← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 126

Sashe 79

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin abun dake faruwa yasa James karisawa wajen da sauri yana faɗin "Uncle what is happening" a fusace Uncle Tga yace "where is lion?" "He's inside his room" James ya bashi amsa yana kallon daddy, wucewa Tga yayi ya haura sama, daddy kuma ya wuce ya nufi waje abun sa dan a tunanin Romeo bai dawo ba, da sauri James ya riƙe sa yana faɗin "Please dad don't..bai kai karshen maganar ba daddy ya dakatar da shi ta hanyar marairaice murya yace "Haba James my friend daughter fa tayi poison na kan ta, please ku bari naje na ceto rayuwar ta" girgiza kai James yayi kafin yace "Daddy you already know that lion baya magana biyu so just kawai ka hakura wasu likitoci su dubata" daddy na kokarin yin magana idon sa ya sauka kan face ɗin Romeo dake tsaye a sama bakin kofar shiga part ɗin sa furkar nan tasa a ɗaure tamau kamar hadari babu alamar wasa a tattare da shi ko kaɗan, tsabar yadda ya ɗaure fuskar har sai da gashin gerar sa suka haɗu daman kaɗan ya hana basu haɗe ba, shiyasa daya ɗaure fuska suka haɗe, nan take jikin daddy ya fara kerma ba shiri ya yasar da jakar hannun sa

Gently Romeo ya fara magana da wannan sexy voice ɗin nasa sannan ya tsare daddy da sexy eyes ɗin nan nasa masu ɗaukan hankali "where are you going?" Cikin sauri Tga dake gefen sa ya buɗe baki ya fara magana, hannu Romeo ya ɗaga masa alamar ba shi ya tambaya ba, daddy ya tambaya, shiru Tga yayi ya kama bakin sa yana kallon daddy, a tsorace daddy ya yiwa Romeo bayani a ta kaice, yar abokin sane tasha poison saboda son da takewa Romeo shi kuma daddyn ta da daddy suna tsoron ma Romeo yaji maganar dan zai iya harbe ta da kan shi, gashi yarinyar bata samun ganin Romeo a zahiri sai dai a Tv dan ko daddyn ta zai zo gidan su Romeo baya taɓa yarda yazo da ita saboda ya san halinsu Michael ma kawai in ya ganta tsab zai iya harbe ta da bindiga, dama dai James tace to shi yana da ɗan saukin kai, hakan yasa daddyn ta kullun yake ce mata zai faɗa wa Romeo idan sun haɗu, amma kuma bala'i tsoron Romeo yake kamar me, ko gaishe da Romeo baya iya yi saboda tsoron sa da yake ji, ita kuma yarinyar ta gaji da jira shi ne tace wa daddyn ta in dai bai faɗa wa Romeo ba zata sha poison, da a ka kwana biyu taga daddyn ta bai faɗa wa Romeo tana son shi ba shi ne tasha poison ɗin a ka kai ta hospital ɗin daddy, to shi daddy Romeo ya hana shi zuwa aiki kwata kwata, saboda ya hana daddyn shan wine, domin daddy idan yaje hospital baya iya yin aiki sai yasha wine wannan dalili yasa Romeo ya hana shi zuwa aiki gaba ɗaya yace ya zauna a gida dama ai ya tsufa, gashi kuma kwararen likitane mumber ɗaya a garin nasu, ana ji dashi sosai, doctor William jacop, sai dai baya iya aiki sai yasha wine yayi tatul ya bugu sosai.

Da hannu Romeo ya yiwa daddy nuni da hanyar bedroom na sa ba tare da yayi magana ba kasan cewar bai son yawan magana, jiki ba kwari daddy ya wuce bedroom na sa, zuciyar sa sai dukan uku uku yake yana addu'ar Allah yasa kar yar abokin sa ta mutu, yasani kab asibitin nasa ba wani likitan da zai iya yiwa yarinyar nan aiki cikin ƙan ƙanin lokacin ya cito rayuwar ta sai shi amma sai dai gashi yau yana ji yana gani shan giya ta ja masa ba zai taimaki yar abokin sa ba, ba zai iya tinkarar Romeo yace masa ba zai sha wine ba yayi hakuri ya barshi yaje ya mata aiki ba, yana jin tsoro dan ya san ma Romeo baya magana biyu ko mai zai faru idan yayi magana yayi ne.

Wucewa James yayi ya nufi hanyar fita daga palon dan suna da meeting da abokan harkallan sa karfe 6 dai dai, shi yasa zai yi sauri yaje saboda Romeo ya hana su wuce 9pm a waje shi yasa yanzu ya lallaɓa ogannin na sa akan a dai na meeting ko wani harkalla da daddare sai da safe, kasan cewar James shine babban yaron su da sukafi ji dashi yasa suka hakura suka dai na meeting na dare, dan James yana da girma a idon su suna son sa sosai, shine babban yaron su da idan suka bashi aiki cikin kankanin lokaci yake wannan aiki ya gama, har mamaki suke domin ko shugaban kasa suka ce James ya kashe zai iya kashe shi tsab ya samu horo daga wajen su sosai kama daga harbi da bindiga faɗa da hannu da sauran su, sai dai shi James ɗin yana ɓoye ya iya duk wayan nan abubuwan a gida saboda kar Romeo ya fahimci a koi wani abu, hakan yasa yake zama kaman wawa a cikin su ya nuna musu baya son tashin hankali kuma yana da hakuri, dan karsu kawo wani zargi a ransu amma ba abun da bai iya ba kuma shima ba wai saukin kai gare sa ba kawai basajane amma yana da zafi.

"Where are going James" Romeo ya tambaya in a cool voice yana tsare James É—in da sexy eyes É—in nan nasa masu firgitar da marasa gaskiya su kwantar da hankalin yan mata su razana zukatan jaruman maza, cikin sauri James yace "I just want to go out and chill" wucewa Romeo yayi ya koma bedroom na sa ba tare da ya sake magana ba, shi kuma James ya fice waje da sauri, Tga ya kuma ya sauko kasa ya zauna saman sofa, while shi Micheal daman bai fitoba yana lafe a saman katafaren bed É—in Romeo, su kuma Jay da John basa nan uncle Herry na barci.

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞

TRIPLET'S💞

*THE BEGINNING*

💞STAR LADY💞

WhatsApp me for more information 09162620621

Episode 25

Kai tsaye *Florida avenue* James ya nufa sai sharara gudu yake da motar sa a saman shinfiɗaɗiyar titin da zata sada shi da*Florida avenue* ya sanya kiɗa na tashi yana tuƙi yana tunanin yadda zai yi da ogan su, dan yanzu sun dawo masa da zancen kashe GAR sabo, kuma sun matsa masa a kan maganar sosai, saboda sun san duk cikin yaran su shi kaɗai ne zai iya yi musu wannan aikin cikin sauri, kan sa ya kulle sosai ya shiga damuwa neman mafita.

Bai ankaraba ya buge wani mutumi da yazo tsallaka titin, a sukwane ya ja wata mahaukaciyar birki har sai da kansa ta bugu da jikin glass ɗin motar, wani irin jiri ya gani lokacin guda, da sauri ya fito daga cikin motar, duk da kan sa sai faman sara masa yake haka ya karisa wajen mutumin da ya buge ɗin, kwance yake saman titi, sai dai da alama bai wani bugu sosai ba, bai ji ciwo sosai ba amma da alama ya samu karaya a kafa, da sauri James ya duƙa duk girman mutumin haka ya ɗauke shi cak, ya sanya shi cikin mota, kasan cewar unguwar na masu kuɗi ne hakan yasa ba hayani ya ba mutane kowa na cikin gida, tunani ya fara yi ina ya kamata ya kai mutumin nan.

Daga karshe dai ya yanke shawara ya wuce da shi gida duk da ya san zai fiskanci matsala daga Michael da Romeo amma bashi da zaɓi dole ya kai shi gida, haka ya ja motar sa da gudu ya juya motar ya koma gida.

Yana yin parking a parking space na gida ya fito ya ɗauki mutumin ya nufi hanyar shiga cikin gida, a guje jinga jingan sojojin dake tsakar gidan suna gadi, suka nufo shi, har suna rige rigen ansan wannan mutumin daga hannun sa dan su taimaka ma shi, ba musu ya miƙa musu dan dama bai son su Romeo su gan shi ya ɗauko mutumin zasuyi mamaki kasam cewar sun san shi da lalaci.

Haka suka shiga palon, a sukwame TGA ya miƙe tsaye yana mamaki, wucewa sojan da ya ɗauko mutumin yayi, yaje ya kwantar da mutumin saman sofa 3 seater sannan ya fice daga palon.

"James who is this man? What happened to him?" Tga ne ya jerowa James wannan tambayar, a takaice James ya faÉ—a masa abun da ya faru na buge mutumin da yayi, nan take Tga ya É—aure fuska sosai, a fusace yace "carry him out from this house!!!" zaro ido James yayi yana kallon ikon god, yana jinjinawa karfin hali irin na Tga, sai kace gidan sa to ko Romeo mai gidan ma ai ba zai ce a fita da mutumin nan lokaci guda ba tun da ni na bugesa da mota, sai ya bari mun masa jinya.

James yayi nisa cikin tunanin da zancen zuci da yake, sai ji yayi Tga ya daga masa tsawa "James I'm I not talking to you?" Yar firgigit James yayi kafin yace "I can't uncle" zaro ash eyes ɗin sa Tga yayi kafin ya wuce ya nufi waje, James na tsaye yana mamaki hali irin na yan uwansa su kwata kwata basa son baki a rayuwar su, inma mace ko namiji duk su basa so, basa son kowa ya raɓe su, sun fi son suyi rayuwar su su kaɗai, gaba ɗaya gidan haka suke ba mai son wani yazo cikin su, basa son mutane musamman Romeo yafi kowa tsanar wasu suzo kusa da su, daga shi sai Michael da Tga sun tsani baki.

Sai tunanin ta yadda zai kare da Romeo a kan mutumin nan yake, gashi mutumin yana sume baya cikin hayyacin sa, zuba masa idon James yayi yana kallon sa.
Chapter 79 · 0% Book details