← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 126

Sashe 86

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tabbas baba ya fahimci babu abun da duna ya fahimter dan gane da bayanan sa dama kuma yasan mawuyacin abune dunan ya fahimter kasan cewar sa jahili sosai wadda bai taɓa sanin wani abu ba face shan jini, hakan yasa baba yayi shiru kawai yana addu'a a ransa Allah yasa duna ya gane gaskiya, Allah yasa yana da rabon shiriya, ita kuwa Rimsha ta kan kame baba saboda tsoron ganin yadda duna ya rikiɗe ya dawo kyakkyawan saurayi, faritas da shi ga dogon hanci har baka, har da wani curly hair kwance masa a kai har zuwa gaban goshin sa, kyau iya kyau duna ya haɗu, sai satar kallon sa Kausar take tana tsoro su haɗa ido.

Kallon ta duna yayi kafin yace "Fine girl why kika cika tsoro ne haka?" Kara matsawa jikin baba tayi dan tsoro, saboda har muryan duna sai da ya sauya, ya dawo mai cool voice, ita ma Kausar ta tsorata sosai, ita kuwa Ayla ko a jikin ta, dan ta saba ganin abun da yafi wannan ma, sai dai tasha mamaki yau saboda son da duna kewa Rimsha ya biyota har nan yazo tambayar kwana biyu lafiya bata fito waje ba, tab lallai akoi kura, aure tsakanin mutun da aljani, aljanin ma magician tab lallai Rimsha kin cire tuta, shi kuwa duna ba abun da yake tunawa sai kyan fuskar Rimsha da kuma dimple nata idan tana magana.

Ganin duna yayi shiru ne, yasa baba yace "lafiya duna" miƙewa yayi yana faɗin "zan dawo anjima sai ka faɗa min me ya kama ta nayi kafin wannan yarinya ta dawo nawa" to kawai baba yace masa, sannan ya fice daga room ɗin.

Dawo da kallon sa baba yayi kan face ɗin Rimsha dake ta zazzaro sleeping eyes nata, cikin nitsuwa ya fara magana "kina jina Rimsha, na san baki son shi kuma bana miki fatan ma ko hannun ki ya taɓa, amma karki nuna masa hakan, dai basu da imani ko ɗigo a ransu, idan yazo ki biye masa kuyi hira, a hankali har mu ja shi ya shiga cikin addinin mu, idan ya shiga addinin Musulunci, imani ta ratsa shi to komai zai yi sauki, amma yanzu idan kika yi avoiding na shi to tsab zai iya kashe ki, kuma kafin ya kashe ki, zai iya biyan bukatar sa a kan ki tun da kinga ra'ayin hakan ya nuna, zai biya bukatar sa sannan kuma ya kashe ki da kan sa, kuma zai dafa namar jikin ki ya cinye" kara tsorata Rimsha tayi nan take taji hanjin cikin ta ya kaɗa shi ru tayi tana tunanin yadda zata kaya tsakanin ta da wannan bakin aljanin.

💞KADUNA💞

Aafia

Yau tun safe Aafia ke ta surfa uban bala'i a gida wai an sace mata waya, hayaniyar ta ya tashi Abbi da Aunty daga barci, suka sauko Palon kasa nan suka same ta, ta tasa mai aikin da Abbi ya kawo a gaba wai ita ta sace mata waya, sai kuka yarinyar take tana ta rantsuwa a kan wlh ba ita bace, abun gwanin ban tausayi, sai wani girgiza Aafia keyi da kugu, tana surfawa yarinyar masifa, while ita kuma Umaisha tana zaune saman sofa ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya, sai faman latsa nata wayar take taba turɓune fuska, "Meke faruwa Aafia" Abbi ya tambaya yana kallon ta, kukan makirci ta sawa Abbi tare da tafiya ta rungume sa tana faɗin "Abbi jiya da daddare ina barci naji motsi dana ɗago kai na, sai naga wannan mai aikin ne, to ban kawo komai a rai na ba kasan cewar nasan wani lokaci tana kawo mana tea da daddare, yau da safe na tashi banga waya taba, kuma wlh Abbi ita kaɗai ta shiga bedroom na mu, kuma kafin nayi barci nayi amfani da wayar, dana gama na ɗaura saman bedside drawer nayi barci" already ita kam Aunty tasan sharri Aafia keyiwa mai aikin, dan wlh ba wani tea ɗin da yarinyar nan ke kai musu da daddare, mawai makircine dan sun ga ba mai iya ce wa karya suke, ita kuwa yarinya sai kuka take tana faɗin "wlh ban ɗauki wayar taɓa" shiru Abbi ya ɗan yi kafin yace "to muje ki sai wata wayar mana" turo baki Aafia tayi tana faɗin "Ni Abbi wancan wayar nake so, saboda ina da abubuwa da dama masu amfani a cikin ta" kasan cewar shi Abbi namiji ne kuma babba mai hankali, sai ya gane karya Aafia keyi, hakan yasa yace "to jeki ni zan ansa miki wayar" turo baki Aafia ta kara yi cikin shagwaɓa tace "Abbi muje room nata mu duba mana, nasan ba zata wuce ɓoye wayar a room ɗin ba, kuma wlh idan yana wajen Abbi barin gidan nan zatayi dan ba zamu zauna da ɓarauniya ba" "ke dai jeki kiyi shirin zuwa school zan ansa miki wayar da kai na na ce ko, batun zaman ta a gidan nan kuma ni zan yanke hukunci" ba dan haka taso ba, ta wuce rai a ɓace ta haye sama,

Dawo da kallon sa kan Umaisha yayi kafin yace "Ke ba zaki tashi bane, kin zauna kin tasa mu a gaba" tun bai gama rufe baki ba Umaisha ta miƙe ta wuce tabi bayan Aafia, dawo da kallon sa kan Aunty dake tsaye a bayan sa tana mamaki yayi, a nitse yace "Je ki duba ɗakin yarinyar ki ɗauko min wayar" ba musu Aunty ta wuce dan ita ma tasan can Aafia ta kai wayar ta ajiye, dan tayiwa yarinyar sharri

Dawo da kallon sa kan yarinyar Abbi yayi a nitse yace "Kiyi shiru" cikin kuka tace "Wlh baba bani na ɗauka ba, ni bana sata kuma ban taɓa yi ba, ka tambayi mamana kaji, dan Allah kada ku koreni daga gidan ku, wlh babana ya rasu bamu da mai bamu abinci, da kuɗin aikin nan nake saya mana abinci" tsugunnawa Abbi yayi ya goge mata hawaye yana faɗin "Ya isa tashi kije kiyi kwanciyar ki, ni ba yaro bane kinji ko? Kuma babu wanda ya isa ya koreki daga gidan nan, dan ba su suka kawo ki ba, ko bana nan wata tace ki bar gidan nan kice ba in da zaki je sai wanda ya kawo ki ya dawo ya mai dake" Gyaɗa masa kai tayi tana ta zuba masa godiya, ta wuce ta koma ɗakin ta.

Abbi na wajen har Aunty ta dawo hannun ta riƙe da wayar Aafia, amsar wayar Abbi yayi ya nufi bedroom na su Aafia, ita kuma Aunty ta wuce nasu bedroom ɗin.

Tsaye gaban mirror ya isko Aafia, tana tsaye tana faman feshe jikin ta da perfume, cikin nitsuwa ya fara magana ta hanyar amfani da matsayin sa na babba kuma mahaifi a gare su "ina son ku sani duk abun da mutun yayi a duniyar nan kan sa yayiwa, in ma mai kyau ko mara kyau, kuma kullun ina mai tsawatar muku a kan ku rinƙa jin kan nakasa da ku, sannan ku tausaya masa amma bakwa ji, ku dai na ɗaukan duniya da zafi, dan ba wata tsiya a duniyar nan, kun san da haka, tun da duk da wayon ku Mahaifiyar ku ta bar gidan nan, sannan kuna sane da dalilin da yasa ta bar gidan nan, ta guje mu ne saboda bani da kuɗi na shiga jarabawar Ubangiji, amma hakan da tayi yasa na samu nakaso ko wani abu, gashi kwance tashi ba wuya a wajen Allah, Allah ya azurta ni da arzikin da ban mallaka a baya kafin na aure taɓa, kuma kuna sane 3 years back, mun sake shiga jarabawar Ubangiji, Allah ya aiko Husain ya taimake ni, ba dan haka ba ai da yanzu kuma sai dai ku tafi aikatau gidan wasu, wannan bai ishe ku ishara ba? To ina mai kara jan kunnen ku, kubi duniya a sannu, dan ko wani lokaci duniya na iya juyawa daku" ya kai karshen maganar tare da miƙa mata wayar ya fice da bedroom ɗin.

A tunanin sa maganar sa ya shiga kunnen su, sai dai abun da bai sani ba, maganar Rufee ta riga nasa zama a kunnen su, sun riga sun yi nisa, Abbi yayi kuskure wajen rashin binciken da waye suke kawance, idan su fita ina suke zuwa, me da me suke aikatawa a School, duk wannan bai sani ba kuma bai damu da ya sani ba, ka san cewar ba wani zama yake a gida ba, wannan shi ne É—aya daga cikin babban illar rashin uwan a kusa da mutun.

Abbi na fita Aafia ta ja guntun tsaki tare da turo baki tana faɗin "wlh Abbi bashi da wani aiki sai yiwa mutane wa'azi kamar wani malami, sai kace mu bamu yi karatu ba" Umaisha ce ta ansa zancen da cewa "Ki godewa Allah Ummi da Yaya Irfan basa nan, ai sun fi Abbi masifa musamman ma Ummi, ni gwara ma da ta tafi, da yanzu tana nan tan faman takura mana, a kan abubuwa da dama, ni bari na kira yaya Irfan ɗin ma na lafaza shi ya bani kuɗi koda 200k ne dan na ɗan yi broke" cikin sauri Aafia tace "Ai kuwa kin tunamin zan biya ta bank na cirowa Rufee 100k ɗazun ta kirani tace tana son 100k kuma kashe take bukata" turɓune fuska Umaisha tayi kafin tace "Kuma sai ki bata? Sai kace wata uwar ki, nifa wlh Rufee nan bata burgeni kawai dai ban son nuna mata hakan ne yasa nake biye mata, amma dai natsane ta wlh" "wlh Umaisha idan kika sake shiga tsakani na da Rufee sai ranki ya ɓaci, ba ruwan ki da ni" ta kai karshen maganar tare da jan dogon tsaki, ta wuce wajen drawer kayan su, ta ɗauko wasu riga da wando ta sanya

kayan sun matse ta sosai, sannan ta É—auko suwaga bag É—in ta ta sanya Booth a kafar ta, wani É—an handkerchief fari ta É—aura a kan ta, sannan ta É—auki key É—in motar ta, a fusace ta fice daga É—akin, ko breakfast ba ta tsaya ta yi ba bare kuma yiwa su Abbi sallama, haka ta wuce ta fice daga gidan, dan tana da class 8 dai dai.
Chapter 86 · 0% Book details