← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 126

Sashe 39

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihu mai gigita kwakwalwa Zainab ta saki daga cikin Kitchen ɗin, a guje Alhaji ya miƙe ya nufi Kitchen ɗin, kwance ragajab ya iskota a kasa ga jini na zuba daga gakin ta idon ta sun ɗagu sama bakin ciki gaba ɗaya ya bace idon nata ya zama fari zalla, zaro ido waje Alhaji yayi tare da karisawa wajen ta yana ihu yana kiran sunan ta amma ina bata ko motsi, duƙawa yayi yasa hannu yana kokarin ɗaga ta nan take idon ta ya sauya launi zuwa Pink color san man ya sake komawa purple kafin ya koma maroon kamar jini, ihu Alhajin ya fasa sai da Hajiya ta sauko kasa da gudun gaske tana faɗin "Lafiya nake jin Ihu?" A guje Alhaji ya fice daga cikin Kitchen ɗin ya bar gidan ma gaba ɗaya, kamar wani mahaukaci haka ya dawo sai baza babban riga yake a kan titi yana gudu, daga karshe ma cire babban rigar yayi yayi wurgi da ita a kan hanya ya ci gaba da guduwa

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞

*💞TRIPLET'💞

*💞The beginning💞*

*Episode 12*

Ganin abun dake faruwa da Zainab yasa Hajiya ta fasa ihu tayi waje tana kiran mai gadi, da gudu mai gadi ya fito da toilet ba tare da ya É—aure wandon sa ba saboda yasan halin Hajiya da bala'i masifa karta masa wani hukuncin,

a ruɗe ya nufota yana faɗin "Hajiya lafiya" cikin tsawa tace "Kai malam ka ja wandon sama tukun nan" jikin sa sai kerma yake, dai dai lokacin Abba ya danna horn a bakin gate ta waje, a tsorace Hajiya tace "Wayyo Allah Alhaji ya dawo ban gyara gidan ba dama da gaske yake da safe zai shigo gashi na aiki Lami kasuwa Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kaga baba mai gadi karka buɗe masa kofa tukun nan ka bari ina zuwa ka koma toilet ɗin kaji?" Ta kai karshen maganar tare da wucewa da gudu ta koma cikin gida, ta shiga ruɗani ta manta da Zainab dake baje a kasa, tana shiga palo ta hau tattare tattare sharp sharp taje ta jawo kofar kitchen da karfi ta rufo ta wuce ta haye sama sauri sauri ta canza kayan jikin ta ba tare da tayi wanka ba, ta dawo Palo hannun ta riƙe da perfume na jiki, tsabar ruɗewa a tunanin ta air freshener ta ɗauko ashe perfume na jikine, haka ta feshe palon da body perfume nata gudu gudu ta mayar sama ta sauko ta nufi wajen, baba mai gadi yana bayi kamar yadda ta umarce sa bai fito ba, ita da kanta taje ta buɗe wa Abba gate tana faɗin "Sorry yana bayine" sauƙe glass ɗin motar Abba yayi cike da fara'a a face nashi yace "Ai nasan halin sa da yawan shiga toilet shi yasa ma ban damu ba" Abba kyakkywa ne sosai kaman sa ɗaya dasu Imran ba marabe shi suka ɗauko dukkan su, amma Hajiya Umaiya tafi su kyau tsabar kyan ta kamar ita tayi kan ta gata fara tas kamar baturiya,

Kutsa motar cikin gida Abba yayi kai tsaye ya nufi parking space, yana kashe motar ya fito ya rungumi Hajiya Umaiya yana faÉ—in "Umaiya tun da na tafi baki cin abinci sosai ko?" Girgiza masa kai Hajiya tayi kafin tace "In ci mana me ka gani" "Naga kin kara ramewa ne ai kuma kinyi duhu" ya kai karshen maganar tare da jan dogon hancin ta, raba jikin su tayi suka jera zuwa cikin Palo,

lokaci da suka shiga palon sai da mood na Abba ya canza dan shi mutun ne mai bala'i tsab ta ita kuma Umaiya kazama ce lamba ɗaya gashi duk yan aikin da aka kawo mata sai sunki zama saboda mugun tan ta bata da mutunci ko kaɗan ga wulanta ɗan adam ita idan datti zai shekara yana zaune kusa da ita bazata taɓa damuwa da shi ba, ta riga da ta saba, har namiji mai aiki sai da Abba ya kawo a baya amma haka Hajiya Umaiya ta sako mutumin a gaba da kazantar ta ga zagi da cin mutuncin yaga ba zai iya ba ya kama kan sa, yanzu mai aiki ɗaya ce ta rage mata Lami ita kuma kullun kashe ta da aika zuwa kasu Hajiya take dan akoi ta da ciye ciyen kwalama gata da son jiki kamar wata mage.

Ganin face É—in Abba ya sauya ne yasa Hajiya wayan ce masa da cewa "Muje kayi wanka sai muje restaurant mu ci abinci ko?" Jinjina kai kawai yayi dan in da sabo ya saba Umaiya bata girki kullun sai dai suje su sayo abinci shi yasa ta ko ina a gidan ledojin takeaway ne da su kan su takeaway É—in, haka Abba ke hakuri dan yana bala'i kaunar Umaiya fiye da komai a rayuwar sa

"Ina su Imran banji motsin su ba?" Abba ya tambaya yana hawa saman benen, bin bayan sa tayi tana faɗin "Imran ya ɗauki Akil da Akila sun tafi Uk hutawa yace one week zasu yi" ta kai karshen maganar dai dai Abba zai buɗe kofar ɗakin sa, jinjina kai da mamaki yayi lokacin da ya ga cikin bedroom na shi kamar yadda ya tafi ya bari haka ya dawo ya samu yau satin sa ɗaya da yin tafiyar zuwa Abuja amma yadda ya fita ya barɗakin ba wani gyara da a ka masa ga short na shi da ya cire tun ranar da zai tafi ya barshi saman bed bata taɓa ba yana wajen baya jin ma tun da ya tafi Umaiya ta shigo ɗakin, yana ɗaya daga cikin abun da yasa yan aikin ta ke kin zama su gudu sai tace su zasu sanya mata kaya idan tayi wanka ita bata son taɓa komai sai wayar ta kawai wankan ma sai bayan kwana uku uku take

Girgiza kai Abba yayi tare da wucewa ya ajiye yar jakar sa kamar jakar system a saman bed ɗin ya fara ƙoƙarin gyara gadon yana faɗin "Alhaji Mustapha ya kirani ina hanya yace min zai zo shi da Hajiya Zainab su duba jikina waye yace musu bani da lafiya? Ko kece? Na dai am sa musu da to basu kariso bane?" Sai lokacin Hajiya Umaiya ta tuna da zancen Hajiya Zainab dake baje a Kitchen, ihu ta fasa tare da nufar waje da gudu, a razane Abba yabi bayan ta yana faɗin "Umaiya lafiya?" kai tsaye kitchen ta nufa tana salati, Abba na shigowa ya ja birki cike da tashin hankalin suke kallon Hakiya Zainab dake kwance a kasa an kwakwale mata ido dukka biyu ga jini nata malala kamar kogi, san nan an yanke mata nono dukka biyu an cire hancin ta, mutuwar tsaye sukayi shi Abba tsabar tsorata ya kasa karisa shigowa cikin kitchen ɗin, suna tsaye sunyi tsuru tsuru ita kam Hajiya Umaiya ma suman tsaye tayi a wajen,

wani guhuwa me mai karfin gaske ne ya shigo cikin kitchen bakin kirin da shi yana bada sautin kamar wakar shaiÉ—anu aljanu, sun razana ainun sun kasa gaba sun kasa baya ita dai Hajiya Umaiya suman tsaye tayi shi kuma Abba yana ganin meke faruwa amma ya kasa motsawa, yana ganin guguwar nan tazo ta mamaye Hajiya Zainab ta rufe ta ruf na wasu yan mintoci kafin daga bisani guguwar ya mulmule ya zama kamar ball san nan ya fice ta window da ya shigo, guguwar na fita Abba ya duba babu Hajiya Zainab babu labarin ta guguwar ya tafi da ita ko alamar ta babu a wajen jinin ta daya zube ma babu shi a wajen, wajen ya koma clean, tashin hankali ba'a saka maka date yanke jiki Abba yayi ya sume a wajen ita dai Hajiya Umaiya a tsaye ta sume.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Gidan Abbi*

Sosai Abbi ya shiga damuwa gani yake Irfan ba zai samu aiki ba kasan cewar yadda kasar ta zama yanzu, jiki a mace ya É—auki waya ya kira dillalan da suka taya company 7 millon a kan suzo su saya kawai su bashi kuÉ—in ya fara wani business kafin su Irfan su dawo dan yasan idan Irfan na nan ba zai bari ya sayar ba shi yasa ya sallama musu shi tun kafin Irfan ya dawo an gama komai.

Cikin kankanin lokaci dillalan suka zo kofar gidan Abbi, cike da rashin jin daɗi Abbi yace su shigo, ba musu suka shigo su biyu hannun su riƙe da jaka baka mai yar girma kaɗan, kai tsaye palo Abbi ya wuce da su, bayan sun zauna, har da ruwa Abbi ya kawo musu suka amsa suka sha san nan suka gaisa,

bayan sun gama gaisawa ne Abbi yake sanar da su a kan su kawo 7 millon ɗin ya sallama musu company, ɗaya daga cikin sune yace "Alhaji ae yanzu ba zamu iya sayan wan nan kangon 7m ba aa ya mana tsada 5m shine last abun da zamu iya saye idan ka sayar mana" shiru Abbi yayi ya kasa magana saboda ɓacin rai, ɗaya daga cikin dillalan ne ya sake cewa "Alhaji ka sayar ne ko baka sayar mana ba mu tashi muyi tafiyar mu" kamar daga sama a bakin kofar shigowa suka ji an ce ba'a sayar ba kuma ba za'a sayar ba ku tashi ku fice daga gidan nan" a sukwane suka juyo ciki har da Abbi dan ganin wanene,

wani matashi ne tsaye a bakin kofar shigowar hannun sa riƙe da katuwar jaka jikin sa na sanye da riga baki da wandon jeans blue ya daura rigar sanyi mai hula ya kuma sanya hular rigar a hansa baka iya ganin face nashi sosai, a yanayin jikin sa dai ba zai wuci 25 years ba,

Ganin dillalan basu tashi bane yasa ya daka musu tsawa yana faɗin "Bazaku tashi bane?" Cikin sauri ɗaya daga cikin su yace "Alhaji mun saya 7 millon ɗin ga kuɗin bamu takardun mu tafi da shi" a fusace matashin nan yace "Wan nan fillin bazaa sayar ba ku fice daga gidan nan tun kan ranku ya ɓaci" jiki ba kwari suka wuce sumui sumui suka fice daga palon suka bar gidan
Chapter 39 · 0% Book details