← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 126

Sashe 76

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan taga ikon Allah dan watsa É—akin mum da a kayi yafi yadda a ka watsa nasu, haka ta tsallake kayan ta wuce ta duba ATM card na mum ta É—auko ta fice daga É—akin cikin sauri.

Sadiq na tsaye a harabar gidan yana jiran ta bai san meke faruwa ba kuma itama bata sanar da shi ba, tana fitowa suka fice daga gidan tare da rufe ko ina na gidan, suka nufi bakin hanya

Suna tafiya ne Sadiq yace mata "da kika sanya face ɗin nan kin canza ba wanda zai ce kece" bata gane me ya faɗa ba sai dai kawai tace masa "Okey" shiru ya mata har sukaje wajen mai POS ta miƙa ATM nata tace ya bata 20k cikin sauri mai POS ya ciro mata kuɗi kasan cewar yaga kamar suna sauri, ansan kuɗin tayi tare da ATM nata suka wuce suka hau a daidaita sahu suka koma asibiti.

Kamar yadda suka bar su mum haka suka dawo suka same su, sauri sauri Jehan taje wajen sai da kati ta miƙa 1k nan suka haɗa mata kati Sadiq na tsaye a gefen ta, suka miƙo mata kati da canji, kati kawai ta ansa bata ansa canji ba tace bata buƙata, hannu Sadiq yasa ya ansa mata canjin 800, ya miƙa mata a wulakance tace bata buƙata ta bashi, bai damu ba ya zura kuɗin cikin aljihun sa suka wuce suka koma wajen su mum dan su samu damar ganin likita.

A takaice dai sun ga nurse sannan an basu gado a kan mum ta kwanta likita zai zo ya dubata, Jehan ce ta biya kuɗin gadon suka shiga da mum ciki, kwalla Jehan ta fara yi ta zauna kusa da mum ta riƙo hannun ta tana karan to mata duk addu'ar da yazo bakin ta, while su kuma maman Sadiq da gwaggo suna zaune daga ɗan gefen gadon ta kafan mum sunyi tagumi jugum jugum gwaggo na hawaye ta sunkuyar da kan ta kasa, shi kam Sadiq bakin window ɗakin yaje ya tsaya ya dafe kan sa suna jiran dr yazo ya duba mum suji meke damun ta gashi dai ko motsi bata yi kamar ta mutu.

To bari mu leƙa Rimsha kafin dr yazo muji meke damun mum

👹DAULAR MUTUWA👹

Zaune a wajen Rimsha ta kwana, ko motsi bata iyayi saboda matsanancin yinwa da kishin ruwa da take ji, yau kwanan ta na huɗu kenan ba abinci ba ruwan sha, duk da cewa kwana biyu daga ciki a sume tayi su, sosai Ayla ta tausayawa Rimsha duk da cewa bata san labarin taba bata san daga ina Rimsha ɗin ta fito ba, amma dai tana ji a jikin ta tabbas Rimsha bata saba da rayuwar wahala ba, ba yar gidan malam Shehu bace, daga ganin fatar jikin ta da yar gidan hamshakin mai arziki tayi kama ko dai yar gidan sarauta ko yar gidan wani shugaba, haka Ayla ta rinƙa ayyana Rimsha yar gidan wanene a ranta, har rana ya ɗaga, kwata kwata Rimsha bata iya magana ko motsa bakin ta bata iya yi.

Sai da rana ya É—ago sosai ne sannan magicians É—in suka zo suka buÉ—e wa su Rimsha kofar É—akin nasu suka turo musu abinci, sannan suka fice suka bar kofar a buÉ—e, da sauri Ayla ta jawo kayan abincin ta É—auki jug É—in ruwan da suka kawo masu da sauri ta kafawa Rimsha a bakin ta, da kyar Rimsha take iya haÉ—iyar ruwan saboda wahala da ta sha

Ka ɗan ta sha ruwan ta fara kwarara amai tana tari, da sauri Ayla ta riƙe ta tana ɗan bubbuga mata baya, sosai Rimsha tayi aman ruwan da tasha kafin ta koma ta jingunu da jikin bangon, sakin ta Ayla tayi ta matso kusa da Kausar dake kwance rai a hannun Allah itama saboda yinwa, haka Ayla ta ɗago kan ta ta fara bata ruwan, itama Kausar kamar Rimsha kaɗan ta sha ruwan ta fara amai.

Sai bayan sun É—an huta sannan Ayla ta sake basu ruwan kaÉ—an kaÉ—an, a wannan karon basu yi amai ba..

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

B 💞Star Lady💞

TRIPLET'S💞

*THE BEGINNING*

💞STAR LADY💞

WhatsApp me for more information 09162620621

Episode 24

Sai bayan sun É—an huta sannan Ayla ta sake basu ruwan kaÉ—an kaÉ—an, a wannan karon basu yi amai ba, yau dai Ayla bata ci abincin ba ta kyale musu a kan su suci tun da ita taci jiya kasan cewar abincin ba yawa, kallon abincin da kyau Rimsha tayi kafin ta É—ago ta kalli Ayla cikin raunanniyar murya tace "Ayla wannan miyar ai kamar naman mutun ne a ciki" gyaÉ—a mata kai Ayla tayi kafin tace "Eh naman mutun ne a ciki, nima kullun iya shinkafar kawai nake ci bana sa miyar, sai kuma fruits É—in nan shima ina cinyewa" shiru Rimsha tayi tana mamakin a ran ta tana faÉ—in "Wa ina zubillah ya Allah ka kawo mana É—auki, ya Allah dan karfin mulkin ka, dan karfin izzan ka da girman ka ya Allah ka tarkatsa wannan gida na azzalumai cikin gaggawa, ya Allah ka kawawo bayin ka musulmi É—auki, Allah kayiwa wa'yannan azzaluman hukunci mai tsanani tun a duniya, ya Allah kai ka É—ai kasan adadin rayukan bayin ka da ya salwanta a nan" zuba mata ido Ayla da Kausar sukayi suna kallon yadda ta zubawa abincin dara daran sleeping eyes tana tana zancen zuci.

Ganin ta ki dai na kallon abuncin ne yasa Ayla ta ɗan taɓa ta, ɗago dara daran sleeping eyes nata tayi ta kalli Ayla ɗin "Kuci shinkafar mana, baiwar Allah ni gashi baki faɗa mana sunan ki ba ma" cewar Ayla, lunshe ido Rimsha tayi tare da mayar da kan ta ta jingina da jikin bangon ɗakin tana sauke ajiyar zuciya a hankali.

Cikin sanyin murya tace "Sunana Rimsha kuma ni ba zan iya cin wannan shikafar ba, dana ci namar mutun gara yinwa ta kashe ni" girgiza kai Ayla tayi kafin tace "A'a ni bance kici namar ba miyar ma gaba ɗaya bance ku ciba iya shikafar kawai nace kuci sai kuci fruits ɗin, shi kuma miyar ku kyale musu abunsu zasu zo su ɗauka anjima, kuci da wuri mu fita waje mu sha iska, muyi hira da sauran yan gidan zuwa yamma za'a rufemu" kanta na jingine da jikin bangon ba tare da ta ɗago ba ta waro dara daran sleeping eyes nata a kan face ɗin Ayla kasa kasa tace "Ni ba zanci shinƙafar bama, dan ko nace zan ci amai kawai zanyi dan haka kawai kuci" tayi maganar cikin harshen turanci, kallon kausar Ayla tayi kafin tace "Matso kici kinji?" ba musu Kausar ta matso ta fara cin gayan shinkafa babu miya

ÆŠaukan Apple Ayla tayi ta sanyawa Rimsha a hannu tana faÉ—in "kiyi hakuri kici wannan kinji?" rike apple É—in Rimsha tayi tana matsar kwalla haka ta kai apple É—in É—an bakin ta, ta É—an ciza tana matsalar kwalla.

Haka Rimsha wannan apple É—in kawai taci yayin da ita kuma Kausar taci shikafa fari ba miya sannan suka haÉ—a da fruits É—in ita da Ayla su kaci.

Bayan sun gama ne Ayla tace suzo su fita waje, make kafaÉ—a Rimsha tayi tana faÉ—in "No i can't go anywhere" "Kiyi hakuri muje mu É—an kalli hasken waje kinji ko" Ayla tayi maganar a raunane

Da kyar Rimsha ta iya dafa bango ta miƙe suka nufi waje sai dafa bango take suka fito tsakar gidan, nan fa Rimsha taga duniya ga yara nan har da manya mafiyawancin su suna zaune ne a bakin kofar ɗakin su, dukkan su suna bushe kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin yinwa da wahala.

Saman wata yar benci Ayla ta wuce taje ta zauna ta zubawa yan gidan ido wadda ko wace ke zaune a kofar ɗakin ta, duk yinwa ya cinye su, sun rame sun bushe sun zama kamar kashi da rai, ko maganar kirki basa iyayi, saboda yinwa mafi yawancin su basa cin abincin gidan kasan cewar da naman mutun ake miyar sai dai suci fruits wasu suci da gayar shinkafa wasu kuma suci fruits zalla amma basa taɓa shan miyar,

kusa da Ayla Rimsha ta zauna tana bin gidan da kallo tana mamaki a ranta.

Can idon ta ya hango mata wani mutun dake zaune ya haɗa kai da gwiwa yayi shiru, zuba masa ido Rimsha tayi na yan mintoci kafin ta miƙe da kyar ta nufesa
a tsorace Ayla tace "Meesha karkije wajen mutumin nan fa zai iya marinki dan bai da mutunci ko kaÉ—an" a ta kai ce Rimsha tace "Sunana Rimsha ba Meesha ba" da sauri Ayla tace "Irin sunan wata friend na a islamiyar mu ne gare ki kuma ita Meesha muke ce mata shiyasa na kiraki hakan amma kiyi hakuri yanzu dai ki dawo karki je wajen sa" shiru Rimsha tayi kamar bata ji me Ayla ke faÉ—e ba ta wuce abun ta ta nufi mutumin tana jan kafa da kyar.

A gaban sa ta tsugunna cikin sanyin murya tace "sannu" shiru yayi bai mata magana ba kuma bai É—ago ba, sake mai mai ta maganar nata tayi nan ma bai É—ago ba, sai a karo na uku ne ya É—ago a zafafe yana zaro ido ya É—aga hannu zai mareta kenan, a sukwane ta rimtse idon ta a hankali ta furta Wayyo Allah na, zaro ido sukayi dukkan su lokaci guda jin Rimsha ta iya furta sunan Allah, cikin sauri shi ma mutunmin ya kwatanta ko zai iya kiran sunan Allah amma ina ya kasa, ita ma Rimsha tayi kokarin sake kira amma ina sunan yaki fitowa, haka ta hakura ba dan taso ba
Chapter 76 · 0% Book details