Sashe 64
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokaci ya ja haka James ya rinƙa wasa da tunanin ogan su a kan kashe GAR, yayin da shi kuma daddyn Jelly ya samu saukin takura daga wajen baban Muneer haka zalika shi kuma Abbi dukiya sai haɓaka take yana kara samun kuɗi, Allah ya sawa abun albarka, yayin da shi kuma, daddyn su Rimsha siyasa ta gaba to ko ina sunan sa ke yawo jama'a na son shi sosai, ta ko ina masoya ne, Nawazudden, Nawazudden, ta ko ina, sosai daddy ke murna da farinciki a kan haka, tun wan nan tafiya da su Imran sukayi basu sake samun dama sun zo Nigeria ba, saboda abubuwa da suka sha musu kai, yayin da ita kuma Umaisha ta biyewa Aafia ta dai na sanya hijabi, duk wani abun da Akil yace mata sai da ta watsar ta dai na yi, kasan cewar abubuwa sun sha kan sa sosai baya samun damar bibiyar me take, sai dai bata sanya attachment da eyelashes, sune abun da ya rage a cikin dokan da Akil ya kafa mata bata karya ba, ita kuwa Aafia komai sanya wa take hankalin kwance, shima Irfan tun wan nan tafiya da yayi sau ɗaya yazo hutu, ko da yazo ya tsawatar wa Aafia sosai a kan sanya hijabi da ta daina sanya attachment da eyelashes da sauran su, amma yana komawa ta watsar da duk wani nasiha da tsawatar wan da ya mata ta koma gidan jiya
shi kuwa wan nan mutumin da suka haÉ—u a kofar gidan su Rufaidat yasha neman ta har ya gaji basu sake haÉ—uwa ba amma bashi da burin da ya wuce sake ganin ta, Abbi bai cika zama a gida ba shi yasa su Aafia ke yin abun da suka ga dama, sai dai duk wan nan abun da suke sun san ba dai dai suke ba dan Abbi bai barsu haka nan ba sai da ya tabbatar ya basu ilimin addini, so sun san komai sun san ba dai dai suke ba, amma suka take sani.
A ɓangaren su Abba kuwa duk karshen shekara wayan nan dodannin suna zuwa musu, kuma sai sunyi sati suna zane su kafin su tafi, in sun tafi kuma sai bayan shekara suke sake dawuwa, babban damuwar shine da dodannin sun tafi shikenan suma zasu manta komai hakan yasa basu samu dama sun iya sawa a musu saukan Al Qur'ani mai girma ba kasan cewar sun manta komai basa iya tuna komai.
*ABUJA*
Kamar kullun yau ma daddy na gida bai fita ba missalin karfe 3 na yamma, yau suna tare da uncle Shitu, sai hira suke a palo, uncle Shitu na ta hira da Rimsha ita kam Jehan daman ba shiri take da kowa ba, dan Uncle Shitu bai isshe ta kallo ba, a cewar ta duk wanda ke karkashin daddyn ta to a karkashin ta yake dole ya girmama ta,
Jehan yar sanda sosai take bawa kan ta horo tayi ta azabtar da kan ta ta fannin gudu da ɗaga karfe, iya bin kwakkwafi a kan abu, bata da yawan surutu kamar dai ita ma Rimsha ɗin basu da yawan surutu, sai dai Jehan a koi ta da zafin kai, rai na mutane, rashin kunya, tsaurin ido, shagwaɓa, izza da kuma girman kai, amma duk da haka tana da ilimin addini sosai sai dai bata kai Rimsha ba amma tafi Rimsha ilimin boko, dan ita ta ɗauki boko da muhimmanci, ita ma Rimsha tana da ilimin bokon sai dai ko a School daman Jehan tafi Rimsha da class, ita ma Rimsha bata son rai ni amma tana da fara'a ga son mutane ba ruwan ta shiru shiru bata son hayaniya.
Sai hira suke zubawa daddy na cike da farinciki ita kuwa Jehan ta lafe a cinyar Gwaggo sai shagwaɓa take zuba mata, gwaggo na biye mata, mum dad suna hira Uncle shitu na hiran da Rimsha a kan wani hadisi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama in da yake cewa ka kyautatawa Mumini kyakyawan zato, ka zauna da kowa zuciya ɗaya, idan kayi hakan ko da wani yayi niyar cutar da kai Allah ba zai bashi dama ba dan kai baka kullace sa a ranka ba.
Suna tsaka da hirar su mai gadi yayi sallama, da fara'a daddy ya amsa masa, har kasa mai gadi ya duƙa yace "Alhaji kayi baki a waje" kasan cewar daddy ya saba da ansan baki kala kala ko yaushe musamman ma da siyasa ta gaba to hakan yasa bai damu ba ya miƙe ya nufi waje yana faɗin "Ina zuwa baby Jehan" jikin sa sanye da jallabiya baka.
Fitan daddy ba'a da 5mins ba uncle Shitu ya miƙe yana faɗin "Bari na bi bayan Alhaji sai mu dawo tare" da fara'a mum ta amsa masa da to, san nan yayi waje.
Yana fita harabar gidan sai bai ga kowa ba, cikin sauri ya nufi waje, dai dai lokacin wasu jibga jibgan sojoji ke kokarin tura daddy cikin motar su, jibga jibga ne sosai da sosai gashi dukkan su face nasu da face mask zasu kai su takwas, cikin sauri Uncle Shitu yace "Meke faruwa lafiya?" ÆŠaya daga cikin sojojin ne ya nunawa uncle Shitu ID card nashi na aiki ba tare da yayi magana ba, kallon daddy uncle Shitu yayi kafin yace "Meke faruwa Alhaji" girgiza kai daddy yayi kamar zai yi kuka yace "Wai wani É—an kidnaping suka kama yace musu nine mai gidan shi nike basu makamai suke sace mutane, nayi kokarin su barni na kira lawyer amma sun ki yarda, ni ina jin akoi abun da a ka shirya min ne, please Shitu ga amanar family na ka kulamin da su kafin na dawo karka sanar musu abun da ke karuwa san nan ka kira min lawyer mu haÉ—u da kai a office É—in na su" innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine kawai abun da uncle Shitu ke iya furtawa, muryan sa har kerma yake wajen cewa "bari na fito da mota sai muje tare" basu jira uncle Shitu ya gama magana ba suka ja motar su a guje suka tafi da daddy kamar zai yi kuka
cikin sauri Uncle ya koma cikin gida ya É—auko mota, duk abun da ke faruwa mai gadi na kallon su sai salati kawai yake, uncle Shitu na kokarin jan motar mum ta fito, tana faÉ—in "Lafiya Shitu fita kuma zaku yi ne ba sallama" in brief uncle Shitu ya sanar da ita sojoji sun kama da daddy da kuma abun da ke faruwa amma yanzu zai bi bayan su, su taya su da addu'a komai zai dai dai ta In Sha Allah, sosai mum ta shiga tashin hankali mara misaltuwa har jiri jiri take gani saboda tashin hankali nan take taji kan ta ya mata yauyi ta kasa motsawa daga wajen, har uncle Shitu ya ja motar mai gadi ya buÉ—e masa gate ya fita da gudun gaske yabi bayan su daddy.
Slowly mum ta juyo da nufin ta koma cikin gida sai ganin Jehan tayi tsaye a bayan ta tana hawaye, da kyar ta iya É—aga kafafun ta da suka mata nauyi kamar dutse ta karisa wajen Jehan É—in, ta rungumeta tana goge mata hawaye tare da bata baki, a haka suka koma cikin Palo.
Da gudu Jehan ta faɗa jikin gwaggo tana kuka tana faɗin "Gwaggo uncle yace an kama daddy wai ɗan kidnaping ne" zubur gwaggo ta miƙe tare da dafe girjin ta tana ambaton sunan Allah, ita ma Rimsha miƙewa tayi cike da shin hankali nan take hawaye suka fara wanke mata fuska, mum na kokarin yin magana sukaji sallama daga bayan su, a bakin kofar shigowa palon, a sukwane suka juya, wasu yan sanda ne sanye cikin kayan aikin su hannun su riƙe da wasu mai ɗauke da wasu rubutu, kai tsaye suka shigo cikin palon basu jira wani izini ba kuma
Kai tsaye wajen mum suka nufa suka miƙa mata takardun da bairo a kan ta sanya hannu, ko kaɗan bata damu ba a tunanin ta tun da har suka iya wuce asalin babban gate na estate ɗin suka zo nan to manyan yan sanda ne, kuma kila a kan case ɗin daddy suka zo, dan haka bata tsaya duba takardun ba kawai ta sanya hannu jikin ta sai kerma yake
gwaggo ce tayi ta maza wajen cewa takardun me wan nan, already lokacin mum ta sanya hannun sun miƙawa Rimsha a kan itama ta sanya hannu, ko kallon in da Gwaggo take basu yi ba
cikin kiɗi ma da tashin hankali Rimsha ta sanya hannu jikin ta sai kerma yake, ansan takardun daga hannun Rimsha sukayi suka miƙa wa Jehan ita ma ta sanya hannu, kallon tsab Jehan ta musu kafin tace "Wace dokace ta baku damar shigowa gidan matan aure kuma har cikin palo ba tare da izinin masu gidan ba kuna kartin maza da ku? San nan wan nan takardun me, ba zan sanya hannu ba sai na san takardun menene" tayi maganar babu alamar tsoro ko kaɗan a face nata, sai lokacin mum tayi nadamar sanya hannu da tayi a takardun, taruɗe sosai shi yasa tayi saurin sanya hannun dan bata kawo komai a ran taba.
Ba tare da sun yi magana ba babban cikin su mai riƙe da takardan ya ciro ID card ya nuna mata, kallon sama da kasa ta masa ko tsoro babu a face nata tana ganin kartin maza har huɗu amma bata ji shakkan su ba tace "ID card ba shine na tambaye ka ba, abun da na tambaye ka wace dokace ta baku damar shigowa cikin gidan matar aure ba tare da izinin su ba, kuna kartin maza da ku, san nan kuma takar dan me kuka kawo mu sanya hannu, ba zan sanya hannu a komai ba sai naji na menene ko kuma ku bani takardan na karanta"