← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 126

Sashe 24

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Washegari da safe daddy ya sha ruwan mamaki ganin yau jelly ita da kan ta tayi wanka tun kafin ya dawo sallar asuba ta tashi ta yi wanka ta shirya cikin uniform nata riga fari da wando ash da ɗan karamin farin hijabi zuwa kirji, hakan ba karamin mamaki ya ba wa daddy ba dan bata taɓa kwatatan ta hakan ba, amma sai ya ɓoye mamakin sa ya yaba mata sosai sai dariya take fararen hakoran tannan sai kyalli suke, wucewa shi ma yayi ya je yayi wanka, ko da ya fito bata ɗakin ta fice palo sauri sauri ya shirya cikin suit sannan ya ɗauki jakar computer sa da wayar sa ya duba time 7:02 sauri sauri ya fito zaune ya iskota saman sofa tana ta murmushi kamar ba ita ba a wan nan karon daddy ya kasa ɓoye mamakin sa yace "My baby what is happening ne?" Miƙewa tayi ta rungume sa tana faɗin "My daddy I want you to be happy everyday that's why" rungume ta yayi kawai amma bai yarda da maganar ta ba dan yasan halinta sarai, kafin ya sake ta yana faɗin "Muje muyi breakfast mu tafi kar lokaci ya kure" ba musu ta bishi suka zauna saman kujerar table, Nana tazo tayi serving na su sauri sauri suka yi breakfast, bayan sun gama daddy ya riko hannun ta suka nufi waje, suka je suka shiga mota gidan baya idi driver ya shiga gidan gaba ma zaunin driver yayiwa motar key suka bar gidan, a bakin gate na school na su suka tsai da motar daddy ya juyo ya kalle ta yace "Yau ba zamu shigar da ke ciki ba nayi late sauka ki shi ga school ina kallon ki" ba musu ta sauka daga motar da murmushi tace "Daddy na, ina kaunar ka sosai ka kula min da kan ka sannan kayi min alkawari ba zaka sake kuka ba komai zai faru da ni" daddy bai kawo komai a ransa ba yace "Na miki alkawari my baby ba zan sake kuka ba" sako kan ta tayi ta glass ɗin motar ta manna masa kiss a kumatu bata jira reply na shi ba ta wuce da sauri saboda hawaye da ya gangaro mata, zuba mata ido daddy yayi yana kallon ta, ya sha ruwan mamaki ganin yau bata juyo ta masa bye bye ba saɓanin kullun da take juyowa wani lokaci ma tafiyar baya baya take tana kallon sa, ganin su daddy basu tada mota bane yasa ta fahimci daddy na kallon ta dan haka sai ta kara sauri ta shige cikin school, tana shiga school Idi driver ya tada motar suka bar wajen sai mamaki daddy yake nan take yaji jikin sa ya mutu gaban sa na faɗuwa, haka ya daure dan bai kawo komai a ran sa ba har suka isa office na shi,

Ita kuwa jelly tana laɓe a wajen gate sai da taji motar su daddy ya bar wajen tayi Sa'a mai gadin ya zaga bayan gida su daddy na tafiya ta fito da sauri ta kariso bakin hanya ta tari abun hawa ta hau tana sauke ajiyar zuciya "Ina zan kai ki?" Mai mashin ɗin ya tambaye ta cikin sauri tace masa "In da ake hawa mota" ɗan juyowa yayi ya kalle ta kafin yace "Motar zuwa ina?" Sai lokacin ta tuna ita bata ma san a wani gari gidan su yaya Imran yake ba shiru tayi tana tunanin hiran da suka yi a baya da Imran "Motar zuwa ina nace?" Mai mashin ɗin ya sake gefo mata tambaya nan ta tuna last zuwan yaya Imran yace mata daga Kaduna ya fito da ta tambaye sa daga ina ya fito tuna haka yasa cikin sauri tace wa mai mashin ɗin "Motar zuwa Kaduna" ba tare da ya sake magana ba ya buga mashin ɗin sa suka nufi park sai sauke ajiyar zuciya take,
Ko da suka isa bai sauke ta ba sai da ya kai ta har wajen motocin Kaduna tayi Sa'a kuwa motar saura mutun ɗaya ya tashi, mai mashin ɗin yace "Kawo kuɗi na biya miki kuɗin mota" ba musu ta sauke jakar school dake bayan ta, ta zaro dollar dubu ɗaya tana faɗin "Nawane kuɗin?" Waro ido waje mai mashin yayi yana kallon kuɗin dake hannun ta nan take jikin sa ya fara rawa kasa kasa yayi da murya yace "Ki mai da kuɗin nan idan kina da kuɗin Nigeria ki kawo" miƙa masa dollar tayi tana faɗin "To kai riƙe na baka dan kana da kirki ina da kuɗin Nigeria" ta kai karshen maganar tare da sanya dayan hannun ta ta zaro dubu dubu guda biyar ba musu mai mashin ɗin ya ansa dollar da ta bashi ya mata godiya san nan ya ansa 5k da ta ciro ya sauka ya biya mata kuɗin motar zuwa Kaduna ya mata sallama tare da bata canjin ta ya wuce, shi kan sa driver ya sha ruwan mamaki ganin yarinya kamar jelly tazo hawa mota hakan yasa ya tambaye ta ina zata je dan ya tabbatar tana cikin hayyacin ta yarinya 14 years, cikin sauri ta sanar da shi Kaduna zata je da mamaki a face na shi na jin tana cikin hayyacin ta haka a ka loda kayan passengers a bayan mota, driver ya shiga kowani passenger ya shiga mazaunin sa jelly ta zauna kusa da wata tsohuwa mota ta tashi zuwa Kaduna.

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai

💋Star Lady💋

*💞TRIPLET'S💞*

💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞

STAR 🌟 LADY..✍️

*💋The beginning💋*

Episode 7

💞💞💞💞💞💞💞💞

*3 years back*

*Abuja*

*7:10 am*
Chapter 24 · 0% Book details