata nan take shatin yatsun Romeo suka bayyana kwance a kumatun Tyrone raÉ—au, wajen yayi jawur kamar jini, kan kace me sai hawaye masu bala'i zafi suka fara bin kumatun Tyrone É—in, an san soja da jarunta, amma fa duk jaruntar su idan Romeo ya mare su sai sunyi hawaye.

A fusace Romeo ya miƙe ya damko wuyar kakin jikin Tyrone tare da haɗawa da wuyar sa ya shaƙe shi ya ɗaga shi sama, da karfi yayi wurgi da shi gefe, yau Tyrone ya ɓata masa rai, a kan me zai ce watch ɗin sa ne me yake nufi da hakan kenan , shima criminal ne kenan?

Kan kace me yana yin Romeo ya sauya, idanun sa sun rikiɗe sunyi jawaur kamar wuta, gaba ɗaya jijiyoyin saman idon sa sun tashi, gashin jikin sa har wani miƙewa suke saboda ɓacin rai, jijiyoyin kan sa duk sun miƙe zara zara dasu, lokaci guda ya riƙeɗe ya zama asalin lion da daddy ke kiran sa da shi, har wata irin huci mai bala'i zafi yake fitar wa tamkar zakin da yayi shekara biyu babu abinci yanzu kuma ya samu abinci an hana shi ci, haka Romeo ya zama.

Gadan gadan ya tinkari Tyrone, da hannu ɗaya ya damko wuyar sa tare da miƙer da shi tsaye, wani mahaukacin shaƙa yayiwa wuyar Tyrone ɗin har sai da idon Tyrone suka firfito waje kamar zasu faɗi kasa, wani irin zufar ɓacin rai ne ta fara gangarowa lion daga gefe da gefen kunnen sa, nan take wasu zara zaran jijiyoyi suka bayyana a wuyar sa yau ran maza ya ɓaci, Tyrone ya dangan tashi da manya manyan criminals na duniya, idan ya tuna hakan sai yaji zuciyar sa na tafasa kamar zata fasa kirjin sa ta fito waje

A fusace yayi wurgi da Tyrone saman centre table glass dake tsakiyar sofa set Milk color,

Watsa watsa tables ɗin yayi glass ɗin suka tarwatse pieces a wajen, wani razanannen ihu azaba Tyrone ya saki domin glass ɗin ya soke masa fuska, kan kace me jini ya fara fita daga face nasa, yana son bawa Romeo hakuri amma ya kasa, saboda wahalar da ya sha, sanna kuma ya san halin Lion idan yana hukunta ka kace masa sorry kara fusata shi zakayi har ya maka abun da baka taɓa tunani ba.

Lion wato Romeo baya son kalmar sorry kwata kwata a rayuwar sa, hakan kara arzuƙa sa da fusata sa yake, idan yana hukunta ka kayi kuskuren ce masa yayi hakuri, to kashiga uku, kara masa ɓacin rai zakayi har ya kashe ka ba tare da ya sani ba, ya tsani kalmar sorry ne saboda mum ɗin sa, tun ranar da ta tsugunna a gaban su tace musu sorry yaji ya tsani wannan kalmar.

Ko kaɗan lion bai damu da glass dake wajen ba tsabar ran maza ya ɓaci, ta kan fasassun glass ɗin yabi ya wuce ya damko wuyar Tyrone, sai faman nishi Tyrone yake kamar zai mutu, su kuwa sauran sojojin da suka zo tare da Tyrone tun Romeo bai biyo ta kan su ba sukayi neel down suka kama kunne suna jiran nasu hukuncin.

Riƙo Tyrone da lion yayi ashe akoi glass a jikin rigar Tyrone ɗin, kasan cewar fatar Romeo soft skin ne sosai hakan yasa glass ɗin tayi masa wani wawan yankan a hannun ga kuma wanda ya bi ta kan su ya wuce duk sun suke masa kafa kasan cewar ɓacin rai yasa ya cire takalman kafan sa, wajen duk ya fara ɓaci da jini, amma lion ko ajikin sa, kamar ba jikin sa glass ɗin ta yanka ba, ɓacin rai yasa bai ma ji wani abu wai yanka a jikin sa ba, banda huci ba abun da yake fitar wa.

Wani mahaukacin naushi ya kai wa Tyrone a gefen ciki, kasa kasa Tyrone ya saki ihun azaba, dan ya galabai ta sosai ko mumfashi baya iya yi da kyau bare ihu, da karfi lion ya shaƙe masa wuya, sai hucin yake sauke wa yana furzar da isaka mai bala'i zafi daga bakin sa, yana ji a ran sa ko kashe Tyrone yayi ba zai huce ba.

A wannan hali su daddy suka fito da yar gudun su suka same su, dan sun ji hayaniyar fashewar glass a palon

Ganin yadda Romeo ya shaƙe Tyrone kamar zai kashe shi ne, ga kuma Tyrone ɗin yana ta zaro ido waje alamar rai ya kusa yin hakin sa, hakan yasa Jay yayi shahada ya nufi Romeo da sauri yana faɗin "Please lion please and please let him go" ya kai karshen maganar dai dai lokacin da ya kariso wajen, cikin sadaukar da rayuwar sa ya sanya hannun sa yana kokarin cire hannun Romeo daga wuyar Tyrone, amma ina ko motsa hannun Romeo Jay ya kasa yi, sai fama yake.

A fusa ce Romeo yasa ɗayan hannun sa ya damko wuyar Jay ɗin ya haɗa su da Tyrone ya gwara kan su ji kake gwaram, wani gigitatchiyar ihu Jay ya fasa, kafin ya rufe baki, lion yayi wurgi da shi gefe guda saman dining table, shi kuwa Tyrone har lokacin yana shaƙe masa da wuya yaki sakin sa, dan ji yake ko kashe sa yayi ba zai huce ba, a kan me zai ce watch nasa ne a wajen wayan nan jiga jigan criminals ɗin, dan me zai dangan tasu, yanzu idan a gaban wasu ko yan jarida ya faɗa hakan ba shikenan sai suyi ta yaɗawa suce ashe The general of the army babban criminal ne na duniya ba shi ma

Su daddy kuwa tun da sukaga yau Romeo wato lion ya daki wani soja da kaki a jikin sojan suka san lallai yau ran maza ya ɓaci, domin kuwa lion baya hora sojijin sa da kaki a hijin su dan kamar yadda suke girmama tutan kasar su haka suke girmama kakin sojojin su, amma yau ya daki Tyrone da kaki a jikin sa bai cire masa ba ya fara dukan sa tab yau ran Lion ya ɓaci.

Sai da su daddy sukaga da gaske lion zai kashe Tyrone sanna sukayi kan sa da sauri suna faÉ—in "Please and please lion... Basu kari sa ba ya daka musu wani mahaukacin tsawa, wadda ya sanya dad da John sume wa a wajen, shi kuma uncle Herry ya kwasa da gudu yayi sama abun sa, shi kam Jay tun da Romeo yayi wurgi da shi daman ya sume a wajen

Gaba É—aya bodyguard dake wajen table sun fice daga palon tun farko da lion ya fara dukan Tyrone dan suna mutuwar tsoron lion fiye da tunanin mai tunani.

A hankali Tga yake saukowa daga benen saboda har yanzu wajen na masa ciwo, sai dai yanzu yana iya sanya wando kuma ba laifi ya ɗan samu sauki, saboda Michael yaje ya shafa masa wajen yau da safe, yanzu ma hayaniyan da yaji a palon ne yasa ya lallaɓo ya sauƙo kasa dan yaga menene.

Ganin abun dake faruwa na lion na shirin kashe Tyrone ne yasa Tga karisowa wajen da sauri, already Tyrone ya sume, hannun Tga yasa yana ɗan bubbuga bayan lion alamar rarrashi a fusace lion yayi wurgi da Tyrone tare da juyowa ya damki wuyar Tga, idon sa ya rufe ransa ya ɓaci, baya ji baya gani, bai san suwaye ke gaban sa ba, haka ya ɗaga Tga sama yayi wurgi da shi, gefe guda, Tankar zakin gaske Romeo ya zama yau
Chapter 108 · 0% Book details