← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 126

Sashe 80

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace Tga ya dawo cikin palon tare da sojoji biyu jibga jibga masu jini a jika, kai tsaye mutumin Tga ya nuna musu yana faɗin "carry this man out from this house" kallon sojojin James yayi suna kokarin ɗaukan mutumin cikin tsawa James yace "Are you mad, get out from here!!!" Cikin fushi Tga yace da sojojin "i said take this dirty man out" kafe su da ido James yayi kafin yace "Okey carry him let me see" shiru sojojin suka tsaya sun rasa maganar wa za su bi, dan duk wanda suka karyawa doka to zasu rasa aikin su, Tga ogan sune a wajen aiki, while shi kuma James sanyin idanniyar ogan kowa a gidan ne wato Romeo, sun gwammaci suki bin umarnin ogan su wato tga a kan su ɓatawa James rai dan gwara musu hukuncin Tga a kan na Romeo, dan haka sai suka juya suka fice daga palon dan sun san halin Romeo a kan yan uwansa sam baya adalci kuma zai iya yin komai a kan Triplets ɗin sa.

Ganin sojojin sun juya sun fice ne yasa Tga ya nufo mutumin da kan sa da nufi ya ɗauke sa ya fitar da shi, yana kai hannun sa zai ɗauki mutumin, a fusace James ya damki hannun nasa tare da turesa gefe guda, rai a matukar ɓace Tga yayi kan James da nufin dukan sa, nan fa James yace bai isa ba, kamar wasu zakuna haka suka fara faɗa.

Da karfi Tga ya kaiwa James duka a gefen ciki wadda hakan ya masa mugun zafi sosai, lokacin guda James ya sauya idon sa sukayi jawur nan fa ya riƙiɗe ya zama tamkar mayinwa cin zaki wadda yayi shekara biyu babu abinci ya fito farauta, nan yafara farauta Tga, a fusace ya sanya dukkan karfin sa ya ɗaga Tga yayi wurgi da shi gefe saman glass table na tsakiyar sofa milk color, nan take table ɗin ta tarwatse, gadan gadan James ya haye kan Tga ya fara kai masa bugu ta ko ina yana gurnanin ɓacin rai, ran maza ya ɓaci gaba ɗaya jijiyoyin kan sa dana wuyar sa sun miƙe sai dukan Tga yake sosai, da dai yaga duka da hannun ma bata masa ba sai ya ɗamko wuyar rigar Tga ɗin ya miƙar da shi tsaye, yana kokarin kai masa naushi a ciki, Tga ya riƙe hannun sa tare da kwashe kafafun James ɗin ya zube kasa, nan fa Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka shima

Kasan cewar James ya samu horon faÉ—a sosai wajen ogannin sa, hakan yasa ya san dabarun faÉ—a sosai, cikin dabara ya juyar da Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka.

kamar wasu mayinwatan zakuna haka suka rinƙa farautar junan su, sai dai Tga yaci karfin James, dan shi horon soja ya samu daga wajen Romeo, hakan yasa yayiwa James duka duk ya farfashe masa jiki da fuska, da kyar James ke mumfashi, amma Tga idon sa ya rufe duka kawai yake kai masa ta ko ina.

Zuciya ta jasa yana neman kashe James ba tare da ya sani ba.

Kamar daga sama yaji an riƙe hannun sa ta baya, yana kokarin juyowa, a fusace Romeo ya murɗe masa hannun da karfi ta baya tare da ɗaga sa sama daga kan James ɗin yayi wurgi da shi gefe, idon Tga ya rufe baya ji baya gani, bai san waye yayi wurgi da shi ba, a fusace ya taso ya nufi Romeo dan idon sa James yake gane masa, Romeo na tsaye, fuskar nan a ɗaure tamau kamar bai san menene dariya ba, dara daran blue eyes na san nan sun sauya zuwa ja saboda dukan James da Tga yayi, har wani tsuma jikin sa keyi, yau da Tga ba kanin daddy bane da ba abun da zai hana ya kashe shi, amma duk da haka dole ya basa hukunci mai tsanani, shi kuwa Tga idon sa ya rufe gadan gadan ya iso wajen Rome yana kokarin kaiwa Romeo duka a ciki, cak Romeo ya riƙe hannun sa tare da kai masa wawan bugu a ciki wadda ta sanya sai da ya fasa ihu mai sauti, bai kai ga gama ihun ba, Romeo ya sake ɗaga sa sama yayi wurgi da shi saman sofa, wadda sai da ya sanya ya fara dawo cikin hayyacin sa, karisawa wajen sa Romeo yayi rai a matuƙar ɓace ya ɗamko wuyar sa ya miƙar da shi tsaye, ya tsake masa wuyar tasa, nan fa Tga yaji kamshin mutuwa, cikin fitar hayyaci yasa hannu yana kokarin cire hannun Romeo daga wuyar sa amma ina ya kasa koda motsa hannun Romeo ɗin, sai faman zaro ido waje yake, Yana kokarin tantance wa idon sa ke gane masa, shin abun da ya gani da gaske ne, shin Romeo ne ko gizo ne, bai kai ga iya tantance wa ba

Romeo yasa kyakkyawar kafar sa ya taka shi da karfi a kirjin sa wadda sai da ya saki ihu mai ranaza kwakwalwa, tamko wuyar sa Romeo ya sake yi ya kai masa duka a ciki wadda sai da tasa shi dawowa cikin hayyacin sa da kyau, dan yasan ba mai karfin yi masa irin wannan damka da dukan duk gidan sai Romeo.

Kwashe kafafun sa Romeo yayi nan take Tga ya zube kasa kan gwiwowin sa, rai a ɓace Romeo ya sanya kyakkyawar farin hannu sa ya ɗamko gashin kansa Tga ɗin ya ɗago kan nasa sama suna fiskantar juna, zuba masa dara daran blue eyes nasa nan Romeo yayi yana kallon face nashi kamar mai tunanin wani abu.

Sai galabaitaciyar kukan wahala Tga yake, murya na sarkewa da kyar ya iya faÉ—in "I'm sorry lion" shiru Romeo yayi kamar bai ji saba, yayin da shi kuma James ke kwance kasa yana numfashin da kyar da kyar, ga fuskar sa nan duk Tga ya fashe masa sai jini yake, abun ku da fatar turawa ba quality sosai ba kamar bakar fata ba, fatar su bata jure wuya ko kaÉ—an.

Jin hayaniya yasa su daddy saukowa kasa, ganin abun dake faruwa yasa suka kariso cikin palon da yar gudun su, cike da tashin hankali a fuskokin su, kuka Michael yasa ya duka kasa yana bawa Romeo hakuri, dan yasan halin Romeo sarai duk yadda yake son sunnan idan suka ɓata masa rai ya zuciya to dukan mutuwa yake musu, gashi kuma da alama yaji haushin abun da Tga ɗin yayiwa James sosai, dan da alama ya ɗan ɓata rai ka ɗan, shiyasa ma ya murɗe wa Tga ɗin hannu kuma ya dake sa har sai da ya zube kan gwiwowin sa, kwata kwata Michael baya son yaga suna samun matsala da juna.

Su kuwa su daddy sai godiya suke dan yau Romeo bai É—auki zafi sosai ba, da ya É—au zafi yadda Tga ya bugi James ai da yanzu wani zance ake.

Ganin yadda Romeo ya É—agawa Tga wuya sama sosai ne, gashi kuma Tga na shan wahala wajen jan numfashi, hakan yasa murya na rawa daddy ya kariso wajen ya É—an tsaya daga É—an baya, cike da kaunar Æ´aÆ´an nasa yace "Please my lion leave him" shiru Romeo ya musu yana ta kallon face É—in Tga kamar mai karantar wani abu

daddy zai sake magana, Romeo ya dakatar da shi ta hanyar É—aga masa hannu alamar bai son jin wata magana kuma, shiru daddy yayi ya koma gefe ya tsaya
jin kukan Michael ya fara yin yawa ne kuma gashi Michael yana da matsala yasa Romeo ya juyo da dara daran blue eyes nasa kan fiskar Michael É—in, a hankali ya saki gashin kan Tga É—in tare da nunawa Michael hanyar bedroom nasa da hannu ba tare da yayi magana ba, dan bai son Michael ya shiga damuwa, kuma yasan halin sa sarai yanzu zai sa kan sa cikin damuwa,

matsowa Michael yayi da rarrafe ya kariso gaban Romeo yana faÉ—in "Please lion for giv....bai kai karshen maganar ba, Romeo ya daka masa wata gigitatchiyar tsawa wadda ya razana duk wata halitta mai rai dake cikin palon "I said get in!!!" Saboda tsorata Michael bai san lokacin da ya tashi da gudu ya haye sama ba ya razana sosai, yasan halin Romeo idan ya É—au zafi ba wanda ya isa ya tinkaresa shi yasa su daddy duk suka tsaya a baya, shima Michael É—in dan yafi su sanin halin Romeo ne, ya san bai É—auki zafi sosai ba shi yasa ya tinkaresa.

Goya hannu a saman kirjin Romeo yayi gently ya fara magana "what is happened?" Yayi maganar yana tsare Tga da dara daran blue eyes nasa nan, da kyar Tga ya iya buÉ—e baki saboda wahalar yadda Romeo ya muÉ—e masa wuya ya sanya shi kallon sama, ba dan Romeo ne ya masa tambayar nan ba da ba zai iya magana ba, amma tun da Romeo ne ba yadda zai yi dole ya amsa Maganar ko ma tayaya ne, a hankali yace "please help me with water, i need water!!" kallon Romeo daddy da Uncle Herry sukayi suna jiran Romeo ya bada izinin su kawo wa Tga É—in ruwan, amma sai sukaga Romeo yayi shiru alamar ba za'a kawo ruwan ba kenan, dan shi Romeo shirun sa ma magana ne, wani lokaci da shiru yake magana da Mutane, gaba É—aya jama'ar gidan sun san ma'anonin shirun Romeo, idan anana magana da shi yayi shiru to akoi abun da yake nufi baya shiru haka kawai, sannan baya magana sai da kwakkwaran dalili, shima kafin yayi maganar sai ya É—auki lokaci kuma ba wai dan bai ji me kace ba, yana ji, wani lokaci ka masa magana kana sauri sai yafi 5mins bai baka amsa ba, wata zubin ma har sai ka cire rai da zai yi magana sai kuma gaji ya baka amsa a nitse da sassayan murya, idan kuma bai game sa ba da wannan shirun zai baka amsa in ka gane to ruwan ka, idan ma baka gane ba nan ma kai ta shafa shi dai ya gama nasa.
Chapter 80 · 0% Book details