← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 126

Sashe 112

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A sukwane ya juyo dan ya tabbatar wa idon sa abun da yake gani, ganin da gaske ne yasa ya karisa wajen da sauri ya sanya hannu ya É—auki asalin na Michael wadda ta faÉ—o daga aljihun sa yana mamakin ya akayi watch É—in sa ya dawo gida, to ko dai daman bai tafi da shi bane? Ya jefawa kan sa tambayar da bashi da amsar ta, tuna cewa Romeo na kiran sane yasa yayi saurin É—aukan watch É—in ya fice zuwa part É—in Romeo.

Yana tafiya a hanya ya É—aura watch É—in a hannun sa.
A nitse yayiwa Romeo excuse sannan yashiga É—akin, Romeo yana tsaye yana fiskantar balcony bedroom É—in ya bawa kofar shigowa baya, James É—an basaja nan fa ya fara basajan nasa ya murje kamar ba shi ba, har da murmushi yana faÉ—in "My blood how are you" Shiru Romeo yayi na yan mintoci

Ba tare da ya juyo ya kalli James ɗin ba yace "where did Josephine live" Wato mum ɗin su kenan, James yayi shock da jin tambayar da Romeo ya masa, dan Romeo kwata kwata bai taɓa yin wani magana da ta shafi mum ɗin su ba, yau kawai ya tambayi ai nane location ɗin ta lallai akoi matsala kenan

Cike da tsoro yace "Me ya faru? Me kuma tayi?" A takaice Romeo yace "zan je nayi warning ɗin tane" zaro ido James yayi dan yasan warning ɗin Romeo babu kyau a tsorace yace "Daman gobe zan yi tafiya zan biya ta wajen nayi warning ɗin nata please lion karkaje wajen ta ka bari naje" shiru Romeo yayi bai sake magana ba, James kuwa yayi amfani da kwarewar sa a fannin basaja ya rinƙa lallaɓa Romeo har ya hakura da zuwa New York wajen mum ɗin nasu, ba karamin daɗi James yaji ba, sallama ya yiwa Romeo ya fito ya nufi wajen Musharraf, ta cikin glass ɗin show glass dake gefen sa ta nan ta bi James da kallo yana son fahimtar wani abu, sosai ya zubawa watch ɗin hannun James dara daran idon nan nasa, har James ya fice, a ransa yana tunanin dole yayi bincike a kan James dan zuciyar sa ta dage da zargin James sosai, a hankali ya juyo ya koma saman bed nasa ya kwanta tare da lumshe dara daran idon sa yana tunani a kan James, yana jin babu daɗin a ransa har barci ta ɗauke sa.

Mu leƙo Nigeria mu dawo

💞KATSINA💞

💞SUPER RESTAURANT💞

Shabiyu da minti arba'in Jehan ta fito daga wajen girkin restaurant É—in hannun ta rike da tray mai É—auke da plate dake shake da jolof rice yaji kayan haÉ—i sai kamshi yake, ga soyayyen ayaba wato plantain a gefe plate É—in, sai coca colar É—aya da ruwan faro, wani table ta nufa wadda wani matashin ke zaune a wajen yana latsa wayar sa, kallo É—aya zaka masa kasan É—an karya ne, dan yadda yake wani bubbuÉ—e hanci yana kallon mutane kallon banza.

Gaban sa tazo ta É—aura masa abincin saman table É—in ta juya zata tafi, a wulakance yace "Ke wace iriyar dakikiya ce? Wannan shine abun da nayi oder?" Shiru tayi ma shi kamar bata ji shi ba ta ci-gaba da tafiyar ta

Tsawa ya daka mata "Ke ba dake nake bane?!!" Ci-gaba da tafiyar ta tayi dan ita bata cika kula ire iren wayan nan mutanen ba, a cewar ta basu da hankali, ita kuma bata kula mahaukata,
ta san wannan hargagin duk me yake wa, dan yaga wasu yanmata sun shigo restaurant É—in ne yake wannan hargagin banzan dan su É—auka shi wani shegene yazo sayan abinci mai tsada, alhalin shinkafa yar 2k yazo ci.

Ganin Jehan taki kula shine ga kuma yanmatan suna kallon sa hakan yasa yaji idan ya bar su Jehan haka yaji kunya wajen yanmatan nan, dan haka sai ya miƙe a fusace ya nufi wajen Ibraheem tun da shine mai controlling na restaurant ɗin, sai wani cika yake yana batsewa kamar wani shegen mai kuɗi, duk kuma yana yi ne kar yaji kunya a idon ƴanmatan nan.

Ibraheem bawan Allah tun da Jehan tazo yake aikin kashe wuta, daga ta jajumo masa wannan sai ta jajumo masa wancan, yanzu ma yana zaune shiru yana latsa wayar sa cikin nishaÉ—i yana murmushi da alama abun da yake gani a cikin wayar tasa tana sashi nishaÉ—i,

Kamar daga sama ya fara jin ruwan bala'i wannan mutumin da Jehan ta kaiwa abinci "Wannan wani irin iskanci ne? Nayi odar gasassun kaji da chip ma'aikaciyar ku ta kawomin yar gidan malam Shehu wato shinkafa, me za'ayi da wata yar gado itace gidan uban kowa, ni na wuce cin shinkafa wlh sai dai kaji, kuma abun haushi ina mata magana tayi banza dani, har kamar ni zaku yiwa wannan cin mutuncin, to wlh baku isa ba sai na sa an rufe wannan restaurant ɗin, kun san waye ni kuwa? To na ma fasa cin abinci a wannan kazamin restaurant ɗin, kun ɓata min rai!!!" Duk bala'i da yake Jehan na jin sa amma ko ajikin ta dan bai ishe ta kallo ba.

Sai hakuri Ibraheem yake ba wa mutumin nan, amma yaki hakura ya dage shi ba zai ci abincin ba ya fasa

Daga jin wannan zancen nasa kasan dama bai da kuÉ—in sayan abincin.

Ba yadda Ibraheem bai bashi hakuri ba amma yaki yace ba zai ci ba kuma ba zai sake zuwa restaurant É—in ba, sannan sai yasa an rufe restaurant É—in yaga uban da zai buÉ—e

Daga karshe dai shiru Ibraheem yayi yana jin sa, har ya kammala surfa ruwan masifar nasa ya juya zai bar wajen, karaf sukayi ido huÉ—u da Jehan dake tsaye a bayan sa

Dogon tsaki yaja kafin yace "Ki rubuta ki ajiye sai kinyi nadamar abun da kika min" daga kasa Jehan ta fara kallon sa zuwa sama, wani kazami da shi ta faÉ—a a ranta

A takaice cikin kwanciyar hankali tace "KuÉ—in abinci" zaro ido yayi yace "Ban gane kuÉ—in abinci ba, ai ga abincin ku can ban ci ba kuje ku É—auki kayan ku" shiru Jehan ta É—an yi kafin tace "Kai kasan baka ci ba, ni dai kuÉ—i zaka bani, domin in dai Jehan ce ta kawo maka abinci to ko kaci ko baka ci ba dole zaka biya kuÉ—i"

Shi dai Ibraheem ido kawai ya zubawa wannan dirama na Jehan da mutumin,

Rai a ɓace mutumin yace "Wannan ne kuma baki isa ba, bazan biya abun da ban ci ba" shiru Jehan ta ɗan yi kafin tace "Zaka bani kuɗi nane ko dai sai rai na ya ɓaci?!!" A wannan karon tayi maganar cikin harshen turanci, nan take yaji tsoro ya kama shi

yadda Jehan ke magana da confidence yana sanya mutane da yawa tsorata suyi zaton ko yar wani ne ko kuma akoi abun da ta taka, amma kuma basu sani ba ita ma tsoron nata na ciki, kawai dannewa take tayi magana da confidence dan ta kwatar wa kan ta yanci, a tunanin ta idan ka nuna kana tsoro abune sai ya baka tsoron da gaske, amma idan kace baka san tsoro ba a filli sai abun yazo maka da sauki.

Mutumin dai yaji kunya domin ya tsorata da Jehan dan ta tsaya with her full confidence tayi masa magana kamar wata yar uban wani ko ta taki wani tsiya.

Ƙasa ya farayi da murya yana faɗin "Ni ba zan biya abun da ban ci ba" tsare sa da ido tayi bata sake masa magana ba, hakan ba karamin tsorata shi ya sake yi ba, dan gani yake kamar ko dai wannan kanwar maza ne, ma'ana irin kannen yan daban layin nan ne shi yasa take haka, ko kuma dai yar wani hamshakin ɗan daban ne, wadda idan ka taɓa ƴaƴan su suke kashe mutun

Allah sarki bawan Allah shi kuma ta nan ya kai Jehan, ita kuwa ta tsaya kyam a fili babu alamar tsoro a fiskar ta amma a ciki sai dukan uku uku zuciyar ta keyi kamar zatayi fitsari a wando.

Ibraheem na kokarin dannan Jehan a kan ta hakura mutumin ya tafi tun da bai ci abincin ba su su É—auki asaran kawai, afili Ibraheem yayi magana kamar da gaske amma ba haka bane, yana tsoron kalaman mutumin ne da yake cewa zai iya sawa a rufe restaurant É—in wadda idan hakan ta faru ogan su sai ya rufe shi a police station zai ce shi ya hadda sa komai, shine baya kula da costumers, sai dai ya manta wace ce Jehan dan in tayi magana ba wanda ya isa ya sata ta janye.

Hannu ta É—agawa Ibraheem kafin tace "Malam ka manta nace kada ka sake min magana ne? Ogan ka shine dai'dai nayi magana da shi ba kai ba, please karka sake shiga harka ta" shiru Ibraheem yayi dan shi kan shi Jehan na bashi tsoro wani lokaci, shi É—aukan mai aljanu ma yake mata.

Jehan kenan duk wanda ya zauna da ita tofa É—aukan da zai mata daban.

ÆŠago dara daran idon ta tayi ta kalli agogon dake manne a bangon wajen 12:50pm É—aure fuska tayi sosai cikin tsawa tace "Ka bani kuÉ—in abinci lokacin tafiya ta gida yayi!!!" Zaro ido Ibraheem yayi "Lokacin tafiyan ta gida yayi kuma?" Ibraheem ya mai'mai ta a zuciyar sa yana mamaki.

Mutumin kuwa da yaga Jehan fa ba wasa take ba, sai ya hakura ya ciro 2k daga aljihun sa ya miƙa mata yana faɗin "kuje Allah ya isa na" karɓan kuɗin tayi abun ta ta wuce ta koma wajen girkin nasu, shi kuma mutumin haka ya wuce ya fice daga restaurant ɗin yana son cin abinci amma yana jin kunyar yaje yace zai ci yanmatan da yayi burga dan su su mashi dariya gashi kuma yinwa yake ji sosai haka ya hakura ya fice daga restaurant ɗin,
Chapter 112 · 0% Book details