← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 126

Sashe 40

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan dillalan sun tafi ne matashin ya kariso cikin palon ya zauna saman sofa dake fuskantar na Abbi san nan ya buɗe jakar da ya zo da ita "Bawan Allah waye kai? Me ya kawo ka gidana" cewar Abbi, shiru saurayin yayi bai tanka Abbi ba har ya gama buɗe jakar ya ciro wasu takardu guda biyu ya miƙawa Abbi yana faɗin "Irfan ya shirya next week zai wuce London *UNITED KINGDOM* karatun master's nashi su kuma Aafia da Umaima ance na canza musu makaranta, kuma na canza ɗayan takardan nasu ne na canza musu school, san nan wan nan kuɗin 100 million ne akace na kawo maka ka tayar da company ka san nan idan kana da wata buƙata a kace ka faɗa min" ya kai karshen maganar tare da ɗago kai ya zubawa Abbi ido yana jiran yaji ko Abbi na da wata buƙata "bawan Allah waye ya aiko ka?" Abbi yayi maganar cikin sanyin murya "No Alhaji wan nan bai shafeka ba kawai dai kafaɗamin idan kana da wata damuwar dan zan wuce aiki na ya kare" shiru Abbi ya ɗanyi kafin yace "Bani da ita amma zan so sanin wanda ya aiko ka da kuma kuɗin zuwa kwanana nawa ko sati nawa zan biya" rufe jakar saurayin yayi tare da ɗauka ya ajiye kusa da Abbi saman sofa, ya juya ya nufi hanyar fita yana faɗin "Bawan Allah ne ya baka kuma ba ya baka dan ka mayar bane no kyauta ne daga Allah sauran bayani a kan karatun Irfan a Uk yana cikin aljihun jakar nabarka lafiya" ya kai karshen maganar tare ficewa daga palon ya bar gidan gaba ɗaya,

shi dai Abbi a tsorace yake jiki na rawa ya buɗe aljihun jakar dan yaga sauran takardun Irfan ɗin, nan ya ci karo da wata farar takarda mai ɗauke da sako later warware takardan yayi ya fara karantawa kamar haka "Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu ɗan uwana barka dai fatan kana lafiya ina maka fatan alkhari da fatan gamawa da duniya lafiya, nasan zakaji tsoron an san kuɗin nan shi yasa na haɗa maka da wan nan takardan, karkaji tsoro ka ansa kuɗin mallakin kane na baka har abada idan ma kana baƙatan kari zai iya karoma, yasu Aafia na canza musu school Masha Allah naga result na Aafia tayi kokari jamb ɗin ta yayi kyau tana da ilimi sosai ni ta ɗauko ashe, ita ma Umaisha ba laifi tana kokari ranar Monday Irfan zai iya wucewa Uk an gama shirya masa komai yaje yayi master degree ɗin sa ka gaida min da yarana idan sun dawo kasa musu Albarka, sako daga Hussain" zubur Abbi ya miƙe yana faɗin "Hussain daman Hussain yana raye? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun haba ɗan uwana me yasa zaka mana haka zuciya bata da amfani in dai har zaka iya sanin halin da nake ciki ka kawomin ɗauki to nasan zaka iya jin abun da nake faɗa yanzu ma dan Allah Hussain ka dawo garemu shakara 18 fa kenan rabon mu da kai zuciya bata da amfani karka biyewa zuciya kadawo mu haɗe kan mu, mu ci-gaba da yiwa iyayen mu addu'a, saboda ni da Maik zaka dawo ba dan yaya ba karka duba abun da yaya ya maka a baya ka ki dawowa dan Allah ka dawo mu muna son ka ai" ya kai karshen maganar tare da komawa ya zauna ya fara fitar da abubuwan cikin jakar wai ko zai samu address ɗin Hussain,

har ya kammala fito da komai na jakar babu komai sai wayan nan kuÉ—in da takardun sai kwalayen wayoyi kirar I phone 13 guda uku ko wani waya an rubuta sunan mai shi a jikin kwalin Umaisha Aafia Irfan, haka Abbi ya tattara komai ya mai da cikin jakar, yayi farinciki sosai ya kuma yi bakin ciki sosai yana bala'i son ganin Hussain amma ba dama tunda bai san in da zai same su ba,

kwashe komai yayi ya mai da ya ɗauki jakar kuɗin ya fito dan ya tafi banki, nan ya ci karo da sabbin masu gadi ga wasu matasa tsaye a harabar gidan yasha mamaki sosai a tuanin sa ɓarayi ne har yafara kiran sunan Allah daya karesa,

ɗaya daga cikin matasan ne ya kariso in da yake cikin girmamawa ya gaida shi san nan ya ɗaura da ciwa an ce suzo su rushe wasu ɓangarori daga gidan nan su gyara ginin san nan su kara gina abubuwan da babu, cikin sauri Abbi yace "Waye ya turoku?" A tunanin sa kila sun san address ɗin wadda ya aiko su, amma sai yaji akasin haka domin kuwa suma a waya a ka kirasu a ka basu wan nan aikin basu san daga in da a ka kira su ba, wucewa Abbi ya yi rai a ɗan ɓace ya nufi yar motar Irfan yana faɗin "Kuyi aikin ku" cikin sauri suka fara aikin su shi kuma Abbi ya shiga motar Irfan ya tayar ya nufi gate, tun bai kariso ba wani jibgegen mai gadin da aka kawo masa sabo yazo ya buɗe masa gate ɗin ya kutsa motar waje ya nufi bank su kuma masu aiki suka fara aikin su.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*KANO*

Zaune daddyn Jelly yake cikin katafaren office na shi na Engineer dake company nin sa filman Nigeria limited sai murmushi yake yana murna a kan aikin nan da suka samu dan ba karamin aiki bane contract ne na billions of Naira,
da sallama P.A ɗin sa ta shigo hannun ta ɗauƙe da kyakkyawan plate mai ɗauke da Tea da snacks, har kasa ta duƙa ta gaida shi sai murmushi yake ya amsa mata gaisuwar san nan ta miƙe ta ajiye masa plate ɗin a saman table ɗin ta fice daga office ɗin tana yaba kyan hali irin na daddy, cikin nitsuwa daddy ya ɗauka tea ɗin ya fara sha ya ture snacks ɗin gefe dan bai jin yinwa sosai kawai ma dan ya saba shan tea ɗin ne idan yazo office amma ban da haka yau baya jin yinwa dan yayi breakfast dasu Irfan kafin su fito tare shi ya wuto office su kuma suka tafi ganin gari a kan da yamma zasu biyo masa su koma gida tare, bai karisa shan tea ɗin ba barci ya ɗauke sa a wajen yana zaune.

After some hours

Da kyar daddy ya iya buɗe manya manyan idanun sa da suka masa nauyi, da kyar ya iya waro su waje ya sauke su saman katafaren agogon bangon dake manne a bangon ɗakin sa dake cikin office ɗin, zubur ya miƙe tare da goge idon sa yana kallon time ɗin da kyau 4:45 pm, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shi abun da kawai yake iya furtawa mamaki yake yaushe yayi barci haka shi da yake zaune yake shan tea lokacin kuma 10:00 am me ya faru da shi haka? Haka ya zauna yana jerowa kan sa tambayoyin da bashi da amsar su

jiki ba kwari ya yunkura zai miƙe a sukwane ya koma ya zauna ganin jikin sa babu kaya innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya faɗa tare da kara waro idon sa waje sai yanzu ma ya lura ashe a cikin bedroom na shi na cikin office ɗin yake, yasha ruwan mamakin waye ya cire masa kaya gaba ɗaya haka, wai mekeke faruwa ne ya kai karshen maganar tare da miƙewa a fusace ya fara sanya kayan sa dan yaje ya tambayi P.A dan ba wadda ya isa ya shigo office na shi ba tare da sanin ta ba,

Bayan ya gama sanya kayan sa tsab da tunani fal ransa ya nufi waje yana jan kafa da kyar da kyar dan gaba É—aya jikin sa ya masa nauyi,

Haka ya fito daga office É—in gaba É—aya ya nufi wajen P.A, turus ya tsaya ganin office nata wayan babu komai har desktop computer ta babu a wajen, ta kwashe komai ta tafi, ganin haka yasa daddy ya fahimci a koi wani abu a kasa akoi makarkashi ya, cikin sauri ya juya ya koma cikin office na shi ya É—auko wayar sa dan ya kira P.A É—in,

nan yaci karo da saƙo guda biyu ɗaya na P.A ɗaya kuma na Baban Muneer wato Alhaji Auwal abokin takarar sa sun turo masa, jikin sa har kerma yake wajen buɗe sakon baban Muneer,

yana shiga sai yaga video ne cikin tsumuwa ya buɗe video, wata iriyar mahaukaciyar yarazana yayi lokacin da idon sa ya sauka kan Video, har sai da wayar tasa ta faɗin ƙasa a wajen, kasa motsawa yayi ya kurawa wayar ido yana kallon ta dan koda wayar ma ta faɗi kasa bata ɗauke ba video nayi, tashin hankali kwance daddy yake saman gado sa na cikin bedroom ɗin office ɗin kwance yake jikin sa ba kaya shi da P.A, abun da ya kara rikitashi shi ne gashi kuma ba barci yake ba a video idon sa biyu suke sheke ayar su sai dai shi ya kasa tuna lokacin da a kayi hakan a video dai gashi nan ita P.A tana nuna bata so shi kuma yana tilasta mata, dogon salati yasa muryan sa har rawa take ya durkushe kasa a wajen nan take hawaye wani na bin wani suka fara bin kuncin sa, ganin abun yake tamkar a mafarki, a hankali ya buɗe bakin sa muryan sa na kerma yana kuka yace "Ina saurayi matashi ma ban yi zina ba sai yanzu why why P.A zaki min haka Alhaji Auwal kacuci rayuwata ka gama da ni Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" yana cikin surutan da yake, kiran Alhaji Auwal ya shigo wayar nasa, cikin sauri jikin sa har ɓari yake wajen ɗaukan wayar tare da yin picking na call ɗin,
Chapter 40 · 0% Book details