← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 126

Sashe 62

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun John na iya gudu har ya kasa dan already dawakan ma sun riga sun jima da wuce sa, shi kuma Romeo ya wuce ya bar wajen tun tuni, yau Tga ne ya hukun ta John, ya hora John iya horar wa, kafin ya kyale sa tare da yi masa kashe di a kan kar ya sake sha wine ya shigo cikin gida a buge, idan zai sha ya nitsu waje guda ya sha kuma ya kwanta a wajen yayi barci har sai ta sake sa, gidan su gidan mutun ci ne a kasar dan haka ya kiyaye shan wine yana yawo a sakar gari kamar mahaukaci kar ya ja musu zagi da zub da mutunci, sosai John ya niku tillis da kyar ma yake magana, sai murna Jay yake an masa magani John yau, da haka suka watse kowa ya nufi part na shi.

*12:30 am*

Duniya duk suna barci shi kuma Romeo a lokacin bodyguard É—in sa ke serving nasa abinci, kamar wani aljani, while shi kuma James yana kwance saman katafaren gadon sa yana aiki a system na sa, yana shirya ta yadda zai sa mai gidan sa ya janye daga aikin kashe GAR.

Zaune Romeo yake saman table chair na palon kasa ga jibga jibgan Bodyguard guda 24 a kan sa 12 ta gefen nan 12 ta gefen nan, kamar dai yadda suka saba, palon gaba ɗaya gauraye yake da hasken kwayayen lantarki dake manne a saman POP palon, har wutan jikin staircase a kunnen suke, shi yasa palon yayi haske over, hakan ba karamin kara kawata palon yayi ba gwanin kyau da ɗaukan hankali, ga sanyin Ac da kamshi air freshener da ya haɗu da kamshin perfume ɗin Romeo hakan ya bada wata irinyar fitinanniyar kamshin mai kwatar da hankali mai shaƙa

sanye Romeo yake da kayan barci, riga fara kal mai jikin bargo zuwa gwiwar sa mai ma ɗauki a tsakiyar rigar, while gaban rigar a buɗe, ga wani kwantatciyar dark black gashi mai tsantsi da sheki kwance a saman faffaɗar kirjin nasa, soft skin na shin nan sai sheki yake kamar bai taɓa fita waje ba, sai faman lumshe dara daran blue eyes na shi yake kamar mai jin barci, lallausan lips na shin nan sun kara zama red sosai saboda ya ɗan cizasu kamar wadda wani abun ya ɓata wa rai, hakan yasa suka kara ja sosai, lips na shin sun kasan ce kamar audiga saboda laushi shi yasa da ya ɗan ciza su kaɗan sai su kara ja.

Duk wani abun da zai buƙata bodyguard ɗin sun zuba masa a plate kasan cewar sun san koda sun tambaye sa ba amsa musu zai yi ba, hakan yasa daddy ya faɗa musu abubuwan da yafi buƙa ta da yazo dining table su zuba masa, shi yasa da yazo suke serving na shi kawai.

Almost 20 mins yana zaune yana latsa waya sai faman lumshe dara daran ido sa yake yana É—an cije lallausan lips na shi, ga abinci kuma bodyguard sun zuba masa.

A ɓangaren James kuma bayan ya kammala shirye shiryen sa sai ya kira mum ɗin su a waya, dan su gaisa, duk da ba wani son ta yake ba kuma yana jin haushin ta hakan baya hana shi, duk bayan 1 year ya kirata su gaisa, ba ƙaramin daɗin hakan take ji ba, saboda son da take musu amma shi Romeo da Michael da Tga, da dad, uncle Herry, ko da wasa basu taɓa kiran ta a waya ba ba kuma su taɓa kusan tar in da take ba, Mahaifiyar su baturiyar cikin New York ce, a halin yanzu ma tana zaune a can New York ɗin, tsakanin Washington DC da New York babu wani nisa sosai amma ko da wasa basu taɓa tunanin ma su kai mata ziyara ba, sun tsani ganin ta basa son ta ko kaɗan ta sanadiyar haka ne Michael da Romeo suka tsani dukka mata, dan su sunfi tsanar ta.

Sai daɗi mum take ji da James ya kirata, suna gaisawa ya tambaye ta ko tana buƙatar kuɗi, cikin murna tace masa a'a kiran da ya mata ma yafi mata komai a duniya, yana jin bata bukatar komai ya katse kiran sa, tayi kokarin kiran sa amma ina bata same sa ba, dan in ya kira ta suna gama waya yake sata a blacklist dan ma kar ta sake kiran sa, dan ba wani son ta yake ba kawai tana ɗan bashi tausayi ne shi yasa yake kira yaji ko tana bukatar wani abun ko kuɗi

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞

TRIPLET'S💞 20

https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo

*THE BEGINNING*

💞*STAR LADY*💞

EPISODE 20

Sai daɗi mum take ji da James ya kirata, suna gaisawa ya tambaye ta ko tana buƙatar kuɗi, cikin murna tace masa a'a kiran da ya mata ma yafi mata komai a duniya, yana jin bata bukatar komai ya katse kiran sa, tayi kokarin kiran sa amma ina bata same sa ba, dan in ya kira ta suna gama waya yake sata a blacklist dan ma kar ta sake kiran sa, dan ba wani son ta yake ba kawai tana ɗan bashi tausayi ne shi yasa yake kira yaji ko tana bukatar wani abun ko kuɗi

Ajiye wayar yayi saman bedside drawer ya ɗauki remote ya kashe wutar ɗakin gaba ɗaya, san nan ya kunna lamp na saman bedside drawer, tare da jan bargo zuwa saman kirjin sa ya lumshe ido, amma ya kasa barci sai tunani yake a kan yadda zai ɓullowa ramarin aikin da a ka sa shi na kisan GAR, dan gaskiya zai iya kashe kowa idan suka bashi aikin hakan amma ban da GAR, ba zai iya wan nan aikin ba, ko wani ya gani zai cutar masa da ɗan uwan sa na jini sai in sa karfin sa ya kare bare kuma a ce shi da kan sa kai ina hakan ba zai yiwu ba, gashi kuma baya jin kamar zai iya fita daga kungiyar nan nasu, dan yana son aikin sosai da sosai, Yasan cewa shi ne yake da hanya mafi sauki da zai iya kashe GAR cikin ruwan sanyi ba tare da shan wahala ba, amma ko a mafarki yayi mafarkin hakan to idan ya tashi sai ya hukun ta kan shi, yanzu shi babban damuwar sa a nan shi ne idan shi yaki yarda ya kashe GAR to fa zasu bawa wani aikin, gashi kuma GAR bai damu ya yawo da sojoji ko bodyguard sosai ba kasan yana ganin kamar ba wata damuwa, amma time to time yana fita da sojoji sosai. Haka dai ya rinƙa tunane tunanen sa na neman mafita har barci yayi awon gaba da shi.

A ɓangaren Romeo kuwa, hankali sa kwance yake ɗaukan fruit da bodyguard suka yayyan ka masa suka shake masa plate da su, hankalin kwance cikin nutsuwa yake ɗauka yake kaiwa ɗan ƙaramin bakin sa, a hankali yake motsa laɓɓan sa kamar bai son tauna abu haka yake cin fruits ɗin, da yaci kaɗan bodyguard ɗin jikin su na kerma zasu muƙo masa tissue paper, wani lokaci ya ansa ya goge bakin sa wani zubin kuma yayi kamar bai gan su ba, haka zasu mai da, suna tsai tsaye kamar wasu saƙaguna ko alamar barci babu a idon su, shi kuma yana zaune sai latsa waya yake yana cin fruits a hankali cike da class da izza.

Sai 01:00 am, san nan Romeo ya miƙe cikin nitsuwa ya nufi bedroom na shi, yana tafiya suma bodyguard ɗin suka nufi waje dan suje su kwanta su hutu, kasan cewar dama Romeo shi ne mutun na karshe dake cin abinci kullun, dan wani lokaci ma sai 2 na dare yake cin abinci kamar wani aljani sai dai ba wani abun kirki yake ci da daddaren ba baya wuce fruits ko kuma salmon, to da zarar yaci abincin daren sa ya wuce bedroom suma bodyguard ɗin zasu wuce nasu bedroom ɗin sai kuma da safe idan za'ayi breakfast sai suzo wajen table ɗin dan suyi serving masu cin abinci, sojoji uku ne ke girka musu abincin a gidan, idan sun gama kirkin su Romeo sai su fara girkin nasu bodyguard da sauran sojojin dake gidan, mai shara da mopping a gidan dukka sojiji ne, duk wani aiki na gidan jibga jibgan sojoji masu razanar da zuciyar maza ke yin sa.

Romeo na shiga bedroom na shi ya haye katafaren lallausan gadon sa mai kama da audiga, daman sai lumshe dara daran idon nasa yake alamar yana jin barci, bedroom É—in gauraye yake da gasken wuta lantarki launin sky blue, hakan ba karamin karawa bedroom É—in kyau yayi ba, kashe wutar É—akin gaba É—aya yayi har da na jikin furniture É—in da lamp na saman bedside drawer duk ya kashe su dan shi bai son haske idan zai yi barci, nan take É—akin ya gauraye da duhu, remote ya É—auka ya kara gudun Ac san nan ya ja lallausan bargon sa mai kama da audiga zuwa saman faffaÉ—ar kirjin sa, ba jimawa barci yayi awon gaba da shi.

*NIGERIA*

*KADUNA*

Matasan unguwa ne suka fito yuka samu Yusuf yashe a kasa ya rasu, sosai suka sha mamaki da jimami abun da ya faru, wasu daga cikin abokan sa sai cewa suke yanzu fa suka rabu da Yusuf lafiyar shi kalau, wasu kuwa cewa suke an ya ba wani abun ne ya samu Yusuf ba, haka dai jama'a sukayi ta ceceku ce.

Sai washegari a kai masa sutura a ka kaishi makwancin sa wato gabarin sa, sosai mahaifiyar su Rufee tashiga damuwa da tashin hankali dan Yusuf shi ne karfin gidan, ita kam Rufee bata wani damu sosai ba kuka iya na yan mintoci tayi daga nan ta dasa daga in da ta tsaya, ba wanda ya iya gane me yayi sanadiyar mutuwar Yusuf, kowa ya bar abun a matsayin karar kwana, alokacin da abun ya faru a koi matasa guda biyu dake zaune kofar gidan su, a kan idon su komai ya faru amma sun manta komai sun kasa tunawa, abun ya wuce musu kamar basu gani ba.
Chapter 62 · 0% Book details