← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 126

Sashe 12

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

.....Still Aunty na tsaye a wajen har Umaisha ta fito shirye cikin atamfa ɗinkin doguwar riga kayan sun mata kyau sosai kuma basu wani matse ta sosai ba sun dai zauna cif cif a jikin ta, ta ɗaura ɗankwalin kayan ɗaurin ture kaga tsiya ta yafo gyale yar karama fari a kafaɗa, ta sanya flat shoe fari a kafar ta hannun ta ɗaya riƙe da yar jakar ta fara, ɗayan hannun kuma riƙe da wayar ta da key ɗin motar ta tayi kyau sosai,
har ta kai bakin kofar palon zata fita sai kuma ta juyo tace "Aunty idan Abbi ya fito kice masa na wuce School" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta fice daga palon taje ta shiga motar ta kirar continue continue ta bar gidan,
Jiki a mace Aunty ta koma ta zauna saman kujerar table ɗin tana mamakin waye ya sanya mata gjishiri a abinci ta, shirye cikin suit Abbi ya fito hannun sa riƙe da jakar computer sa kai tsaye wajen da Aunty take zaune ya nufa a takai ce yace "Zan fita kina bukatar wani abun ne?" Da sauri ta miƙe tsaye tana faɗin "Dan Allah Abbi kayi hakuri" guntun murmushi yayi kafin yace "Shike nan komai ya wuce amma dai ki kiyaye gaba zan sa akawo wasu masu aikin tun da kin sa mun sallami wayan can kuma gashi kin zo baki iya girkin ba dole nasa a nemo wasu" ya kai karshen maganar tare yin hugging nata ya manna mata kiss a goshi kafin ya sake ta ya juya ya nufi hanyar fita yana faɗin "Ki kula min da kan ki na baki amana" "To mijina sai ka dawo Allah ya tsare min kai yauwa Abbi Umaisha tace na faɗa maka ta wuce School" jinjina kai yayi kafin yace "okey ki musu addu'ar Allah ya tsare min su" ya kai karshen maganar tare da ficewa daga palon murmushi tayi tana godewa Allah daya sa Abbi shi mutun ne mai saurin sauko wa idan yayi fushi, cike da kwarin gwiwa da fara'a ta kwashe kayan abincin ta mai da su kitchen ta haɗe abincin waje guda ta zuba cikin kwando ta wanke kwanikan ta gyare ko ina san nan ta fito ɗauke da kwandon abincin taje ta miƙawa baba mai gadi akan yaje waje ya zubar sannan ta dawo ta haye sama ta koma bedroom nata ta haye gado ta kwanta tana mai da numfashi.

RIMSHA

Gudu yake da motar sosai kamar zata tashi sama a tsakiyar dokar daji mai cike da dogayen bishiyoyi masu ganye kore shar, saboda cikan ganyen bishiyoyin yasa wajen yayi duhu sosai kamar dare, baka jin motsin komai a wajen wajen shiru, gudun bala'i yake shararawa da motar nan wadda da ka gan shi kasan gudun cetan rai yake ko kuma na rashin gaskiya,
Sun shafe 2 hours suna sharara gudu a dokar dajin nan suna keta bishiyoyi kafin su isa wani katon waje mai girman gaske wan da ke cike da yashi fari tas mai laushi har kyalli yashin yake, suna shiga wajen yashin ya rage gudun motar kasan cewar yashin yayi yawa tayar motar ba zata iya wani gudu sosai a wajen ba waje ne mai girman gaske dan sai da suka safe 1 hour suna tafiya cikin yashin kafin su fita ya keta ta cikin wasu bishiyoyin masu ban tsoro sun kewaye wajen sun yi kamar raun ta cikin su ya biyo duhune mai tsananin gaske a wajen haka ya kutsa motar sa ya wuce su ya ɓullo gaban wani katon gunkin kan mutun wadda jini ke zuba daga bakin gunkin kasan gunkin an kewaye kamar rijiya a nan jinin ke taruwa kamar kogi, gunkin shi kaɗai ma mutun ya gani ya isa ya sa shi mutu ko suma saboda ban tsoron sa idan ka ganshi kai kace yana da rai dan an gina idon sa a buɗe ga fari da baki irin na idon mutum ga kuma hawayen jini da ke fita daga idon na shi da baki da hanci yana da hanci mai girma gari guda girman kan gunkin nan ya kai girman kan traila ga tsawo ga faɗin daga saman goshin gunkin an rubuta *DAULAR MUTUWA* da manyan baki sun fito ɓaro ɓaro san nan aka zuba jini a wajen ya dawo ja kai da ganin wan nan ko ba'a faɗa maka ba kasan gidan mutuwa ne ba gidan zaman lafiya ba,
Yana zuwa dai dai gaban gunkin motar su ta ɓace ɓat ta fito cikin wani katafaren gida mai girman gaske kamar gidan fursina kashe motar yayi a tsakiyar gidan ya fito yana miƙa kamar wadda ya taso daga barci,
wasu kartin mutane su biyu masu kama da samudawa bakaƙe kirin kamar wayan da aka yiwa fenti da gawayi kai da gani kasan wayan nan cin namar mutane suke idon nan nasu jawur kamar jini ga katon hanci kamar tukunya suna da tsawo ga kiɓa wayan nan idan suka ɗaura maka hannun su ɗaya a kan ciki to fa sai dai wani ba dai kai ba, gashin kan nan nasu a tsai tsaiye kamar ƙawo gashi dogo ya musu kamar jijiyar bishiya suna da bala'i muni kamar a yanka a ɓuye wuka, duk in da suka yi taku ɗaya sai kaji kasa ya bada dim ɗim saboda girman su, matashin saurayin nan na tsaye har suka kariso wajen sa ɗaya daga cikin sune yasa hannu ya shafa kan mata shin, nan take matashin ya riƙiɗe ya dawo jibgegen kato baki mummuna mai katon hanci sai dai bai kai su girma ba ɗayan ne ya buɗe kofar motar cikin wata iriyar murya mara daɗin ji mai bada sautin amo mai kara kamar ganga da yaren su na matsafa yace "Barbushi yau ma yara huɗu ne aka samu fa" wadda aka kira da Barbushi ne ya kalli matashin da ya rukiɗe yanzu ya zama kato yace "Zaka iya tafi aikin ka ya kammala sai mun haɗu a aiki na gaba" ba musu Saurayin ya wuce ya nufi cikin gidan yana taku kasa na bada dum dum kamar ganga saboda girman ƙafarsa, dawo da kallon sa Barbushi yayi kan ɗayan daya buɗe motar da murya kamar an tada injin markaɗe in jin ma irin lalataccen nan mai kara mara daɗin ji mai rikita ƙwaƙwalwa yace "Kai Santilago ka kwashe su ka kai su ɗaki daban daban zuwa gobe da safe idan gimbiya ta fito sai muji me zata ce" Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya nufi hanyar komawa cikin gidan yana taku ƙasa na bada dum dum har ya shige ta wata ƙatuwar kofa mai ɗauke da tambarin wata mata tsaye ba kaya a jikin ta, ga malalen jini nan kwance cikin idon matar ga idon nata sun yi ja bakin nonon ta duk jini ke zuba aka zana ta,
shi kuma Santilago ya sanya hannu ya ɗauko Rimsha dake sume da hannu ɗaya ya ɗauko ɗaya daga cikin yaran ma da hannu ɗaya ya saɓa su a kafaɗar sa san nan ya ɗauko saura biyun yariko kafofin su kan su na lilo na kallon ƙasa haka ya wuce da su ta wata faffaɗar hanya dake ɗan gefe da kofar da Barbushi yabi yana tafiya kasa na amsawa nan ya rinƙa wuce ɗakuna masu burglaries kamar gidan fursina ba abun da ke tashi daga ɗaku nan face bala'i warin jini wani ɗakin kuma kaga akoi yara a ciki wani kuma sai dai kaga kashi ko wani sassa na jikin mutane, dai dai wata katafaren gate dake wajen ya tsaya, da gudu wani mutun wadda da ka gan shi kasan cikakken bil adama ne, yazo da gudu ya ɓuɗewa Santilago gate ya wuce da su Rimsha ciki, yana shiga wasu kantin mutane kusan kamar sa suka rufa masa baya su uku, ko wacce ɗaki daban ya kai ta Rimsha itace ta karshe suka kai ta wata ɗaki dake karshen ginin suna kokarin buɗe kofar ta farfaɗo daga doguwar sumar da ta faɗa kafin tayi wani yun kurin Santilago yayi wurgi da ita cikin ɗakin suka jawo kofar dafaffiyar karfe mai karfin gaske suka kulle suka sa key suka juya suka bar waje.
ÆŠaki ne mai matikar duhu baka iya ganin komai a ciki ko yatsun hannun ki baki iya gani, ga bala'i wari jini mai sa tashin hankali da tashin zuciya dake fitowa daga cikin É—akin.
Da kyar ta iya miƙewa zaune jiri na ɗibar ta sabida bala'i yinwa da take ji a sukwane ta toshe hanci lokacin da ta fara dawowa hayyacin ta waro dara daran fararen idon ta waje tayi ko zata samu daman ganin wani abu sai gwale idon take tana bin ɗakin da kallo tana toshe da hanci da hannu ɗaya ko tsillin tsinke idon ta ya kasa iya gane mata a ɗakin saboda tsananin duhu, motsin ta fara ji daga ɗan nesa da ita, a sukwane ta takure jikin ta waje guda saboda tsoro ta runtse dara daran idon ta tana ambaton sunan Allah ji tayi an ɗan taɓa ta a bayan ta hankali tashe ta yi saurin waro idon ta waje tare da juyawa a sukwane tana faɗin "wanene? akoi wani a nan ne?" ji tayi an kwashe da wata mahaukaciyar dariya da wata murya mara daɗin ji kamar na aljanu,
daga ɗan gefe kuwa wata iriyar siririn murya mai kama dana baby's taji ana kuka da shessheka kasa kasa, a razane tamike tsaye tana ja da baya tana faɗin "Dan girman Allah idan akoi mutane a ɗakin nan kumin magan kar ku haukatani ku dai na kukan nan mu rungumi Allah, Allah zaiji kukan mu zai kawo mana ɗauki" tayi maganar cikin harshen turanci ihu aka kurma da wata katuwar voice irin na yan shaye shaye, a sukwane ta toshe kunnuwan ta da hannayen ta dan ihun mai rikita ƙwaƙwalwa ne ba zata iya ji ba kan ta zai fashe nan take ta fara hawayen tsoro.
kamar daga sama taji an cire hannayen nata daga kunnuwan ta ana mata kukan mage a kunne, ihu ta fasa tare da bazama cikin duhun kamar mahaukaciya.
muryoyi uku uku ne suka fara fita lokaci guda ɗaya na dariya ɗaya na kuka ɗaya na wani irin abu kamar wakar shaiɗanu aljanu daga gefe guda kuwa kukan mage ne mai sautin gaske ke tashi, idan ta toshe kunne sai a buɗe mata idan tayi ihu suma abubuwan su kara sautin nasu ihun idan ta zauna shiru taji ana taɓata ga ɗakin duhu baka ganin komai.
Hawaye ta fara yi sosai wani na bin wani tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta daga ciki har da addu'ar san ya sabon kaya wato
Chapter 12 · 0% Book details