Sashe 91
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su Aafia kuwa, suna barin wajen kai tsaye wajen wani É—an karamin wajen hutawa dake cikin school É—in suka nufa, waje ne mai É—auke da kujeru wadda aka gina su da siminti, kasan wajen grass ne kanana masu kyau green color. Saman kujerun su Aafia suka je suka zauna, Anisa na bawa Aafia hakuri
Yar dariya Aafia tayi kafin tace "Ba komai kuma idan kika duba ai Amal na da gaskiya, taya za'ayi Man yace wata tana burgesa kuma a gaban budurwar sa wadda yake ikirarin zai aura, duk da cewa basu wani jima da haɗuwa ba, ai hakan bai dace ba" Anisa zata yi magana sai ga Rufee, kasan cewar tasan halin Rufee da masifa, sai tayi shiru kawai suka basar da maganar, zama kusa da su Rufee tayi ba tare da tayi musu magana ba, sai wani kwaɓe fuska take kamar wadda taga kashi.
Shiru suka zauna har Amal ta kariso wajen, Amal na zama wayan nan mayun macizan suka iso, masu karfin dafin bala'i ga idon su nan kamar na mutane, gasu da kattin kai kamar faranti, idan ka gansu kai kace mutane ne saboda ison su, sulalewa sukayi ta cikin grass dake wajen, kai tsaye suka kaiwa Amal sara a kafa, suna saran ta kuma suka ɓace ɓat, ihu Amal ta fasa tare da sulalowa ta zube kasa, kamar an ɗauke wutar nepa tayi tsit, daga wannan ihu ɗayan shikenan bata kara wani ba, ta zama gawa.
A razane su Aafia suka miƙe sukayo kan ta, yayin da shi ma, man ɗin ya kariso wajen a lokacin wai yazo bawa Amal hakuri kamar bai san komai ba.
Aafia na kokarin taɓa Amal Man yayi saurin dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa "A'a Aafia karki taɓa ta!!!" A sukwane dukkan su suka ɗago suna kallon sa...
Share fisabilillah ðŸ‘
To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪
💞Star Lady💞
💞TRIPLET'S💞
💞 FATEEMA MUSA💞
(💞STAR LADY💞)
*GargarÉ—i*
_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba, ko a haɗamun document, ko amin Edit, Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_
WhatsApp me for more information 09162620621
Episode 28
Aafia na kokarin taɓa Amal Man yayi saurin dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa "A'a Aafia karki taɓa ta!!!" A sukwane dukkan su suka ɗago suna kallon sa, cikin sauri ya kariso wajen ya sanya hannun sa ya ɗaba Amal ɗin, shiru bata ko motsi, su Aafia basu sani ba, sanya hannun sannan da yayi, ya kwashe dafin da ke jikin tane, ba dan haka ba suka taɓa ta mutuwa zasu yi suma.
Munafiki nan fa ya sanya musu kukan munafurci yana faɗin "Amal bata numfashi, Amal bata tare da mu, Shikenan munshiga uku" Aafia ta kasa magana ganin abun take kamar mafarki, ita kuwa Rufee ihu ta sa ta duƙa tana girgiza Amal ɗin tana kiran sunan ta, baya baya Anisa ta fara yi tana hawaye, ganin abun ita ma take tamkar a mafarki.
Shikuwa Man yana tsugunne sai kuka suke shi da Rufee, kan kace me jama'a sun taru a wajen, nan fa a ka É—auki Amal a ka wuce da ita Hospital, a in da likita ke tabbatar musu da cizon maciji ne ya kashe ta.
Haka a ka É—auke ta zuwa gida, dan aje a sallace ta a kai ta gidan ta na gaskiya, Aafia tsabar tsorata ta kasa driving na motar ta da kan ta, ta kai kan ta gida, sai dai Anisa ce ta jata zuwa gidan nasu.
Ko da ta shigo palo, a zaune ta samu Aunty tana kallo a Tv, taci kwalliyar ta kamar yadda ta sama tana zaune ta aza kafa É—aya kan É—aya.
Ganin Aafia wata zololo da ita jiki ba kwari ko sallama bata yi ba ta shigo palon, ba karamin ɗagawa Aunty hankali tayi ba, cikin sauri Aunty ta miƙe tsaye tana faɗin "Aafia lafiya meke damun ki" kuka Aafia tasa tare da zama saman sofa, dai dai lokacin Umaisha ta sauko kasa cikin shirin ta zata wuce school, jikin ta na sanye da atamfa ɗinkin doguwar riga A shape ta sanya karamin gyale a kan ta sai kamshi take zubawa.
Da yar gudun ta, ta kariso cikin palon ganin Aafia na kuka, ita kan ta Aunty sai da taji jikin ta ya mutu, yau dai Aafia ke kuka to me ya faru da ita, ita kuwa Aafia kuka take tsakanin ta da Allah kamar yarinya karama, dan ta tsorata sosai shi yasa ma ta kasa zuwa gidan su Rufee É—in, ba zata iya ganin sallar jana'izar Amal ba, hakan yasa ta nemi dawowa gida kawai.
Rungumeta Umaisha tayi tana faɗin "Aunty Afi lafiya meke faruwa?" Cikin kuka da kyar Aafia tace "Umaisha Amal ta mutu, Amal ta mutu Umaisha" zaro ido waje Umaisha tayi cike da tsoro tace "Ban gane Amal ta mutuba, ai na ta mutu ɗin? Ko dai mafarki kike ne?" Kara sautin kuka Aafia tayi tana faɗin "Umaisha da gaske nake wlh Amal ta mutu yanzu nan muna zaune da ita kawai tayi ihu ta faɗi kasa, sai gawa, an kai ta asibiti, dr yace saran maciji ne ya kashe ta, kuma su guyson sun duba ko ina a wajen basu ga snake ɗin ba" salati Aunty tasa tana faɗin "Kiyi hakuri ki mata addu'a ne kinji Aafia" cikin kuka Aafia taje dogon tsaki kasan cewar already Rufee ta shiga tsakanin su da Aunty ɗin kome zata musu ba zasu taɓa ganin farin taɓa.
Miƙewa Aafia tayi ta haye sama ta ci-gaba da kukan ta, ita ma Umaisha saman ta koma dan ta fasa zuwa school ɗin, dan lokaci guda itama tsoro ya kama ta, sai dai gani take kamar Amal bata mutu ba, tana raye, ita dai Aunty addu'ar nemawa Amal Rahma wajen Ubangiji tayi sannan ta koma ta zauna taci gaba da kallon ta, tana mamakin hali irin na su Aafia.
💞JELLY💞
Ba laifi jikin nata ya samu sauki sosai dan har ta farfaɗo, sai dai kuma me ta mance komai she lost her memory, saboda buguwar kai da ta samu, amma likita yace idan ta haɗu da abun da ya taɓa faruwa da ita a baya ko kuma wani da ta sani zata komawa dai dai, yanzu duk wani abun da wannan Hajiya ta tambaye ta sai tace bata sani ba, sai dai kuma still wannan shagwaɓa da bakin surutun nata yana nan bai mutu ba.
Haka dr ya sallame su, suka wuce gidan Hajiyar da Jelly, gida ne babban gida irin na manya manyan atrajirai masu faÉ—a a ji a kasar, mata huÉ—u ne a cikin gidan, gaba É—ayan su suna haÉ—e waje guda, ma'ana ba amusu part part ba, part É—aya a kayi, mai É—auke da katafaren palon kasa, to daga palon kasan ne zaka iya wucewa Part É—in duk wanda kake so, amma duk a cikin palo guda.
Kai tsaye ɓangaren ta Hajiyar nan ta nufa da Jelly, sai kallon gidan Jelly ke yi kamar bata taɓa kallon wani abu makamancin hakan ba, suna shiga ta kai ta wani haɗaɗɗiyar bedroom mai bala'i kyau, yaji komai da ake buƙata.
Sai da ko da ta kai ta zata fita sai Jelly tace bata san wannan ba, ita dai Hajiya bazata fita ta barta ba, sai dai su zauna tare, sosai Hajiya ta lallaɓata tace taje tayi wanka tazo taci abinci, nan fa Hajiya taga ikon Allah dan kuwa Jelly dai ba abun da ta iya ga bala'i shagwaɓar tsiya ,ga bakin surutu kamar reza.
Kuka ta sawa Hajiya kamar yar karamar baby, dama yaya lafiyar kura bare tayi zawo, daman ita Jelly da lafiyar ta ma ya a ka kare da ita bare kuma an samu matsala ta manta komai tayi losing memory ai sai dai abun da hali yayi, sai hakuri kawai.
Haka Hajiya ba dan taso ba ta shiga toilet tayiwa Jelly zan kaÉ—eÉ—iyar budurwa wanka, ita a tunanin ta saboda matsalar da Jelly ta samu ne yasa ta zama haka, bata san cewa dama already jelly kam haka take ba.
Kayan da Nawid ya sai mata lokacin da suke hospital Hajiya ta sanya mata ɗaya daga ciki, sannan ta riƙo hannun ta suka fito palo dan ta zuba mata abinci sai taje itama tayi wanka ta ɗan miƙe.
Koda sukazo palo ta zubawa Jelly abinci tace taci, kafin ta dawo bari tayi wanka, kuka Jelly ta sanya mata tana faÉ—in "A'a ni karki tafi ki barni" Hajiya dai taga abun da yafi karfin ta, tunani ta fara yi karfa Jelly tace da ita zata kwana a É—aki, in ko haka ne shi kuma Abbon Nawid ta kai shi ina kenan, tab lallai a koi babban matsala.
Haka Hajiya ta hakura ta zauna ta fara bawa Jelly abincin a baki, dan Jelly taki yarda taci abincin da hannun ta, wai sai dai a bata a baki, hakako Hajiya ta hakura ta rinƙa bata abaki, jelly na ci tana wasa, dan da alama abincin bashi a kan ta, ba yinwa take ji ba.
💞WASHINGTON DC💞
Zaune Romeo yake kusa da daddy saman bed ɗin dad, hannun sa riƙe da cup da kuma drugs, ya tsare dad da wayan nan dara daran idon nasa, yana jiran dad ya shanye drugs da ya bashi, sai faman kwaɓe fuska dad yake alamar baya son drugs ɗin, daman Romeo yasan halin sa shiyasa yake tasa shi a gaba har sai ya sha a gaban sa sannan yake kyalesa, da kyar da kyar dad ke tura drugs ɗin a bakin sa Romeo na bin masa da ruwa mai sanyi dake cikin kyakkyawan cup ɗin hannun sa.
Babu ko excuse Michael ya faɗo cikin bedroom ɗin yana kwaɓe fuska, ko kallon in da yake Romeo bai yiba, kusa da dad yazo ya zauna yana turo