← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 126

Sashe 97

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf ne ya fara taɓa su yana kokarin tashin su daga barci, shi kam Sadiq saboda tausayi ya kasa, kawar da kan sa ma gefe guda yayi yana hawaye, shi kuwa Sha'aban daman bai shigo ɗakin ba ya tsaya a Palo, dan kar baban Sadiq ya gansu, su uku ya fara zargin ko dai sune ba aljanu ba.

A firgice baban Sadiq da amarya suka tashi suna salati, dan a tunanin su ma ɓarayi ne, Sabon torchlight da Jehan ta bawa Sadiq kuɗi suka sawo, shi su ka dannawa baban su da amarya hasken a fuska, ga torchlight ɗin da bala'i haske kasan cewar saboda ne.

Sadiq ya kasa magana Yusuf ne ya shaƙe murya kamar aljanin gaske ya fara magana "Kai dattijo wajen ka mukazo" nan fa baban Sadiq ya fara salati yana kiran sunan Allah, ita ma amarya sai salati take tana zazzare ido, dan tsoro kamar zata saki fitsari a wando, har wani zufan hawala suke fitarwa, Sadiq ji yake kamar zai yi musu kuka, shi kam Yusuf dama ogane a zafin rai da rashin kunya dan haka ko a jikin sa, ya fara jerowa baban sa kashedi kala kala, sai amsa masa baban sa yake cike da girmamawa jikin su sai kerma yake, daga karshe Yusuf ya rufe da cewa yu aljanun Jehan ne wlh idan basu fita har kan Jehan ba sai sun dawo sun kashe su, daman Jehan ne tace musu suce haka idan sun zo tafiya, ai kuwa dai baba da amarya suka rinƙa basu hakuri, Yusuf yace musu su kwanta su rufe ido kar su kuskura su motsa sai da safe zasu tashi idan ba haka ba zasu shanye musu jini ko kuma su shanye musu kafafu su dai na tafiya, duk wanna zancen da Yusuf keyi Jehan ta bashi kalaman ta daura sa kan hanya.

Babu musu Baban Sadiq da amarya suka yi abun da Yusuf yace, gashi Sadiq ya dalle musu fuska da hasken torchlight basa iya ganin komai.
Sadiq ne ya tsaya yana haske musu ido har sai da su Yusuf suka haye saman celin suka sauka ta waje, sanan shima ya kashe hasken torchlight ɗin ya salallaɓa a cikin duhu yaje ya haye suka sauka ta baya.

Bayan sun sauka ne suka mai da cilin É—in suka É—an chogana shi suka wuce É—akin su kirjin su sai dukan uku uku yake suna addu'ar Allah yasa kar baban su ya gane su ne ba aljanu ba, ita kuwa Jehan ta É—aura su a kan hanya tana can tana sharara barci ta cikin kwanciyar hankali, dan yanzu ta samu peace of mind tun da za'ayi wa mum aiki, damuwa ya ragun mata sosai ta fara farinciki, amma ba kamar abaya ba.

Washegari bayan sun fito, Jehan ta shirya tsab cikin doguwar riga Abaya pink color za su wuce asibiti da Sadiq, daga nan Sadiq ya kai ta taga restaurant ɗin da zatayi aiki dan gobe Monday zata fara aiki a can, amma still fake face ne a fuskarta, dan tun da ta sawo fake face ɗin nan take yawo da shi ko ina bata taɓa cirewa, mutanen anguwa sunyi magana har sun gaji, sai tambayar ina rayinyar nan Jehan take suke yi, ko dai ta koma garin sune sai dai ba mai basu amsa.

A tsakar gida za su fita Sadiq da Jehan suka isko amarya, ko sannu basu ce mata zasu wuce amarya tayi saurin cewa "Sannun ku da fitowa" a sukwane Sadiq ya kalli Jehan, kashe ma shi ido ɗaya Jehan tayi suka wuce basu tanka amarya ba, sai da suka fita wajen Jehan tace "Karamar mara kunya, da Jehan yar sanda mai zaman kanta kike, wlh tsab zan gyara miki zama a gidan nan" cike da mamaki Sadiq yace "Jehan dan Allah shekarun ki nawa" "I'm close to 16 years" ta bashi amsa, mai mai ta wa yayi a ransa yarinya 16 years da wanna irin kwakwalwa da confidence haka abun da mamaki wlh, duk wani makirci da iya shege Jehan ta san shi, sai dai alhadulillah tana da ilimin addini kuma duk abun da zata yi bata saɓa dokan Allah, tana kokarin kiyaye wa.

Kai tsaye Hospital suka wuce, mum dai tana nan jiya iyau kullun sai dai a sanya mata ruwa, amma bata fargaÉ—o ba.

Zaune suka isko gwaggo saman kujerar da mai jinya ke zama, gaishe da gwaggo Sadiq yayi tare da tambayar ya jikin mum, "jiki da sauki" gwaggo ta bashi amsa, wucewa yayi ya nufi waje yana wa mum addu'ar Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗun ta, a tare gwaggo da Jehan suka amsa da ameen, Jehan ta dubi gwaggo tace "My gwaggo what do you want to eat?" Shiru gwaggo ta ɗan yi kafin tace "duk abun da ya samu" sallama Jehan ta musu sanna ta fito ta samu Sadiq a waje tace suje restaurant ɗin da zata fara aikin sai ta saiwa gwaggo abinci a can, ba musu Sadiq ya miƙe suka tafi zuwa wajen asibitin bakin hanya su samu abun hawa.

Taxi suka tara suka shiga, suka tafi restaurant É—in,

Tun daga bakin bakin gate É—in tampatsetsen restaurant É—in Jehan ta fara, yiwa wajen kallon sama da kasa, Sadiq ya lura da hakan sai yace "Jehan lafiya kike kallon wajen haka" guntu tsaki taja kafin tace "Dirty place" tayi maganar dai dai lokacin da suka karasa cikin restaurant É—in, nan fa Jehan ta fara yiwa ma'aikatan dake wajen kallon raini kallon yan datti, da fara'a Ibraheem ya tarbe su yana washe baki, kara É—aure fuska sosai Jehan tayi wai dan kar su raina ta, shi dai Sadiq idan da sabo ya saba da halin Jehan É—in sa.

Jagora Ibraheem ya musu zuwa ya nunnuna musu abubuwan da ya dace Jehan ta sani, duk in da ta wuce sai ma'aikatan wajen sun mata sannu da zuwa, amma babu wanda tayiwa kallon mutunci ma bare ta amsa masa gaisuwar sa.

Abun da ya bata mamaki shi ne wasu É—akuna da Ibraheem ya nufa da su, ashe restaurant É—in haÉ—e yake da hotel ta ciki ita bata sani ba, tab lallai a koi cakwakiya.

Bata damu ba suka shiga ko ina Ibraheem ya nuna musu sannan suka dawo wajen reception, Jehan ta saiwa gwaggo shinkafa da miya steew aka mata takeaway.

Zasu tafi Ibraheem ya kawo mata rigar da wando nasu na aiki, kallon kayan tayi a wulakance, riga blue da wando baki, a takaice tace "For what?" Sai faman murmushi Ibraheem yake yace "uniform work, shi zaki rinƙa sawa idan zaki zo aiki" ɗaure fuska tayi sosai tace "Kayan da zan sa nazo ma kune zaku zaɓa min?" Ba tare da nuna damuwa ba Ibraheem yace "A'a Hajiya Jehan haka tsarin yake, abun da oga yace shi a keyi a nan" tirkashi kallon sama da kasa tayiwa Ibraheem kafin tace "Au sayata kukayi gaba ɗaya kenan?" Shiru Ibraheem yayi dan bashi da amsan tambayar nan nata

ganin Jehan zata jiƙa musu aiki yasa Sadiq ya ansa kayan daga hannun Ibraheem yana faɗin "Ba komai malam Ibraheem, karka damu zata sanya, sai goben idan tazo" ya kai karshen maganar tare da juyowa ya kalli Jehan yace "Jehan muje ko, zanje gareji kin ga kuma rana nayi" ba musu ta wuce gaba yabi bayan ta, Ibraheem dai zuba musu ido yayi yana kallon Jehan kamar ya make ta yaji dan haushi, yar karama da ita sai iya shege.

A wanna karon abun hawa daban daban suka hau, dan Sadiq zai wuce gareji ita kuma hospital, ba yadda Sadiq bai yi da Jehan ba a kan ta amsa kayan uniform nata amma taki, ta kafe tace sam ita ba zata ansa ba, dan babu wanda ya isa ya zaɓa mata kayan da zata sanya in zata fita, haka Sadiq ya wuce da kayan garejin su ita kuma ta wuce hospital, daman haka suke kullun, idan Sadiq yazo ya gai da su gwaggo sai ya wuce gareji sai yamma idan zai koma gida sai yazo ya ɗauke ta su koma tare.

Tirgashi akoi fa cakwakiya Jehan dai tace bazata sanya uniform ba, wanna shine wasa farin girki, mu leƙo Washington DC mu dawo.

💞WASHINGTON DC💞

12:30Am

kamar kullum duniya dukka sun yi barci, shi kuwa yana zaune saman table chair na dining table na kasa yana latsa system, jikin sa na sanye da bathrobe fara kal kamar yanzu ya fito da ita a ledar ta, gata da laushi tilis kamar audiga, kasan cewar gaban rigar a buɗe hakan ya bayyanar da kyakkyawar lallausan dark black gashin mai tsantsi kwance a saman faffaɗar kirjin, gwanin ban sha'awa dan sai kwalli gashin yake kamar ya shafa mata baby oil, gashin hannayen sa da na kafafun sannan duk suna kwance lup a jikin sa, kasan cewar gashin dark black ne shi kuma fatar sa farane kal hakan yasa gashin bayyana sosai, ya tara dark black curly hair sa ya ɗaure a baya, ya bar wannan na gaban goshin nasa ta karawa face nasa kyau over, yau ma kamar kullun sky blue light ne kunne a palon, hasken wutar ba karamin kyau tayi ba a kan face nasa, ya zubawa system nasa dake saman table wanyan nan dara daran blue eyes ɗin nan nasa masu ɗaukan hankali, kasan cewar ya sauke idon nasa kasa kaɗan yana kallon system ɗin, hakan yasa, zara zaran eyelashes nasa suka kara bayyana dan idon nasa yayi kamar a rufe, yayi shiru yana ɗan cizan red lips nasa nan, kamar mai tunanin wani abu, ya kafe system da ido, ga jibga jibgan bodyguard na su a tsai tsaiye suna jiran yace abinci su bashi tissue ya goge bakin sa, already kamar kullun sun zuba masa duk wani abun da zai buƙata.
Chapter 97 · 0% Book details