Sashe 35
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy ya fito ɗauke da ita a saman kafaɗar sa ya naɗo ta a towel mai laushi sai murmushi take, kai tsaye saman chair ɗin gaban mirror ya ɗaura ta tare da ɗauko karamin towel ya goge mata jiki tsab, san nan ya fara shafa mata lotion nata masu kamshi da daɗi da tsada, bayan ya kammala ya shafa mata mayukan gashin ta masu kyau da tsada ya gyara mata gashin ya feshe ta da perfume masu bala'i kyau da kamshi, san nan ya sauƙo da ita kasa ya wuce ya nufi drawer sanya kayan su ya ɗauko mata wani dankareren blouse gown ja mai manya manyan flowers fari daga ta kasan rigar, rigar kasan ta a buɗe yake kamar umbrella, san nan ya haɗo mata da pant, ya dawo bakin gadon, ba tare da ya mata magana ba ya fara sanya mata pant ɗin, bayan ya gama sai ya sanya mata rigar a wuyar ta yana kokarin sanya mata hannu tayi sauri cirewa tana faɗin "Daddy baka samin wan nan abun da nagani a film matan suna sawa ba" tayi maganar cikin shagwaɓa cikin nuna ko in cula yace "Wani abu kenan?" Hannu tasa saman kirjin ta tana faɗin "that thing that looks like ball a kirji naga suke sawa and then the thing is big" sai lokacin daddy ya gane breziya take nufi hakan yasa yaja dogon tsaki a kule yace "Sai kin girma" kuka ta sa masa tana faɗin "Ni yanzu ma na girma ai, kuma da suka sa suma sunyi kyau ni kasa min nima nayi kyau" dafe kai daddy yayi yana nadamar barin ta ma da yake tana kallo India film, ganin yayi shiru ya kyaleta ne yasa ta fasa masa ihu tana kokarin sauka daga gadon, cikin sauri ya riƙota cikin muryan rarrashi ya fara magana "To ai my Jelly baki da abun sai naje Shopping sai in sawo miki yanzu dai kisa rigar ki karsu yaya Imran suzo su ganki haka, kuma kinga har da su Umaisha yaya yace min zasuzo, ko so kike su fiki kyau ne?" Cikin sauri ta girgiza masa kai tana faɗin "A'a daddy banson su fini kyau" da murmushi a kan face na shi yace "Yauwa my Jelly to kisa kayan naki idan ba haka ba zasu fiki kyau" ya kai karshen maganar tare da sanya mata rigar, ba musu ta tsaya ya sanya mata tsab ya riƙo hannun ta yana faɗin "Muje kasa na baki abinci" maƙe masa kafaɗa tayi cikin shagwaɓa tace "Daddy what about make up fa? Baka min ba ai" girgiza kai kawai yayi tare da sakin hannun ta ya koma gaban mirror ya ɗauko lipstick da powder da kwalli yana tafiya yana tunanin ya za'ayi kwalliyar tayi kyau dan wancan karon ma daya mata kwalliyar kamar dodo ta zama, haka dai ya karisa wajen ta da tunani fal ransa gefen ta ya zauna ya fara shafa mata powder, sai murmushi take, shiko sai rawa hannun sa keyi, sosai ya lapka mata powder a face nata kafin ya ɗauko kwalli ya sanya mata, a mai mai kon yasa mata kwallin a cikin ido sai ya sanya mata a kasan ido dan gani yake kamar zai tsole mata ido idan ya sanya mata a cikin ido, kamar wata matsafiya haka ta dawo haka ya labka mata lipstick ja a baki har ma gefe da gefen bakin, nan take bakin nata ya kara girma, shi kan shi ya tsorata da kallon ta amma ba yadda ya iya da ita, yana kokarin miƙewa tayi saurin cewar "Daddy baka sanya min a saman gerata ba, a na sawa a wajen ma mummy'n su hudan School na mu tana sa musu" ba musu ya koma ya fara zana mata lapka lapkan gera yana tunanin waye zai samu ya koya masa yadda ake wa mace make up dan ya rinƙa sanya Jelly farinciki dan tana bala'i son make up musamman idan taga friends nata a School iyayen su sun musu sai ta yi ta damun sa sai ya mata, da wan nan tunani ya kammala mata make up ɗin, kamar wata aljana haka ta dawo ya zana mata gerar lapla lapka har kusa da ido ga shi sama da kasa ya zana mata gerar, ɗaya yayi kasa ɗaya yayi sama, ita kuwa sai washe baki take tana dariya, cikin sauri ya kawar da kan sa dan idan tayi dariya kamar boka ko wani katon mummunar aljani take dawowa, haka ya kama hannun ta ya ɗau wayar sa suka fice palo
Ko da sukaje palo sai kallon ta su Zuwaira suke, sun kasa gane ta sun san dai ba wadda daddy zai riƙo haka in ba jelly ba,
kallon sama da kasa tayiwa su Zuwaira kafin tace "Ku idan mutun yasha make up sai kuyi ta kare masa kallo to ni karku kwashe min kyan make up na yaya Imran nayiwa duk wadda ta sake kallo na sai na kwakwale idon ta" cikin sauri suka yi kasa da kai shi kuwa daddy ko ajikin sa ya ja hannun ta suka wuce saman table, Nana tazo tayi serving nasu suka fara cin abinci, idan tana taunar abincin kai kace rakumi ne ke cin abinci saboda yadda daddy ya lapka mata lipstick a baki, sai kau da kai daddy yake bai son ganin ta a wan nan yanayi ita kuwa sai murmushi take tayi make up.
👹DAULAR MUTUWA👹
Ruwan sama mai karfi ne ya ɓarke a dajin a firgice yan sanda da suka suma suka farfaɗo, tare da fara ihu mai tarwatsa kwakwalwan ɗan adam, a sukwane suka bazama cikin dajin basu san in da suka dosa ba kwata kwata gudu kawai suke sun rarraba hanya kowa ya kama nashi hanya,
Abun da ya basu mamaki ya kara ɗaure musu kai sai kawai ganin su sukayi dukkan su a cikin asalin *Daular mutuwa* a ruɗe suka tsaya suna zazzare ido kamar ɓera a tarko, suna tsaye suna waige waige suna karewa gidan kallon, sai ganin wasu jibga jibgan wasu halitta masu kama da shanun daji wayo ɓauna amma sai dai wayan nan sunfi ɓauna girma jibga jibgan gaske ne wadda zasu kai girman giwa, a guje wayan nan halittu sukayi kan yan sandan nan alama a yin wace suke, kafin yan sandan suyi wani yunkuri wayan nan halittun sun farmusu, sun fara yin kaca kaca da naman jikin su suna gurnani kamar wasu mayin watan zakuna,
tas suka cinye yan san dan nan ko kashi basu bari ba har jinin da ya zuba a kasa sai da suka lashe tas, san nan suka girgiza jikin su tare da sakin wata mahaukaciyar ihu mai tarwatsa kwakwalwan ɗan adam san nan suka riƙiɗe suka zama mutane matasa kyawawa kamar larabawa, suka wuce suka shige wani ɗaki mai kama da keji.
💞💞💞💞💞💞💞💞
*KANO*
Da sallma su Irfan suka shigo palon, daddy da Jelly suna zaune saman sofa suna buga game a system É—in daddy, daman kullun idan daddy ba zai je office ba sai ya zauna ya kunna musu game É—in kwallo suyita bugawa tare, Jelly ta iya buga game É—in kwallo sosai, wani lokaci ma har winning É—in daddy take,
Jin sallama yasa ta ɗago ido ta kalli bakin kofar da kwalliyan ta kamar boka, ganin su Imran ne yasa ta miƙe a guje tana ihu ta nufi Imran, ta faɗa jikin sa tana dariya, ba tare da ya lura da face nata ba ya ɗaga ta sama yana faɗin "Oyoyo rabin rai na" yayi maganar yana kokarin zama saman sofa, dai dai lokacin idon sa ya sauka kan face ɗin ta, ihu ya saki tare da sauke ta daga jikin sa yana faɗin "Wace ce ke? Wa innahu min sulaimanu wa innahu bismillahi rahmanin rahim ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba bappa wace ce wan nan?" Saboda dariya Irfan har da faɗuwa kasa yayi, dan duk da bai san face ɗin Jelly ba ya fahimci ita ɗin ce tasha make up dan Irfan yana da ƙwaƙwalwa sosai ga dogon tunani, Aafia Umaisha Akila Dukka sai dariya suke ban da Akil da face na shi a ɗaure kamar hadari
AKILA
kanwar Imran ce itace autar su yanzu haka tana da 15 years kamar Umaisha, kyakkyawa ce sosai irin ta É—aya da Imran.
Akil
Matashin saurayi ne mai jini a jiki kanin Imran ne shima daga Imran sai shi a yanzu yana da 22 years while Imran nada 28 years dukkan su kamannin su É—aya sai dai shi Akil farine tas, da yake family su daddy ruwa biyu ne fari da chocolate.
Shi kan shi daddy sai da dariya ta kubce masa, ita kuwa Jelly cikin shagwaɓa tace "Yaya Imran me ya faru?" Miƙewa tsaye Imran yayi ya fasa zama a kujerar cikin tsoro yace "Bappa wallahi muryan ta irin na Jelly ce, dan Allah ina Jelly ta me ya kawo aljana gidan nan" yayi maganar yana kallon daddy, kashe masa ido ɗaya daddy yayi kafin yace "Kai Imran yanzu sai da ka bari kyan baby Jelly ya rikitaka dama na faɗa mata sai tafi kowa kyau, na faɗa mata bazaku gane ta ba dan kyau ɗin da kwalliyar ya mata" sai lokacin Imran ya gane matsalar komawa yayi ya zauna tare da jawota jikin sa yana faɗin "Kai baby Jelly duniyar kyau, irin wan nan kyau ai dole ki rikita yaya Imran kaiii chanchaɗi" kallon gefen ido daddy yayi wa su Irfan nan take suka tsaya da dariyar dan kar jelly ta hassala, cike da farinciki suka kariso suka zazzauna saman sofa tare da ɗagawa daddy gaisuwa, cikin hanzari su Nana suka zo suka ɗauka musu trolley's dasu ka zo da shi,