← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 126

Sashe 44

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

san nan mai makarantar ya yi Godiya ya gabatar da speech akan makarantar ya gabatar da Malaman makaranta gaba É—aya sannan daga bisani ya nemi daddy da ya bama students gifts nasu da award nasu. Amsa masa daddy ya yi.

makarantar ya fara kiran students ɗaya bayan ɗaya suna zuwa amsar gift nasu da award nasu, da aka zo kan Rimsha Ita kaɗai Awards Guda huɗu taci Best in Islamic Studies, best in English, Best in Mathematics, se best in home economics. Sannan aka bata wani medal na The person with the Highest points. Daddy sabida murna seda ya mata hawaye a cikin bainar Jama'a, ta ƙara so gabansa ta share masa hawaye tace "Daddy In Sha Allah we'll keep making you proud" murmushi yayi yana kokarin tsaida hawayen sa, Jehan ta ƙara so wajen cikin harshen turanci tace "Daddy please stop crying" ta faɗi kaman zata yi kuka murmushi shi ne ya kubce masa ya haɗe su gaba ɗaya ya rungume yace "Am proud of you my daughters Allah ya yi wa rayuwar ku Albarka" gaba ɗaya Hall ɗin suka amsa da Amin Amin, shi bema san yayi maganar da ƙarfi ba har suka ji.
Miƙewa yayi ya ciro check a aljihunsa wanda already ya rubuta tun a gida ya miƙama me makarantar yace "gashinan Sadaƙatul Jariya school fees ne na Mutane 500 complet har su gama makarantar nan, ku sanar da marasa ƙarfi da suke son ƴaƴan su suyi karatu basu da halin biya musu gashinan na biya" "Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar" Hall ɗin ya dau Kabbara, Mutuwar tsaya da ta zaune manya manyan masu kuɗi da sukazo taron domin ƴaƴan su suka yi, sun sha ruwan mamaki irin kyautan da daddy yake, baya jin kyashi ko kaɗan, shi kuwa daddy bai jira cewar kowa ba yace su Rimsha su ɗauki stuffs ɗin su su wuce gida, haka kuwa a kayi suka ɗauka suka nufi mota sai sauri daddy yake dan bai son jama'a su tsaida shi suce zasu yi hoto.

Yana zuwa parking space É—an sandan sa ya buÉ—e kusu mota suka shiga, da sauri É—an sandan yaja motar suka bar school É—in.

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai

💞Star Lady💞

*💞 TRIPLET'S💞

https://chat.whatsapp.com/Fv91yECNmlW3W0mQG2hGSo

*💞The beginning💞*

*Episode 14*

*KADUNA*

*Unguwar sarki*

Hajiya Umaiya na sume a tsaye, shi kuma Abba yana sume a kwance har sai da Lami ta dawo daga kasuwa, ta isko su a sume, ihu ta fasa tayi kan Hajiya tana kiran sunan ta, tana taɓa Hajiya, Hajiya ta zube kasa wanwar, kara tsorata Lami tayi ta nufi fridge ta ɗauko ruwa jikin ta sai kerma yake ta buɗe ruwan, tsabar kiɗimewa da tayi bata san lokacin da ta juyewa Hajiya ruwan gaba ɗaya a kan taba, Ihu Hajiya ta fasa mai razaba kwakwalwa tare da miƙewa zaune tana zazzare ido kamar an tare ɓera a tarko, waige waige ta fara yi kamar mai neman wani abun, can idon ta ya sauka kan Abba dake sume cikin tsoro tace "Ke Lami me yasami Alhaji? Yaushe ya dawo?" Kara zaro ido waje Lami tayi murya na rawa tace "Nima a nan na dawo na same ku kuna sume" kara waro ido waje Hajiya tayi, tayi shiru tana kokarin tunano me ya faru, amma ta kasa tuna komai, jiki ba kwari ta yunkura tana son miƙewa, sai ji tayi gaba ɗaya jikin ta ya mata nauyi sosai, dafe kan ta dake sara mata kamar zai fashe tayi da kyar ta iya miƙewa tana faɗin "Kawo min ruwa" da sauri Lami ta miƙe ta ɗauko wani ruwa a fridge ta dawo ta miƙewa Hajiya, ansan ruwan Hajiya tayi tare da duƙawa kusa da Abba ta tarfo ruwan a hannun ta ta shafa masa a face nashi, dogon numfashi yaja tare da saukewa a hankali, ya waro idon sa waje ya fara bin saman da kallo kafin ya sauko da idon sa kan face ɗin Hajiya, a hankali ya miƙe zaune yana kallon Hajiya "Alhaji yaushe ka dawo?" Hajiya ta tambaya tana zaro ido, shiru yayi yana bin ta da kallo, "Alhaji kayi magana mana"

da kyar ya iya motsa bakin sa yace "Hajiya yaushe na dawo? Ba ina Abuja ba?" tashin sense shiru Hajiya tayi tana kokarin tunano yaushe Alhaji ya dawo, amma ina ta kasa tuna komai, shima Alhaji shiru yayi yana kokarin tunano yaushe ya dawo bayan shi dai yasan yana Abuja wajen meeting to ya akayi ya dawo gida

Almost 30mins sunyi shiru suna tunani daga karshe suka hakura da kokarin tunano me ya faru da su, haka suka miƙe suka wuce sama ran su cike da tunani fal.

Hayewa saman gadon Abba Hajiya tayi ta kwanta ta dafe kan ta dake tsananin sara mata kamar zai fashe, shi kuma Abba yaja kafar sa a hankali da kyar da kyar ya shiga toilet dan yin wanka,

a ta kaice dai su Hajiya sun manta komai da ya faru sun manta da abun da ya faru da Hajiya Zainab.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*WASHINGTON DC*

*LOT 33*

*06:00am*

Sanye yake da short mai É—an girma zuwa gwiwar sa sky blue kyakkyawar cinyoyin nan nasa a waje ga kyawawan gashi dark brown kwance a cinyar nasa daga sama har zuwa idon sahu na kafar sa, jikin sa na sanye da farar riga mara nauyi mai karamin hannu, kyau iya kyau Tiger na da shi kyakkyawan Bature ne sosai sai iskanci kala kala, ba kalan da bai iya ba rashin kutunci ne cike fal a kan sa,

A hankali yake takawa har ya haura sama gaba É—aya, ya tura kofa ya shiga wani waje mai kama da É—aki, sai dai gaba É—aya wajen da glass a kayi shi, kasan wajen kuma kyakkyawar grass carpet ne a wajen launin kore, waje ne mai girman plot 1, an kawata wajen sosai ga luntsuma luntsumar kujerun hutawa san nan ga injunan motsa jiki kala kala a wajen, da gani kasan wajen training na su ne, ga in juna da mashuna kala kala masu kyau da tsadar gaske, wajen dai ba'a chewa komai sai dai masha Allah.

A hankali Michael ya kariso cikin wajen, kusa da wani mashin na motsa hannun ya tsaya, yayin da wani matashi ke kwance a wajen yana É—aga wasu kana kana nan karafuna.

Kallon tsab Michael yayi wa matashin kafin yace "Good morning photo copy" Ajiye karafunan hannun sa guy ɗin yayi tare da miƙe wa zaune, subhanallah tsarki ya tabbata ga Ubangiji dayayi wayan nan halittu, guy nan kamannin sa ɗaya sak da Michael ba abun da ya raba su sai kwayar ido da gashin kai, Michael gashin kan sa dark brown ne, shi kuma guy nan gashin kan sa ya rina ta ya sanya mata color ta dawo light brown mai kama da golden, sai kuma kwayar ido Michael kwayar idon sa light brown ne shi kuma guy ɗin nan nashi idon light ash ne masu kyau, ban da ido da gashi komai nasu ɗaya ne.

Kallon tsab guy É—in yayi wa Michael kafin yace "how are you doing this morning?" "I'm going well" ya faÉ—a tare da wucewa ya nufi wajen motsa kafa, har ya kai wajen sai kuma ya juyo yana faÉ—in "James yaushe Romeo zai dawo?" Komawa James yayi ya kwanta ya ci-gaba da É—aga karfen da yake yana faÉ—in "I don't know maybe this week" shiru Michael yayi ba tare da ya sake magana ba, shima James shiru yayi ba tare da ya sake magana ba suka ci gaba da motsa jikin da suke.

07:00am dankareriyar gold watch dake É—aure a hannun su tayi kara lokacin guda alamar awa É—aya ta karu a kan lokaci, kallon juna suka yi, kusan a tare suka ajiye karafunan hannun su, kowa ya sanya hannu yana kokarin kashe karar watch É—in, dankareriyar gold watch ne mai bala'i kyau da tsada iri É—aya ba abun da ya raba watch É—in, ko ina zasu je watch É—in na hannun su basa rabuwa da shi sai dai in zasu yi barci ko zasu yi wanka shi ne suke cirewa,

Tsai da karar watch É—in sukayi a tare, dai dai lokacin jibga jibgan Bodyguard na su guda huÉ—u suka shigo wajen hannun su É—auke da plate masu É—auke da cup na ruwan lemon wadda masu motsa jiki ya kamata su sha idan sun kammala motsa jikin nasu,

Rabuwa bodyguard ɗin suka yi, biyu suka nufi wajen Michael biyu kuma suka nufi James, cikin girmamawa suka miƙa musu plate ɗin, ba musu kowan nen su yasa hannu ya ɗauki cup ɗin suka kafa a ɗan karamin bakin su.

Cikin ƙan ƙanin lokaci suka shanye lemon ɗin tas, tare da mai da cups ɗin saman plate dake hannun bodyguard ɗin, daman ka idar motsa jikin kenan shan 1 cup na lemon idan an kammala.

Bayan bodyguard ɗin sun fice ne Michel ya kalli James yace "Photo copy zan je na shirya na wuce school yanzu" ba tare da James ya kalle sa ba yace "Ba za dai ka dai na ce min photo copy ba ko?" Miƙewa Michael yayi yana faɗin "To ai kai photo copy ne da gaske dama aikin sojan kawai kai ma ka shiga da ya fima yawon ban zan da kake ɗin nan kullun gaka wajen partyn abokai, ka gama school kana zaune" shiru James yayi ba tare da ya sake magana ba, sai mamaki yake wai Michael ne yake ce masa mai yawon banza to ba gwara shi ba ya samu ya kammala school ɗin, aiki ne dai kawai bai fara ba kuma baya ra'ayi yin koma ne hutu kawai yake sonyi a gida shi kuma fa, wuce wa Michael yayi ya fice daga wajen ya nufi bedroom na shi.

A hankali shi ma James ɗin ya miƙe ya wuce nashi bedroom ɗin dan yaje yayi wanka.

After some hours.

James ya fito sanye da wandon jeans baki da t-shirt navy blue masu bala'i kyau da tsada sai kamshi yake zubawa, kai tsaye parking space ya nufa, yaje ya shiga motar sa kirar *Bugatti centodieci* ya tayar
Chapter 44 · 0% Book details