← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 126

Sashe 6

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Da zaman ta ba'afi 10mins ba dr yazo jin dr yazo yasa ta fito da gudu tazo ta miƙa masa Dolly tana faɗin "Uncle ka dubata taki cin abinci kwata kwata" tayi maganar kamar zata yi kuka tun daga nesa dr ya kura mata ido yana kallon ta har ta kariso gaban sa tana miƙa masa Dolly hankalin sa na kan kyakkyawar face na ta bai ma san tana miƙa masa wani abu ba sai magana take masa amma bai ji taba hankalin sa yayi nisa kallon face nata kawai yake, tana kokarin sa masa kuka dady ya fito yana faɗin "dr Sadiq har ka iso?" Yar firgigit dr yayi kafin yace "Eh na iso" yayi maganar tare da ansan dolly da jelly ke miƙa masa cikin sauri ya fara dubata da gudu jelly ta wuce ta rungumi dady tana faɗin "Dady bana son a yiwa Dolly ta allura" rungumeta dady yayi suka koma saman kujera mai zaman mutun 2 suka zauna shi ku ma dr yana aiki yana satar kallon jelly
`````Dr`````
Babban mutun ne wadda a kalla zai kai 35 year a duniya yana da kyan sa dai dai gwargwado É—ane ga abokin dady suna shiri da dady sosai.
Miƙewa dady yayi yana faɗin "My baby zauna ki kalli Dolly ki dr na duba ta bari na yi shirin zuwa office ko" jinjina masa kai tayi tana faɗin "To dady" wucewa dady yayi yana faɗin "Sadiq dan Allah ka duba mana dollyn nan da kyau muji ainihin meke damun ta yasa bata cin abin ci kaga kwana ki ma haka ta mana to dan Allah wan nan karon kam ina son sanin asalin a bun da ke damun ta" ya kai karshen maganar tare da hayewa saman ya shiga bedroom na shi dan shirin zuwa office.

Dady na tafiya dr Sadiq ya dubi jelly da ta buga takumi ta tsare sa da manya manyan idon ta tana kallon yadda yake duba dollyn nata ɗaga ido yayi ya kalli sama ganin cameran palon a kunne ne yasa ya ɗan ɓata rai tare da mai da kan sa kan dolly ya ci gaba da yan dube duben sa ita dai jelly ta zuba masa ido tana kallon sa.

Wacece jelly

Jalila kenan ya ɗaya tilo ga Alhaji Abdul Malik Salman Sultan tun jelly na da shekara biyu mahaifiyar ta ta rasu dadyn ta kuma yaki kara yin wani auren ya ci gaba da zama da yarsa su biyu suke rayuwa cikin wan nan Katafaren gidan sai masu musu girki Nana da Zuwaira Alhaji Abdul Malik bai cika zama sosai a gida ba wan nan dalili yasa ya sanya camerori a gaba ɗaya longu da sako na gidan sa dan ya rinƙa ganin halin da yar sa ɗaya tilo take ciki yana bala'i son jelly sosai fiye da ran sa, duk abun da take so shi ma shi yake so yana son farincikin ta kasan cewar ita ka ɗai ke garesa yan uwan maman ta sunyi sunyi ya bari su ɗauke ta su rike ta a wajen su amma yaki san nan anyi anyi da shi ya kara wani Auren nan ma yaki karawa dan gani yake duk wadda zai auro ba zata rike masa jelly yadda ya dace ba shi yasa yayi zaman sa daga shi sai ita sai masu aiki.
Wan nan shine ta kai taccen wacece jelly.

Shirye cikin wata dakakkiyar shadda sky blue dady ya fito ya sanya hula da takalma farare sai kamshi yake zubawa yayi kyau sosai, in da ya bar jelly nan ya dawo ya same ta ta buga tagumi tana kallon dollyn ta kusa da ita dady ya dawo ya zauna yana faɗin "My baby kar ki damu dolly zata samu lafiya ta dawo normal" kwantar da kan ta tayi saman cinyar sa tana faɗin "Dady ina jin kamar zan yi kuka" kallon dr dady yayi kafin yace "Dr Sadiq ya ake ciki meke damun dolly ɗin namu" satar kallon jelly dr yayi kafin ya fara magana "Alhaji zaka fitane?" Gyaɗa masa kai dady yayi "To muje tare sai na sawo mata magungu nan da suka dace ko? Dan gaskiya dolly bata da lafiya tana da matsala a zuciya amma In Sha Allah tana shan maganin nan zata samu sauki" "Okey to muje mana amma ni zan wuce Office idan ka sawo maganin sai kazo ka bata" "Miƙewa dr yayi yana faɗin "Ba damuwa zan dawo na bata maganin jelly a kula da dolly sai na dawo yanzu zan zo na bata magani ta warke taci abinci kin ji ko? Da fara'a ta amsa da "To uncle sai kun dawo" . A tare dady da dr suka fice daga palon kowa ya shiga motar sa driver yaja dady shi kuma dr ya ja kan sa suka fice daga gidan suka bar jelly rungume da dolly tana jiran dr.

KATSINA
Chapter 6 · 0% Book details