← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 126

Sashe 81

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa yayi saman sofa ya zauna yayi shiru yana kallon Tga yana jiran amsar tambayar sa, dan shi baya mai mai ta magana idan yayi, idan baka ji bama dole dai ka bashi amsa, already Tga ya san da wannan dan haka sai ya rarrafa ya koma kusa da kafafun Romeo cikin nitsuwa da shakakiyar murya yace "I'm sorry lion it's was a mistake" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me Tga ɗin yace ba, ganin haka yasa Tga ya gane, bayani abun da ya haɗasu faɗa da James kawai Romeo yake buƙatar ji, cike da tsoron, murya na rawa ya fara bawa Romeo labarin abun da yafaru tum daga farko har kashe.

Slowly Romeo ya kai kallon sa kan mutumin, sannan ya kalli James dake ta faman juyi a wajen yana numfashi da kyar da kyar, dawo da kallon sa kan Tga yayi yana mamakin, wai ace James ya samu accident dan bai ji ciwo ba ya dawo gida kuma Tga ya masa irin wannan dukan, nan take yaji wani ɓacin rai ya rufe masa zuciya, a fusace ya miƙe rai a ɓace ya fara dukan Tga, daddy na bashi hakuri ya kyale Tga haka ai ya daku amma ina ba wanda ya saurara dan Tga ya bashi haushi, ace James yayi accident Allah ya tsare bai ji ciwo ba ya dawo sannan Tga ya kama sa ya masa irin wannan duka dan yazo da wanda ya buge da mota gida.

Sosai Romeo ya bugi Tga har sai da yaji ya ishe sa, yayin da shi kuma Tga ya sume baya ko motsi, yayi lilis a hannun Romeo, dan ma yayi Sa'a Romeo bai É—au zafi sosai ba

Cike da jin haushin Tga Romeo ya wuce ya nufi in da James ke kwance yana mai da namfashi da kyar da kyar, ko kallon in da su daddy suke bai yi ba, ya ɗauki James ya saɓa sa a kafa ɗan sa ya haye saman bene ya koma bedroom na sa.

Yana tafiya su daddy sukayo kan Tga, dan bashi taimakon gaggawa kasan cewar daddy likitane.

Shi kuwa Romeo saman katafaren gadon sa ya kwatar da James kusa da Michael dake kwance yana kuka.

Ko kallon in da Michael É—in yake Romeo bai yi ba, ya wuce ya É—auko kayan aiki ya fara duba James.

Sai bayan James ya dawo hayyacin sane yace "Please lion ka taimaki mutumin nan da na buge da mota" shiru Romeo ya masa kamar bai ji me yace ba, shi kuma Michael wai yayi fushi da shu shi yasa ya kwanta shiru yana hawaye.

After 40mins

Sai bayan Romeo ya gama duk abun da ya dace yayiwa James ne sannan yace su kira likita ya duba mutumin, amma shi ba zai duba kowa ba, da sauri James ya miƙe, jikin sa ba kwari ya fito ya nufi wajen daddy, dan ya rokesa ya duba mutumin, abun mamaki ko da ya fito palon sai bai ga mutumin ba, yaji tsoron ko dai sunje sun jefar da mutumin ne kamar yadda suka faɗa, da sauri ya nufi hanyar fita daga palon dan yaje ya tambayo security waya fita da mutumin nan

Yana kokarin fita muryan dad ta dakatar da shi "James where are you going" a sukwane ya juyo ya kalli daddy cikin sauri yace "Please dad where is the man I brought" murmushi daddy yayi kafin ya sanar da James mutumin yana É—akin duba marasa lafiyar su, da sauri James ya nufi wajen dan alhakin kula da mutumin na rataye ne a wuyar sa.

Yaji daÉ—i sosai ganin yadda daddy ya bawa mutumin nan kulawa, har da karin ruwa daddy ya masa, sannan mutumin ya farka, kafar sa da ya karye kuma daddy ya sanya kafar cikin wata na ura na aikin su likitocin.

Karisawa cikin É—akin James yayi, ya zauna a gefen mutumin yana faÉ—in "Sorry" kallon sa mutumin yayi kafin ya É—an É—aga masa kai kawai, "What is your name?" James ya tambayi sunan mutumin, a hankali mutumin yace masa "Musharraf" jinjina kai James yayi kafin yace "are you an Arab from saudia?" GyaÉ—a masa kai mutumin yayi kafin yace "Yes" shiru James yayi kafin ya sake cewa "Are you a Muslim?" Nan ma eh mutumin yace masa "Okey how is your body now" James ya faÉ—a yana kokarin mikewa ya nufar hanyar fita "Alhadulillah" Musharraf ya faÉ—a yana bin James da ido kawai amma shi kaÉ—ai yasan azaban da yake ji.

Ficewa James yayi daga room É—in yana jin daÉ—i da mutumin bai mutu ba, a palo ya isko daddy, da fara'a ya yiwa daddy godiya, shima daddy ba karamin daÉ—i yaji ba, dama kuma ya kula da mutumin ne dan James yaji daÉ—i, yana son yaga yaran sa suna nuna masa soyayya kamar yadda yake son su amma basa hakan sai dai tsawa da faÉ—a, shi yasa yanzu yake kokarin yin duk abun da suke so dan ya jawo su jikin sa.

Wannan kenan ku koma Nigeria muga meke faruwa

💞NIGERIA💞

💞KATSINA💞

kallon Sadiq tayi idon ta a bushe, dan yanzu gaba ɗaya ta dai na jin kuka zuciyar ta ya bushe, cikin sauri tace "Sadiq ka nemomin masu sayan gidan nan" sannan ta dawo da kallon ta kan gwaggo dake ta faman kuka tace "Gwaggo bamu bukatar mu fitar da Mum waje kuɗin aiki kawai zamu nema mu wuce babban asibiti, na san dai kuɗin gidan nan zai isa ai mata aiki, daman kuɗin jirgin fita wajen shi ne mai tsada, dan haka a sayar da gidan nan a mata magani daga baya zamu san abun yi bayan ta samu lafiya" ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi cikin ɗaki.

Jim kaÉ—an ta fito sanye da abaya a jikin ta tana faÉ—in "Gwaggo ki koma hospital ni da Sadiq zamu nemo mai sayan gidan" kasa magana gwaggo tayi dan ta jinjinawa Jehan wannan shine dalilin da yasa a kace ilimi na da amfani yau gashi ilimin Jehan ya taimaka musu, dan kwata kwata bata kawo zancen sai da gida ko kuma karsu fita waje da mum ba sai gashi Jehan ta kawo musu mafita.

Jiki ba kwari gwaggo ta miƙe ta wuce hospital wajen mum, su kuma Jehan da Sadiq suka wuce nemam dillalai.

Babban tashin hankali shine duk wanda su Jehan suka kira dan ya sayi gidan idan ya fahimci kuɗi suke buƙata ruwa a jallo, sai yayiwa gidan kuɗin wulakanci, a wannan karon ba karamin tashin hankali Jehan ta shiga ba, dan abun da take tunani shine mafitar su shima yana neman ya gagara, ga mum kuma kwance rai a hannun Allah kowani lokaci daga yanzu tana iya mutuwa, dan da gaggawa ake buƙatar a mata aiki saboda ciwon yaci jikin ta sosai, dan likitan yace ciwon ya jima a zuciyar ta tun bata kai haka ba, cikin watan nan ne kuma ciwon ya kara tsanan ta saboda tashin hankali da ta shiga na rasuwar daddy da kuma ɓatan Rimsha.

Kamar zararriya haka Jehan ta dawo lokaci guda ta fita hayyacin ta rasa mada fa.

Da kyar suka samu wani ya sai gidan 2 million haka suka sallama masa ya zuba musu kuÉ—in a account É—in mum, haka Jehan taje ta ciro 1.5m misalin karfe 5 na yamma, duk wannan yawon da suke tare da Sadiq suke, haka suka shiga a daidaita sahu suka kama hanyar asibiti dan taje ta É—auki mum su wuce babban hospital, tana rungume da jakar kuÉ—in tana tunanin halin da suke ciki.

A kan hanyar su ta zuwa asibitin ne suka samu accident da wata mota, cikin kwata Jehan ta faÉ—a yayin da shi kuma Sadiq ya faÉ—i can gefen titi, saboda juyin da a daidaita sahun tayi da su, shi ne ta watsar da su, kan kace me jama'a sun taru sai salati suke yayin da shima mai motar da sukayi accident É—in da shi ya sume sakamakon buga kan sa da glass É—in marfin motar da yayi.

Allah ya kiyaye Jehan da Sadiq basu ji ciwo sosai ba, a sukwane Jehan ta miƙe bata damu da kwatar dake jikin taba, ita dai kawai burin ta mum ɗin ta tafita daga haɗari ta samu lafiya.

Kai tsaye bakin hanya ta koma tana neman wani mai a daidaita sahu dan su wuce asibiti, ta ruÉ—e ta manta da jakar kuÉ—in ma, haka Sadiq yazo ya same ta, suka É—an kara gaba da in da sukayi accident É—in suka samu wani abun hawan, zasu hau kenan Sadiq yace mata "Jehan ina kuÉ—in kuma" a sukwane ta juyo, tana faÉ—in "Yana cikin wannan abun da muka hau É—in" a guje Sadiq ya juya ya koma, da sauri ta bi bayan sa.

Ko da suka zo wajen babu jakar, tsab suka duba cikin mashin É—in duk da cewa mashin É—in ma ya faÉ—i dan sai da sukayi juyi biyu kafin mashin É—in ya faÉ—i.
Tsab suka duba cikim mashin ɗin babu komai, a razane Sadiq ya ɗago yana tambayar jama'ar dake wajen, kowa yace masa bai gani ba, mutuwar tsaye Jehan tayi ta kasa motsawa, ta rasa me zatayi, daman ta ciro kuɗin ne a nata tunani dan tana zuwa kawai su wuce babban asibiti ta biya kuɗi kawai a yiwa mum aiki ba sai sun kai gobe ba, a yau zaayiwa mum komai shi yasa tayi sauri ta ciro kuɗin dan kar banki su rufe, gashi a daren nan take son ayiwa mum aiki kuma banki basa aiki da daddare bare tace zata bar kuɗin a bank har sai an buƙata, a takaice dai bata son ɓata lokacin shi yasa ta ciro kuɗin, yanzu gashi wanda ya fisu iya ajiyar kuɗin ya ɗauke,ko in ce mara imani.

Shi ma Sadiq kasa magana yayi dan yasan ba karamin wahala suka shaba, wajen neman kuÉ—in nan, jiki ba kwari ya kariso wajen da Jehan É—in ke tsaye, a hankali yace "Ya Zamuyi" shiru Jehan ta masa dan bata da bakin magana, ganin haka yasa ya riko hannun ta suka hau abin hawan da suka tare suka nufi asibiti, cike da tashin hankali da fargaban abun da zasu gayawa gwaggo.
Chapter 81 · 0% Book details