← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 126

Sashe 15

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ɗin ba da zarar yayi kan kice me zaki ga viewers sama da 1 million kamar jira suke hmmm wan nan ma ba kowa ya taɓa kallon face ɗin TGA ba kina leƙa comments section na Johnson zaki ga jama'a suna faɗin handsome of the world ba mata kaɗai ba har maza faɗe suke kuma fa ba fuskar sa suka gani ba dan na faɗa miki kullun da facemark yake yawo ba abun da zaki gani sai idon sa light ash ɗin nan mai kyalli kamar madubi shima idon time to time yake zama ba glass amma a haka jama'a ke mutuwar son sa musamman hausawan mu sai kiji suna faɗin wan nan anya ba aljani ba kuwa dan kyan sa ya wuci ɗan adam tun ma basu karisa kallon ainihin kyan face nashi ba" shiru Amal tayi ta zubawa Aafia ido har ta kai karshen maganar san nan tace mata "Dan Allah Aafia nuna min wan nan The general of the army nan in ganshi dai yau kam cikin sauri Aafia ta ɗauko wayar ta, ta shiga gallery sauri sauri ta fito da video Tga jikin ta har rawa yake tace zo ki kallesa a gidan Tv a na hira da shi duk da ya sanya face mark zo kiga asalin kyau shi fa ko a cikin turawa ma number 1 yake" ta kai karshen maganar tare da miƙa wa Amal wayar ta da sauri Amal ta ansa wayar ta fara kallon kyakkyawa Bature ne zaune saman wata haɗaɗiyar kujera mai matukar kyau da laushi face na shi sanye da face mark baki sai dara daran idanun sa kamar ball masu kyalli kamar glass kasan cewar kwayar idon nasa light ash ne, zubawa surar jikin sa ido Amal tayi yana da murɗaɗen jiki sosai ga faffaɗar kirjin kamar wani zaki duk da yana sanye cikin kaya ya ɗaura jaket mai matukar kyau da tsada a saman kayan na shi hakan bai hana faffaɗar kirjin sa bayyana ba, sau uku Amal na mai da video daga farko tana sake kalla ganin Amal bata da niyar dai na kallon TGA ne ya sanya Aafia ta anshe wayar ta tana faɗin "Ke ni bani karkije kiyi mafarkin sa" waro ido waje Amal tayi tana faɗin "Dan girman Allah Afi ki turamin duk wani videos nasa da kike da shi kuma ki faɗa min sunan account da ake posting na shi a tik tok da kuma gidan Tv dake News a kan sa time to time ɗin kinji?" Ta kai karshen maganar cikkin sigar rarrashi ba musu Aafia ta tura mata video TGA da take da shi dukka ta WhatsApp san nan ta an sa wayar ta tayi searching account ɗin Johnson tayi followed na sa sai murna Amal take da farinciki da haka sukayi sallama dan time ya tafi sosai Aafia da Umaisha suka wuce wajen motocin su kowa ta shiga nata Aafia na kokarin kunna motar ta Rufee ta kariso wajen da yar gudun ta tana kiran sunan Aafia sauke glass ɗin motar Aafia tayi tana faɗin "Lafiya Rufee kika yi wan nan gudun haka?" Girgiza kai Rufee tayi kafin tace "A'a ba lafiya ba daman ina son in ɗan tambaye ki kuɗi ne ɗazun sai na manta sai yanzu na tuna" jinjina kai Aafia tayi kafin ta ciro kuɗi daga jakar ta ta kirga 10k ta miƙa wa Rufee tana faɗin "Ban da sayan kayan haɗin shisha" Ansa Rufee tayi tana faɗin "In Sha Allah abu mai mahimmanci zan saya" tada mota Aafia tayi ba tare da ta sake yiwa Rufee magana ba ta figi motar ta bar wajen da gudu already ita Umaisha ta jima da tafiya Aafia na barin wajen Rufee tayi tsaki kana tace "Yar wahala uwar muce ke da zaki rinƙa hana mu shan shisha kema In Sha Allah sai na koya miki ba shan shisha kawai ba har da sha kwayoyi da bin maza sai kin koya sai na lalata miki rayuwa san nan na auri uban ki na mori dukiya duk na koreku daga gidan kin ɗauka a banza nake saki kike wa matar baban ki abun da kike matan nan ne yarinya dan kawai ki fitar min da ita ne ni kuma na shiga dan banson zama da kishiya wawayen yara kawai" ta kai karshen maganar nata tare da juyawa tana kaɗa 10k da Aafia ta bata tana murmushi ta bar wajen ta koma cikin department na su.
Chapter 15 · 0% Book details