Sashe 90
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita dai amsa masa da to kawai tayi amma ba wai dan haji daÉ—in hakan ba, tayi shiru tana tunanin ko dai ta kira su Aafia ne, duk ta shiga damuwa tana kewar yan uwan ta, sai dai idan ta kira su Aafia ba wani jin daÉ—in su take ba, saboda basa mata magana mai daÉ—i.
Haka tayi shiru tana tunani, kamar a mafarki ta fara ganin wutar palon su na kawowa yana ɗauke wa, da farko ta ɗauka rikicin yan nepa ne dan haka bata wani damu ba, sai kuma taga abun gaba yake yaki tsayawa, har wani shekin wutar yake, yana abu kamar shocking na nepa, tsoro ta fara ji, jikin ta ya fara kerma, sai zare ido take, a hankali ta miƙe tana takawa kamar wadda koi ya fashewa a ciki, kai tsaye saman bene ta nufa, tana tafiya tana jin motsi kamar ana bin ta a baya, ji tayi kamar ta fasa ihu, sai dai kuma ta kasa yin ihun, sosai ta tsorata, ganin ta kusa haurawa sama ne yasa ta kwasa da gudu, ta nufi betroom ɗin Ammie.
Ko da tazo zata shiga bedroom É—in sai kofar bedroom É—in ya rufe kan sa da kansa, ihu ta saki tare da juyawa da gudun gaske ta nufi bedroom na Abba, nan ma ko da tazo zata shiga, sai kofar bedroom É—in ya rufe kan sa, nan fa tsoro ya kara dira mata a ran ta, jikin ta har wani kerma yake, sai zaro ido waje take, ta rasa ina zata sa ranta, tana tsaye a kofar bedroom na Abba kamar a mafarki gaba É—aya wutan gidan ya É—auke, wani bala'i duhu ya gauraye ko ina, a guje ta nufi bedroom nata tare da yin wurgi da wayar ta, da karfi ta fara kiran Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, tana furta hakan kan kace me, wutar gidan ya dawo, haske ya gauraye ko ina, hayewa saman gadon ta tayi, a É—ari ta shige cikin bargo tana kuka kasa kasa, tana ambato sunan Allah, da karfi ta runtse idon ta yau taga tashin hankali da kyar barci yayi awon gaba da ita, har tayi barci jikin ta bai dena kerman tsoroba.
💞KATSINA💞
Ko da Jehan suka isa Hospital ta sanar da gwaggo abun da ke faruwa, sosai gwaggo ta shiga damuwa, ga mum kuma har yanzu bata ko motsi, bata san in da kan ta yake ba, sun zauna jugum jugum a harabar hospital É—in sun rasa madafa, ban da sunan Allah ba abun da suke ambata a ransu,
kamar daga sama sukaji sallama a ta bayan su, gwaggo Jehan Sadiq har suna rige rigen juyawa
Sadiq ne kawai ya iya amsa sallamar, tare da miƙa wa matashin hannun sa suka gaisa, "idan ba damuwa zan iya zama, dan ina son magana da mama ce" matashin yayi magana yana kallon gwaggo, kallon gwaggo shima Sadiq ɗin yayi yana jiran suji me zata ce
Da hannu gwaggo ta yiwa saurayin nuni da wajen zama ba tare da tayi magana ba, kasan cewar matashin ba zai fi sa'an Sadiq ba a haihuwa, shi yasa gwaggo bata damu ba.
"Mama sunana Ibrahim, ni ma'aikacine a super restaurant, wadda aka buɗe kwannan nan, nasan kun san restaurant ɗin, to a takaice dai, daman an baki aikin samo yara yan mata wayan da zasu dace da aiki a wajen, to tun jiya da na shigo hospital nan, naga wannan yar taki a fiska ta dace da irin wadda muke buƙata, sai dai ta fannin karatu kuma zamu mata jarabawa, idan ba damuwa ina muku tayin aikin" cewar Ibrahim, yayi maganar yana karewa Jehan kallo, murya a dashe gwaggo tace "Muna cikin damuwar da ba zamu iya yin wani abun ba yanzu, ita kan ta yarinyar ba zata iya yi muku abun da kuke buƙata ba, duk da ma bamu san a kan wani restaurant kuke magana ba" Sadiq ne ya ansa zancen da cewa "Gwaggo ni nasan restaurant ɗin yana da kyau sosai kuma sabo ne, babban restaurant ne, wlh da Jehan zata ansa tayin su zai taimaka muku sosai" da sauri Ibrahim ya ansa zancen da cewa "Sosai mama wlh mai gidan mu yana da kirki sosai, kuma kinga sabon restaurant ne zata ji daɗi aiki damu sosai" kallon Ibrahim da kyau gwaggo tayi kafin tace "ba wai munki aiki bane, a'a muna cikin damuwar da ba zata iya yi muku abun da kuke bukata ba" "Mama menene damuwar taku?" Cewar Ibrahim, Sadiq ne ya bashi labarin halin da Mum ke ciki, yana magana Jehan na kuka gwaggo na rarrashin ta.
Shiru Ibrahim yayi kafin yace "To nawa ne yanzu ya rage kuɗin" da sauri Jehan ta bashi amsa, tana sharan kwallai "500k saura kuɗin gida da muka sayar, sai kuma 200k da daman already yana cikin account ɗin" "idan aka haɗa ya zama 700k kenan ko?" Cewar Ibrahim, da sauri Jehan ta gyaɗa masa kai, "to nawa daman ake buƙata wajen aikin nata?" Gwaggo ce tace "Dr yace mu tana ji kuɗin aiki kawai 1.5 sai kuɗin jirgin fita waje" jinjina kai Ibrahim yayi kafin yace "Zan iya cika muku amma aro bashi, idan ta fara aiki a restaurant ɗin mu, 40k za'a na biyanta ko wani wata, to idan an biyata ni zan rinƙa cire 20k a ciki ina barin mata 20k tana taimaka muku a gida, har Allah yasa ta gama biyana kuɗi na" da murna su gwaggo suka rinƙa zuba masa godiya, a tunanin su dan Allah ya musu hakan, sai dai basu sani ba idan ya kai Jehan kuɗin da za'a bashi sai ya fi haka, dan mai restaurant ɗin ne yace masa ya samo masa yan mata kyawawa masu jini a jika, wayan da kyan su zai rinƙa jawo masa costumers, shi yasa Ibrahim tun da ya kwalla ido yaga Jehan shikenan, har da hoto ya ɗauke ta bata sani ba, ya turawa mai gidan nasa, aikuwa mai gidan nasu na gani yace Jehan tayi ya kawo ta zasu bashi 500k, dan kyan Jehan dole jama'a suyita tururuwan zuwa cin abinci, mu sammanma matasa da manyan masu kuɗi, sai dai abun da mai gidan nasu bai sani ba, Jehan ba kamar yadda suke tunani bace, dan bata da fara'ar da zata ja musu costumers kamar yadda suke tunani, sannan bata daukan raini bata ɗaukan wulakanci haka zalika tana da raini da kirman kai ga izza, sannan tana kallon kowa kamar a karkashin ta yake, saboda yadda ta taso a gida lokaci daddyn su naman.
hmmm akoi cakwakiya a wannan restaurant É—in yasin, muje zuwa.
Ibrahim da kan yaje ya muÉ—e musu motar sa kirar *Corolla* suka sanya mum gidan baya, suka shiga suka wuce babban Hospital sai daÉ—i Jehan take ji, shima Ibrahim sai daÉ—i yake ji, zai samu kyautar 500k daga ogan sa.
A takaice dai sun yi Sa'a za'a iya yiwa mum aikin a kan 1.2 Ibrahim ya cika musu 500k a ka sanya rana, nan da 1 week za'a mata aiki, sai murna Jehan take, ta mance da duk wani bakin ciki da kuncin da take ciki, ita dai burin ta ya cika mum zata samu lafiya.
💞KADUNA💞
Su Aafia suna zaune suna hiran su na kawaye kamar yadda suka saba kafin lokaci class nasu ya cika, da sallama wani kyakkyawan mata shi ya kariso wajen su, fari tas da shi kamar balaraɓe, da fara'a Rufee da Amal suka amsa ma shi sallamar, while ita Anisa daman bata damu da yawan magana ba, kuma bata cika shiga harkan mutane ba, kusan halin ta ɗaya da Aafia.
Kusa da Amal matashin ya zauna yana faɗin "Ina babban yarinya ne" yayi maganar yana kallon Aafia, guntun tsaki Aafia taja tana turɓune fuska tace "Tana gida, amma anjima kaɗan zata shigo" murmushi yayi kafin yace "Allah Aafia Umaisha babban yarin ya tana matukar burgeni" dogon tsaki Amal taja tare da miƙewa tsaye tana faɗin "Yanzu Man a gaba na kake cewa wata tana burgeka? Ko kunya ta baka ji ba, wannan ai cin fuska ce" ita dai Aafia shiru ta musu kamar bata a wajen, Anisa ce tace "Kai Amal amma baki da kunya, yanzu dan Mansoor yace Umaisha na burge shi ne zaki ɓata rai? To Umaisha ɗin ba kanwar ki bace? Ai ko dan ganin idon Aafia kya mata kara, kuma ai man ba cewa yayi yana son Umaisha ɗin ba, kawai cewa yayi tana burge sa" Rufee ce ta dakawa Anisa tsawa da cewa "Ke Anisa kiyiwa mutane shiru, ke me kika sani game da kishi? Amal na da gaskiya wannan cin fuska ya mata, akan me zai ce wata mace na burgesa a gaban matar sa In Sha Sha" shiru Anisa tayi taba tanka Rufee ba, ita kuwa Aafia ka san cewar bata cika son hayaniya ba, sai ta miƙe kawai ta bar musu wajen, da sauri Anisa ta miƙe tabi bayan ta,
dogon tsaki Rufee taja kafin tace "Wlh Amal karki yarda son Umaisha yake tun da ya faɗi hakan" ta kai karshen maganar tare da miƙewa tabi bayan su Aafia.
Matsowa gaban sa Amal tayi suna fuskantar juna ta fara surfa masa uwar masifa, ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, cikin masifar nata har da cewa karya sake yi mata magana sun rabu kenan, shi dai man shiru ya mata yana kallon ta, har ta gama ruwan bala'i nata, ta wuce ta bashi waje, tana tafiya ya ɗaure fuska tare da zaro idon sa, nan take idon suka sauya zuwa purple color, jikin sa har kerma yake, ɗan jujjuyawa yayi dan yaga ko a koi mutane, ganin babu mutane sosai a wajen ne, yasa ya faki idon yan kalilan student dake wajen ya buɗe bakin sa, wasu dankara dankaran macizai guda biyu suka fito daga cikin bakin nasa, bakake kirin masu kan faranti, kai tsaye bayan su Aafia macizan nan suka bi, cikin sauri kamar munafiki ya miƙe ya bar wajen tare da mai da asalin kalar idon sa wato fari da baki.