← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 126

Sashe 56

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da daddy ya koma palo duk sun gama cin abinci sun watse kowa ya wuce bedroom na shi, yana kokarin wucewa ya haura sama, James ya sauƙo, shirye yake cikin wani ɗan iskan crazy jeans baki sai t-shirt fara tas, ya zuba gold chain a wuya, ya sanya wata haɗaɗiyar Booth a kafar sa baƙa kalar wandon sa a kafar sa, daman shi gashin kan sa bai da tsawo sosai, ba ta kai ya tara ya ɗaure ba dan haka sai ya barta zube kawai, tasha gyara sosai, sai kamshi yake zubawa, kai da gani kasan wan nan wani waje mai mahimmanci a gare sa zai je,

"Where are you going James?" daddy ya tambaya yana duba time a jikin agogon hannun sa, 09:30 pm, a ta kai ce James yace "Party" yayi maganar tare da wucewa da sauri, yana kokarin ciro wayar sa daga aljihun wandon sa, hoton da ogan su ya turo masa a waya ta faÉ—o, dan yaje ya wanke hoton ya mai da ta na cati, É—aukan hoton daddy yayi ya zubawa hoton ido yana kallon face É—in Romeo sanye da face mask "what are you going to do with this pic James?" a sukwane James ya juyo tare da dawowa ya ansa hoton ya nufi hanyar fita yana faÉ—in "is it not my blood brother picture?" Shiru daddy yayi ya haura sama abun sa bai kawo komai a ran sa ba, shi kuma James ya wuce ya fice daga palon ya nufi parking space.

Sauri sauri ya É—auko motar sa ya fice dan kar Romeo ya tambaye sa ina zai je.

Yana fita kai tsaye *Flash dancing club* (gidan rawa) ya nufa, sai da ya kusa isa wajen san nan ya tsai da motar sa a bakin titi ya cire kayan da ya sako daga gida, ya sanya nasu na yan ta'adda, wato irin kayan mai kama da na yakin nan mai É—auke da wukaken ko ta kwana a jikin su, haka ya shirya tsab a kan titi ya cire duk wasu chain da ya sanya a wuya da hannun sa, ya bar agogon su kawai, san nan yasa face mask dan kar wanda ya san shi ya gane sa yazo ya faÉ—a wa daddy da Romeo.

Yana gama shiri ya ja motar sa ya wuce club ɗin, yana parking a parking space na su ya fito ya shige ciki, kai tsaye wani keɓaɓɓen ɗaki ya wuce,
a nan ya isko wasu fafaren Indiyawa suna jiran sa, zama yayi a saman kujerar dake wajen suka fara tattaunawa a kan abun da ya tarasu,

Good 3 hours suka ɗauka suna tattaunawa kafin daga karshe James ya miƙe ya nufi wani ɗan karami kofa dake wajen ya buɗe ya shige, suna zaune suna jiran sa.

Jim kaɗan ya dawo hannun sa ɗauke da wata jaka yazo ya miƙa musu san nan ya basu hannu sukayi musabaha tare da yin sallama, ya wuce ya fice daga wajen ya nufi motar sa.

A wan nan karon ma yana fita daga club É—in ya É—an yi tafiya kaÉ—an ya tsaya ya sauya kayan jikin sa ya mai da wanda ya fito da su daga gida, ya shirya tsab kamar yadda ya fito daga gida san nan ya wuce ya nufi gida.

Yana shiga gate na biyu tayi scanning na shi san nan ya wuce parking space, lokacin karfe É—aya sau ra minti 20 na dare.

Ko da yayi parking na motar ya fito sai ya fara lallaɓawa a hankali kamar mara gaskiya, musamman ma da ya shigo palon kasa, a hankali yake sanya kafar sa a floor ɗin dan kar wani yaji takun sahun sa.

Kamar daga sama yaji zazzakar voice an ce "where are you coming from?" A razane ya É—ago kan sa sama, dan ta saman kan sa yaji voice É—in, ganin Romeo tsaye a saman benen a bakin kofar shi ga part na shi ne yasa James sauke nauyayyar ajiyar zuciya a hankali, cike da tsoro yace "from my friend party" shiru Romeo ya masa tare da tsare sa da dara daran kyawawan blue eyes na shi, sanye yake cikin kayan barci riga da dogon wando farare kal masu laushi da kyau da tsada, kayan sun zauna a jikin sa sun anshe sa sosai kamar dan shi a kayi su, a wan nan karon ma a koi face mask a face na shi, dan shi idan ba barci zai yi ba baya rabuwa da face mask dan bai son jama'a su iya tantance face na shi, bai son su iya gane banbancin sa da TGA, dan kwarai suna kama amma suna da ban ban ci ta abu huÉ—u kawai, wan nan dalilin yasa bai son cire face mask É—in, har ya saba abun ya zame masa jiki, ya zamo idan bai sanya face mask ba ma baya jin daÉ—i.

Da wan nan daddaÉ—ar sexy voice É—in nasa mai kwantar da hankalin mai sauraro cikin nitsuwa yace "From today i forbide any body in this house going to party anymore" cikin girmamawa da rawan jiki James yace "Okey bro" sai kerma irin na marasa gaskiya jikin sa ke yi, duk a ruÉ—e yake, sai zufa yake duk da sanyin Ac dake ta shi a palon kirjin sa sai dukan uku uku yake, tsabar tsoro har kan sa na sara masa kamar zai fashe.

Juyawa Romeo yayi cikin nitsuwa ya taka ya koma cikin part na shi, ba tare da ya sake yiwa James magana ba, da sauri James ya haura sama har yana haÉ—awa da gudu, kallon É—aya zaka masa a wan nan yanayin da yake ciki kaga asalin mara gaskiya, yana shiga bedroom na shi ya faÉ—a saman gadon sa ko takalman kafar sa bai cire ba kirjin sa sai dukan uku uku take, yana murna da ya samu ya kubcewa Romeo, dan yasan ba dan dare bane yanzu da sai Romeo ya kama shi sai ya gano shi, saboda Romeo a koi shi da kaifin kwakwalwa da basira, ga saurin gane abu, ba'a banza yake The general of the army gaba É—aya ba.
Saboda tsorata da James yayi da kyar barci ta É—auke sa ko takalmin kafar sa bai cire ba bare aje ga zancen wanka da sa kayan barci, ya tsorata sosai dan ya san halin Romeo bai da wasa, kana wargi kaÉ—an zai kama ka.

*NIGERIA,*

*ABUJA*

Wasa wasa zazzaɓi ne mai zafi ya rufe Rimsha tana rubgume da zanen da tayi na GAR haka mum ta shigo ta same ta, a tsorace ta kira daddy, lokacin already ya dawo yana gida, yana zuwa ya taɓa jikin ta zafi kamar wuta, hannu yasa yana kokarin ansan zanen da ta rungume, cikin magagin barci da zafin zazzaɓi ta fara sambatu ta kankame zanen sosai tana faɗin "Jehan dan Allah ki kyale min zane na daddy ya hanani kallon GAR a Tv yanzu zanen kawai ya rage min duk wani video sa dake wayata zan goge dan ba zan iya kin bin maganar daddy ba, dan Allah ki kyalemin zanena idan kika ansa Allah zan iya mutuwa, ni GAR yana matuƙar burgeni dan Allah ki kyaleni"

Cike da tashin hankali daddy ya ɗago ya kalli mum wadda ita ma shi take kallon, tashin sense ja da baya kaɗan yayi murya kasa kasa yace "Munyi kuskure, mun yi kuskure tun farko da muka bar Rimsha tana kallon wan nan kafurin yanzu saboda na hanata kallon shi ne har zazzaɓi ya kamata, innalillahi wa inna ilaihir rajiun tab ɗi jam a koi matsala" matsowa Mum tayi ta dafa sa tana faɗin "To yanzu me mafita?" Girgiza kai yayi yana faɗin "Mafita shi ne mu kyaleta ta ci-gaba da kallon sa, a hankali mu raba ta da shi, idan muka ce zamu raba ta da kallon sa lokaci guda zata iya cutuwa kin dai ga alama yanzu to, ba zai yiwu mu ce lokacin guda ta dai na kallon sa ba, idan mukayi hakan mun zalunce ta, kuskure dai mun riga mun yi sai dai mu kiyayi gaba ki san yadda zaki yi kina zare mata abun a ranta a hankali hankali har ta rabu da abun dukka, yanzu zai wuce da ita hospital kome yake ciki zamuyi waya" ya kai karshen maganar tare da komawa wajen ya duƙa ya sameta cak a kafaɗar sa suka nufi waje sai sambatu take ga jikin ta zafi kamar wuta

jiki a mace mum tabi bayan su ta wuce bedroom nata, while gwaggo da Jehan kuma suna É—akin gwaggo basu san meke faruwa ba, ita ma mum tazo dubasu ne ta samu Rimsha cikin wan nan hali.

Kai tsaye hospital daddy ya wuce da ita, suna zuwa a ka anshe ta hannu bibbiyu, a ka fara bata taimakon gaggawa, shi kuma daddy sai yawo yake a bayan A&E yana tunanin mafita.

*KADUNA*

zaune suke gaba É—ayan su suna hira while Imran yana aikin latsar waya yana kallon hotunan Jelly,

cikin natsuwa Abba ya fara magana "Imran yaushe zaka koma school?" Ɗagowa Imran yayi daga kallon wayar nasa da yake cikin girmamawa yace "Next week zan koma" jinjina kai Abba yayi kafin yace "Kai kuma fa Akil?" "Tare zamu wuce da Yaya Imran In Sha Allah sai mu rabu a Germany ya wuce nima na wuce namu School ɗin" Abba na kokarin yin magana Akila ta rigasa cikin shagwaɓa tace "Abba dan Allah nima zan bi yaya Imran, na gaji da karatu a Nigeria" Shafa kan ta Abba yayi tare da jawota jikin sa yana faɗin "Ba komai heartbeat zaki je amma ba yanzu ba sai kin kammala secondary ki san nan kije kiyi jami'a a can" kara lafewa tayi jikin Abba tana mai kaunar iyayen ta da yan uwan ta, Akila kenan heartbeat na kowa dake cikin gidan, har da masu bawa flowers ruwa da mai gadi duk kaunar ta suke, kowa son ta yake, ba iya gidan ba duk wan da ya zauna da ita sai ya so ta saboda kyan halinta da kaunan jama'a ba ruwan ta da rigima ga girmama mutane, tana son zaman lafiya, ga fara'a kowa na tane
Chapter 56 · 0% Book details