Sashe 47
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Michael na zaune sai rokan sa Dest da Test suke amma bai kula su ba, da suka dame sa sai ya miƙe a fusace ya fara jibgan Dest kamar an aiko sa, fuskar nan tasa kamar hadari, gaba ɗaya student dake wajen sun tsorata dan basu taɓa ganin Michael ya daki Dest ba, yanzu tsawon shekara 5 kenan suna tare basu taɓa ganin wani abu makamancin haka a tsakanin su ba.
Dest kuwa ganin Michael zai iya yi masa illa ne yasa ya miƙe da gudu ya nufi hanyar fita daga community garden ɗin, da sauri Michael ya damko kafar sa ya jawo sa, ya sanya kafa ya take masa wuya ga kafar nasa sanye suke cikin Booth na yan kwallo masu karfin nan, haka ya takewa Dest wuya ya zaro belt ɗin wandon sa ya fara zabgawa Dest ta ko ina a jikin sa, sai zaro ido waje Dest yake dan numfashin sa na gab da ɗauke wa baya mumfashi da kyau saboda take masa wuya da Michael yayi, da gudu Test yazo ya duƙa ya riƙe kafar Michael ɗin yana kuka yana bashi hakuri karya kashe masa ɗan uwa, ina Michael yayi nisa baya jin Test, kawai saukewa Dest belt nashi yake ta ko ina a jiki kamar wani zararre ga belt ɗin na shin da tauri sosai, duk ya fashewa Dest jiki, duk da hakan kuma bai kyalesa ba gashi kuma ya take masa wuya
gaba ɗaya student dake wajen sun tsorata sosai sun san halin Michael da zuciya amma basu taɓa ganin sa cikin ɓacin rai har haka ba, su kansu Lucky da Winston sai haushi suke suna goga kan su a jikin Michael ɗin kamar suna dannan sa yayi hakuri.
A wan nan halin James ya iso ya same su, cikin nitsuwa ta baya ya anshe belt É—in da Michael ke zane Dest da shi, a fusace Michael ya juyo dan ganin wani isasshene ya anshe belt, yana juyowa karaf idon sa ya sauka kan James dake tsaye fuskar sa babu alamar wasa ko kaÉ—an, ganin haka yasa Michael cire kafar sa daga wuyar Dest ya koma saman sofa ya zauna yana huci kamar wani zaki, kallon jama'ar dake wajen James yayi kafin ya dawo da kallon sa kan Micheal "John Take him to *(HUHS) Harvard University Health Services*" yayi maganar tare da muna Dest dake ta kokarin bawa kan shi mumfashi, ma'ana yana kokarin jawo mumfashi sa ya saitata, da sauri John da Test suka É—auki Dest É—in suka wuce da shi HUHS, da sauri matar Dest da kawar ta suka bi bayan su
kallon tsab James ya yiwa Michael kafin yace "did he offend you?" Shiru Michael yayi sai huci yake kamar mayin wacin zaki "am I not talking to you?" James ya sake jefo masa tambaya, yayi maganar yana karasowa wajen sa, cikin fushi da tsawa Micheal yace "Why zai kawo min wancan banzan abun na shi a nan?" "Which Abu?" James ya tambaya da mamaki a face na shi "Matar sa mana" Michael ya bashi amsa, girgiza kai James yayi kafin yace "Wajen ka matar tazo?" Miƙe wa tsaye Michael yayi cikin fushi ya fara magana "Ba waje na tazo ba kuma bata isa tazo waje na ba amma ai yasan bana son hakan, bana son wayan nan azzaluman su raɓeni" zuba masa ido James yayi har sai da ya kai karshen maganar tasa san nan yace "Why kake haɗe mata dukka kace basu da kirki This is not good, ya kamata ka sani mummy daban suma sauran daban kamar dai yadda muke ɗin nan", gigitatchiyar tsawa Micheal ya daga masa a fusace yace "Stop James, stop talking about that human hare, she's not my mother at all, i came this world true my dad only, i hate that human i hate her more than your expectations, i don't have any mother in my life!!!"
Kasa da murya James yayi cikin muryan rarrashi ya fara magana "I knew it Michael, i know you hate mum and I, and i hate her because she had done bad thing to us, but this is not the reason, da zaka ce you hate all ladies in this world" dogon tsaki Michael yaja tare da komawa ya zauna yana faÉ—in "I hate all ladies I don't want to see tham close to me" shiru James ya É—an yi kafin yace "Okey I agreed, know let's go back home i want to see you there, I want us to be discuss something" yayi maganar cikin sanyin murya
Tsaki Michael yaja kafin ya miƙe ya fice daga wajen rai a matuƙar ɓace, bayan sa James yabi yana mai matukar jin tsanar mum na su a ransa na karuwa.
Da sauri Copper Winston Lucky suka bi bayan su, sai mamaki student dake wajen suke
Kowa motar sa ya shige, kamar yadda suka saba haka lucky ya shiga gidan gaba Copper da Winston suka shiga gidan baya na motar Micheal, James na tsaye sai da yaga motar Micheal ta miƙi shinfiɗaɗiyar titin fita daga School ɗin san nan, shi ma ya tada motar sa yabi bayan Michael ɗin.
________________________________
*KADUNA*
Unguwar Malali
Kwance Umaisha take saman gadon su dake bedroom na su, tayi nisa cikin tunanin a kan Akil, while ita kuma Aafia tana ta fama da shirya kayan ta cikin drawer sanya kayan su, wayar Umaisha dake gefen ta ya fara kara alamar shigowar kira, sai da gaban ta ya bada dukan uku uku, tun ma bata ga mai kiran na taba,
cikin sauri jikin ta har kerma yake ta ɗauko wayar, My pleasure shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin, mamaki ne ya kamata wato shi Akil har suna ya zaɓawa kansa yayi saving number sa da shi, dan tana da tabbacin shine duk da bai taɓa kiran taba sai yau ɗin, ta san shi ɗin ne dan bayan shi bawan da ya taɓa mata waya, ko Aafia taki ɗaukar wayar dan tsoron Akil ɗin,
My pleasure ta mai mai ta sunan, cike da fargaba ta ɗauki kiran tare da manna wayar a kunnen ta, cikin sanyi murya tace "Assalamu alaikum" daga ɗayan ɓangaren Akil yace "Waalaikumussalam" "In wuni yaya Akil" tayi maganar cikin girmamawa "Me ya same ki?" Ya tambaya da ɗan tsawa, murya na kerma tace "Babu komai" "zaki faɗa min me ya same ki ne kosai na tashi na ɗauki mota nazo na same ki" kallon time tayi 11 na dare kuma ta san halin sa zai aikata, hakan yasa tace "Kayi hakuri zan faɗa maka" shiru yayi yana sauraron ta "Daman a kan School ne naji kace kar na sake fita ko ina kuma wlh ina bala'i son nayi karatu" ta kai karshen maganar kamar za tayi kuka "Ni kin ji nace kar kiyi karatu ne?" Cikin sauri ta girgiza kai kamar tana gaban sa, "A'a yaya Akil" "Kin iya mota?" da sauri tace "A'a ban iya ba" "Wan can dirty brother ɗin naki fa ya iya ne?" Gyaɗa masa kai tayi kamar a gaban sa tana faɗin "Eh ya iya" "Good zan sanya a kawo muku mota guda biyu ke ɗaya sister ki ɗaya sai ya koya muku ko?" Kasa ta kara yi da murya a nitse cikin fargabar abun da zai je yazo tace "Yaya Akil ka bar shi mun gode" wani gigitatchiyar tsawa ya daka mata wadda ya sa har wayar hannun ta ya kusa faɗuwa "Ke har kin isa in ce abu kuma kice na bari? To gobe da safe ina zuwa gidan, kai yanzu ma gani nan zuwa sai ki kalli cikin ido na ki faɗa min ko?"
Kallon Aafia dake tsaye ta Zuba mata ido Umaisha tayi, kamar zata yi kuka tace "I'm sorry yaya Akil ba zan sake ba, sai ka kawo motar muna godiya Allah ya kara arziki" dogon tsaki yaja tare da kashe kiran sa, ajiye wayar Umaisha tayi tare da sakin kuka mai tsuma rai,
haurowa saman gadon Aafia tayi tana faɗin "Ya isa haka Umaisha kiyi shiru" rungume Aafia tayi cikin kuka tace "Aunty Aafia wai shi kam wani irin mutun ne yaya Akil ɗin nan? Kullun cikin masifa da faɗa bashi da hakuri ga zafin rai" Aafia na kokarin magana wayar Umaisha ta kuma yin kara, a kule ta furta "Wai har da wani sawa number sa my pleasure, to yana sanin farincikin ne?" Ta kai karshen maganar tare da ɗaukan kiran ta kara wayar a kunnen ta tana faɗin "Hello" daga ɗayan ɓangaren Akil yace "Daman nasan kuka kike ai shi yasa na sake kira, bana hana ki kuka ba? Me yasa bakyaji ne? Tun yanzu kike yin abubuwan da na hana ki ko? Kina son ki ɓata min rai kenan ko?" Mamakin sa ne ya kara kama Umaisha wai shi wan nan wani irin mutun ne, ji yadda yake wani Magana kamar ba shi ya sanya ni kukan ba,
"Ba dake nake magana bane?" Cikin sauri tace "Kayi hakuri" "Aikin ku kenan sai kun yiwa mutun abu ku rinƙa bashi hakuri kuna cutar sa, to dai ki shirya gobe za'a kawo muku motocin guda biyu discussion continue and continue continue, ki ɗauki karamin ki barwa sister ki babban ku rinƙa zuwa school, zuwa gaba zan canza muku motar kina jina?" Da sauri tace "Eh muna godiya sosai da sosai" "Idan kinje School babu ruwan ki da kowa, karatu kawai nace kije kiyi, idan kika kuskura nasami labarin kina kula wani ba sai nayi magana ba kin san me zai biyo baya, san nan ina son ki mai da hankalin ga karatun sosai dan ni ina son wayayyiyar mace wadda tayi karatu sosai Allah ya ba da Sa'a" yana kai karshen maganar ba tare da ya jira amsar taba ya katse kiran