← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 126

Sashe 46

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar Abba ya iya miƙewa ya ɗauki wayar sa ya kira doctor sa dan yazo ya duba su.

Baa É—auki lokacin sosai ba sai ga dr yazo, koda dr ya duba su sai yace shi bai ga komai ba, mamaki ne ya kara bayyana a face nasu Abba da kan sa ya sanya hannu dai dai sai tin in da dodannin nan suka zanawa Hajiya karfen nan yake ta jini, yasa hannu a wajen yana nunawa Dr, amma dr yace shi bai ga komai a wajen ba, clean yake kallon wajen, sun shiga ruÉ—ani sosai daga su har dr, domin kuwa shi dai Abba shi da Hajiya ga ciwo na nan suna gani a jikin su amma a ce musu ba ciwo, ga jinin su nan sai zuba yake dr yace musu bai ga komai ba, shi Abba ma a face nashi ciwon yafi yawa duk dodannin nan sun zazzane masa face nashi da wan nan zabga zabgan bulalu nasu sai jini fuskar keyi amma shi dr baya ganin komai very smooth yake ganin face É—in Abba, tashin hankali ba'a sa maka date

Abba da ya ga dr ya dage a kan shi bai ga komai ba sai ya fara tunanin to ko dai dr ya samu taɓin hankali ne, dan haka sai ya sallame sa, ya ɗauki waya ya kira driver sa a kan yazo ya kai su hospital, nan driver ke sanar masa ai yana Abuja a hotel ɗin da suka sauƙa tun jiya yake jiran sa bai gan shi ba ya kira layin sa bata shiga, zaro ido waje Abba yayi tare da dafe kan sa yana kokarin ko zai tuna wani abu da ya faru, yaushe ya dawo Kaduna meke faruwa da shi ne, sai jerawa kan sa tambayoyin da bashi da amsan su yake, hakan yasa ya gane ba dr ke da matsala ba shi ne ke da matsala

ita dai Hajiya ta kasa magana tana kwance shiru sai hawaye da take saboda azaban zafin da bayan ta ke mata in da dodannin nan suka yanke ta, gashi kuma dr yace bai ga komai ba alhalin ga ciwo nan karara kwance a bayan ta yana mata raɗaɗin azaba san nan ga jinin ta sai zuba yake amma dr yace bai gani ba kuma har ma da jinin dake zuba dukka bai gani ba wan nan wani irin masifa ne? Haka ita ma ta rinƙa jerowa kan ta tambayoyin da bata da amsar su, tana yi tana hawaye.

Wunin ranar dai haka suka wuni cikin tashin hankali da damuwa, Abba ya kira likitoci daban daban amma duk wanda yazo sai yace bai ga komai ba, tun abun na basu mamaki har suka dai na mamaki suka rungumi kaddara suka lallaɓa suka taimakawa junan su wajen yiwa kan su dressing na wajen, sunayi suna hawaye dukkan su.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*After some day's*

su Akila kowa ya koma gida sun gama yiwa daddyn jelly hutu, kafin su koma ba yadda su Imran basu yi da daddy ba a kan ya faɗa musu damuwar da amma yaki sai yace musu ba komai, da suka matsa masa da tambaya sai ya ɓata rai ya ɗaure fuska cikin umarni yace karsu sake tambayar sa, haka suka hakura ba dan su rinƙa so ba.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*KADUNA*

Irfan yasha ruwan mamaki ganin yadda aka gyara masu gidan su ga kuÉ—in da Abbi ya samu, san nan ga karatun master's degree nashi da zai je yayi a uk wow abun ya masa daÉ—i over har azumi godiya ga Allah sai da yayi, su Aafia kuma an samu babban waya ga babban makaranta nan rashin mutunci ya karu dozin dozin, ita kam Umaisha wayan ta biyu ga wan da Akil ya saya mata san nan ga wadda a ka kawo mata, murna awajen su ba'a magana

cikin kurna Aafia ta kira Kawar ta Rufaidat da suka gama secondary tare, ta sanar da ita abubuwan da suka samu na alkhari, sosai a fili Rufaidat ta nu mata farincikin ta san nan ta dora mata da cewa tana taya ta murnan samun babban makaranta, suma Allah yasa su samu mai dafa masu, da murna Aafia tace In Sha Allah zata faÉ—a wa Abbin ta zai taimaka musu, sai godiya Rufaidat ke yi sukayi sallama

dukkan kawayen ta da sukayi secondary sai da ta kira ta sanar musu da abun alkharin da ya same su, sosai suka rinƙa taya ta murna, ita kam Umaisha daman bata da kawaye. Wan nan kenan

*WASHINGTON DC*

zaune Michael yake a *Harvard community garden* ga lucky Copper Winston a gefen sa,
kan sa na kan wayar sa yana latsawa, su John suka iso wajen suka same sa, zama suka yi gefen sa Test na faÉ—in "I'm feeling hungry bro's" ya faÉ—a yana kallon Michael dake faman latsa waya, John ne yace "Okey kuje super restaurant mana kuyo oder sai a kawo muku nan" satar kallon Michael Dest yayi hakan yasa John ya gane me suke nufi, basu da kuÉ—i kenan, kallon Michael É—in John yayi kafin yasa hannun a aljihun sa ya fito da kuÉ—i yana kokarin basu kenan wasu turawa su biyu suka iso wajen,

ganin yan matan yasa su John juyowa a sukwane suna kallon Michael da kwata kwata hankalin sa baya kan su, cikin sauri Dest yace da yan matan "Kuzo muje" yayi maganar a tsorace dan bai san hukuncin da Michael zai masa ba idan ya ga yan matan a wajen, tsawa É—ayar yarinyar ta daka masa tana faÉ—in "babu in da zanje har sai ka bani kuÉ—in zubar da cikin nan" tashin sense jin muryan mace yasa Michael É—agowa da sauri yana kallon su, ihu Dest ya fasa yana ja da baya, ba Dest kawai ba har John sai da ya ja baya, nan take idon Michael ta canja launi zuwa ja cikin tsawa yace da yarinyar "leave this place before I open my eyes!!" Kallon sama da kasa tayi wa Michael kafin tace cikin faÉ—a "Kai ba da kai nake ba tukun nan kuma idan kaga na bar nan to na samu abun da nake so ne" girgiza kai kawai John yayi yana yiwa yarinyar addu'ar Allah ya ceceta, shi kuwa Michael a fusace yace da Copper "give her a good punishment" zaro ido waje Dest da Test suka yi, shi kuwa John godiya ma yayi ga Allah dan Michael bai bata horo sosai ba, yayi mamaki sosai, dan kamar yadda su Michael su ka tsani Mum É—in su haka suka tsani duk wata mace a duniya shi yasa duk masu aikin gidan su sojoji ne kuma maza, mace bata zuwa ko in da inuwar su take dan suna ganin dukka mata irin É—aya suke da mum É—in su, hakan yasa duk wata macen da tayi gigin zuwa in da suke to kuwa ta shiga uku, sun tsani mata over kuma duk mum tasu ce silar komai.

Dirowa kasa Copper yayi tare da girgiza jikin sa, yana miƙa, durkusawa kasa Dest yayi ya riƙe kafafun Michael yana faɗin "Please Michael forgive my wife bata san kai wanene bane shiyasa kaga ba'a School nan take ba, bata san ka ba da bazata zo kusa da kai ba please she's pregnant kuma ina bala'i son cikin nata sosai" shiru Michael yayi kamar bai san da mutun a wajen ba, shi kuwa Copper tun da ya riga ya ansa umarni sai ya daka haushi mai razanar da kwakwalwa wadda yasa matan fasa ihu suka watsa a guje, kamar jira Copper yake yabi bayan su, yana gudu yana girgiza jikin sa, kuka sosai Dest ya fara ya ci-gaba da rokan Michael a kan ya dakatar da Copper kar cikin jikin matar sa ya zube, shi kuwa John da gudu yabi bayan su Copper duk da yasan ba zai iya dakatar da Copper ɗin ba, dan ba wanda ya isa ya dakatar da shi sai Michael ɗin da ya haɗa su da shi,

shima Test duƙawa yayi suka haɗu suna rokan Michael dake zaune yana latsa wayar sa hankalin sa kwance.

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞

https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo

*💞The beginning💞*

*Episode 15*

_____gudu sosai yan matan suke kamar zasu yi hauka suna kurma ihu, shi kuma Copper yana biye da su, haka suka bazama cikin school É—in basu san in da suka nufa bama.

Suna gudu suna waigowa su kalla ko Copper ya kusa kamo su, matar Dest bata an karaba ta juya tana kallon Copper sai ji tayi ta bugu da mutun, baya baya tayi ta faÉ—i kasa, tare da fasa ihu,

ba shiri ɗayar yarinyar ta ja birki da gudun da take ta waigo dan ganin ko dai Copper ne ya kama matar Dest ɗin yasa take ihu, a guje Copper yayi kan ta da niyar cizon ta, a guje ta miƙe dan ta gudu bata lura da mutumin da tayi karo da shi ɗa zun ɗin ba, still yana tsaye a wajen tana kallon su, tana kokarin gudu ta sake yin karo da shi tayi baya zata faɗi, da sauri yasa hannu ya riƙo hannun ta tare da janta tayi ta bayan sa, daka sufa Copper yayi yayi kansu, a fusace James ya kai masa bugu a kai sai da yayi baya ya faɗi kasa,

a sukwane ya miƙe tare da daka haushi mai karfi yayi kan James ɗin yana buɗe baki kamar mayin wacin zaki, duƙawa kasa James yayi ya damko makogoran Copper ɗin tare da zaro manya manyan light ash eyes ɗin sa, cikin tsawa yace "put your eyes into my own!!"

Ganin James ne yasa Copper daka haushi mai tashin kai kana ya dukar da kan sa kasa, sakin makogoran nasa James yayi tare da miƙewa tsaye, cikin tsawa yace da Copper "Muje in da ka fito" juyawa Copper yayi ya wuce ya mufi *community garden*
ba tare da James ya yiwa su matar Dest magana ba ya wuce yabi bayan Copper, cikin sauri suma su matar Dest É—in suka bi bayan sa.
Chapter 46 · 0% Book details