Sashe 14
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune take saman kujerar table dake cikin E,library dake cikin Greenfield university kaduna tayi shiru, kan ta na kan wani book da take karan tawa ga wayar ta da key motar ta a gefen ta jakar ta kuma yana ɗayan gefen nata, cikin takun ƙasaita wasu haɗaɗun yanmata su uku suka shigo cikin Library'n dukkan nin su suna sanye cikin wandon jeans da t-shirt sun zubo gashin dokin nan har baya kamar nasu, kai tsaye wajen Aafia suka nufa suka zauzzauna saman sauran kujerun dake table ɗin da Aafia ke zaune kallon su ta kasan ido Aafia tayi kafin ta ɗago kai tare da cire katon glass ɗin dake face nata tana faɗin "Yan mata ya kuke?" Ɗaya daga cikin sune tace "Yar Alaji ko in ce hajiya da kan ta tun ɗazun muke neman ki bamu gan ki ba can muka haɗu da Umaisha wajen Masallaci shi ne take faɗa mana kina nan" guntun tsaki Aafia taja kafin tace "Ku dai bari ina da Exam on Wednesday ne that's why nake karantun" ɗaya daga cikin sune tace "Ke dalla Rufee ba wan nan ba mu yanzu Afi baby ki faɗa mana ya kika yi da wan nan shegiyar kwailar Amaryan Abbin ku nan?" Turɓune fuska Aafia tayi tana turo baki kamar biro tace "Rabu da shegiya wai ni zata wa iskan ci jiya har da wani zuwa bedroom na dan munafurci tana wani cemin wai mu haɗa kai mu zama abu guda mu zama friend hmm zata yi bayani ne Allah sai ta bar gidan nan because I don't like her at all I hate this woman over wallahi shi kuma Abbi har da wani cewa zai kawo wasu masu aiki dan yau na zuba mata gishiri a abinci Allah ba wata house girl da zan bari ta zauna a gida duk wadda aka kawo sai na san yadda zan yi na koreta ita Amaryan ita zata yi girki kuma mu rinƙa bata girkin duk wani aikin da tayi sai na ɓata a haka har Abbi ya gaji ya sake ta mu huta Allah ba wata mai aikin da zata sake zuwa gida tayi aiki ita zata rinƙa aiki dan daman gidan su ai ba bu house girl" ta kai karshen maganar tare da zan dogon tsaki bushewa da dariya Rufee Anisa Amal suka yi suna tafa hannu "Wallahi Aafia karki bata wani dama karki kuskura ki bari ta samu sake a gidan ku idan ba haka ba zata samu ciki ta haihu da Abbi kuma hakan babban abun kunya ne a gare ku a ce kamar Abbi mutun mai manya manyan companoni wadda ake ji da shi a kasar nan ya auri yar talakawa kuma har sun haihu tab kofa ina zaku je in faɗa miki sai an rinƙa dan ganta ku da yaron da zata haifa wani lokaci ma sai kiga ana kwatan cen ku da gidan su amaryan ba da gidan Abbi ba" cewar Rufaidat buga table da karfi Aafia tayi tare da miƙa wa tana faɗin "it can't happen Rufaidat dole Halima ta bar gidan mu ko tana so ko bata so" Amal na kokarin yin magana Umaisha ta shigo da gudu tana faɗin "Aunty Afi, today your famous had accepted the invitation and he spoke on the Tv _CNBC Tv 18 Robin Roberts_ for almost one minute" ta kai karshen maganar tana nunawa Aafia wayar ta dake hannun ta a sukwane Aafia ta ansa wayar tana faɗin "What are you saying Umaisha do you mean yau TGA yayi magana har tsawon minti ɗaya bai tsaya ba" tayi maganar tana zaro ido gyaɗa mata kai Umaisha tayi tana faɗin "Duba ki gani yanzu nima na kunna data na gani sai sharing na video mutane suke yau TGA ya amsa tambaya har tsawon 1min yana magana" waro ido waje Aafia tayi tana kallon video kyakkyawan baturen dake magana cikin kyakkyawar turanci yana sanye da facemark a face na shi "Wow" Aafia ta furta tare da mayar da video daga farko ta sake gani a sukwane Anisa da Rufaida suka mike suka dawo kusa da Aafia suna kallon video taɓe baki Amal tayi tana makakin yadda su Aafia ke mutuwar son wan nan mutumin da wata kila ma bai san da zaman su ba a duniya kullun basu da wani zance sai zancen sa, ganin Aafia bata da niyar dai na mai da video daga farko tana sake kallo ne yasa Amal tace "Wai Aafia ni kam wanene TGA nan ne kullun sai kin dame mu da zan cen sa" cikin sauri Anisa tace "A'a sai ta dame ki dai dan ni ina ga ba wan da ya kai ni son ganin TGA wallahi kome nake idan lokacin kallon News akan Tga yayi sai na bari nazo na kalla ina bala'i son kallon face na guy ɗin nan sai dai kullun idan yan jarida na ɗaukan sa zakiga hoton ko video yana sanye da facemark ban taɓa kallon real face na shi ba sai dai dara daran idon sa light ash masu ɗaukan hankali masu kama da glass dan in ya waro idon na shi ko ya ɗago su ya kalli abu sai kiga kamar glass yana walkiya suma fa idon na shi wani lokaci yana sanya bakin glass ya rufe su, kai amma guy nan lamba ɗaya ne ya haɗu ta ko ina ba abun da yafi burgeni da shi ma irin sai yan jarida sun tasa shi a gaba sun sanya masa camera suna tambayar sa sai sufi 20mins suna jero masa tambayoyi suna jiran jawabi sai ya tattara gaba ɗaya tambayoyin nasu ya basu amsa ɗaya da batafi maganar 5 second ba shi ma sai ya ja musu aji sai yafi 2 mins kafin su samu amsan duk wanda zai ce miki ga kalan voice na guy ɗin nan a Nigeria kai bama a Nigeria ba har kasashen waje to ya miki karya dan ko magana yake ciki ciki yake magana kuma ga face mark a face na shi maganar tasa bata fita sosai kuma ni ban taɓa ganin in da yayi magana na tsawon 1min ba idan ba yau ba yanzu haka ki shiga media kiga yadda jama'a zasu yi ta rushing na kallon video yau yayi magana har na tsawon minti ɗaya" taɓe baki Amal tayi tace "To wan nan kam a wani gari yake? Abuja ko? Kuma ɗan waye a kasan nan? Mawaki ne ko ɗan film? Ni fa tun da kuke wan nan hauka ban taɓa sanin akan waye ma kuke ba kuma ni ba mai kallon News bace ni ko kallon film ma bana yi bare wani News" ta kai karshen maganar tare da gyara zaman ta, girgiza kai Aafia tayi tare da komawa ta zauna tana faɗin "Amal ni zan baki wan nan amsan ni zan faɗa miƙi who is TGA kina jin labarin *The General of the Army* ko baki ji shi ma?" guntun tsaki Amal taja tana faɗin "To ni ina ruwana da army's nifa ba abun da na sani kawai ki bani labari idan zaki bani amma ni bani da wata masaniya game da army's" gyara zama Aafia tayi kafin ta fara magana "TGA The General of the Army kenan namijin da ni banga kamar sa ba a duniya cikkaken gwarzo jarumin maza kaifi ɗaya ne shi ba mai iya tankwara shi Bature ne ɗan ƙasar *UNITED STATE OF AMERICA* a babban birnin*WASHINGTON DC* babban sojane da babu kamar sa duk wani sojoji da kike gani a *Usa* to a karkashin sa suke bafa wani babba bane, bai da shekaru sosai, kawai baiwa ce daga Allah ya ba shi he is 28 years amma akoi shi da farin jini ga kuɗi mulki tarin masoya Allah ya bashi amma fa Kirista ne ba musulmi ba gashi da bala'i izza kafin yayi magana sai ya ɗau wasu mintoci ina ganin kamar shi kaɗai ne wajen mum da dad ɗin sa, dan ɗan gata ne sosai kafin manya manyan gidan Tv su samu damar yin hira da shi suna shan wahala, wan nan gidan Tv da sukayi hira da shi yau ɗin nan ma a ka ce miki sau biyar suna tura masa takardan gayyatar nan, da kyar suka samu yayi accepted na gayyatar ta su yanzu ki shiga media kiga yadda media ta ɗauka an yi hira da TGA, kuma yayi magana har na tsawon 1min amma time to time yan jarida suna ɗaukan sa hoto wani lokaci a church ɗin su wani lokaci kuma a Airport haka idan yayi tafiya ya dawo" Aafia na kokarin ci gaba da magana Amal tace "Shirmen banza to ai na ku kuma kuka san shi iyayen gayyan soɗi ae, na kuka san shi da har kuke mutuwar kaunar sa haka? Mutumin da ba bahaushe ba, Bature kuma Kirista fa wata kilama bai san wata kasa Nigeria ba ku kuna nan kuna haukan banza bai san da ku ba" Cikin sauri Aafia tace "Ni dai a gidan Tv na fara ganin sa sai kuma a wani News da muke kallo ranar an ɗauke sa hoto yana saukowa daga jirgi ni ba ma abun dake burgeni da shi irin idan yana tafiya kiga jibga jibgan Bodyguards suna take masa baya ga wasu jibga jibgan sojoji a gefen sa wow ai na a jiye wan nan video nasa kullun sai na kalla na kasa goge ta kuma na faɗa miki wani lokaci yan jarida na ɗaukan sa a church na su wan nan hirar da kikaga anyi da shi ma kusan sau biyar a kace gidan Tv na tura masa takardan gayyata amma bai yi accept ba sai yau yayi musu bazata ko in ce ya mana bazata amma fa akoi wani guy a tik tok dake posting na video sa time to time har gidan Tv na ɗauka su ɗaura idan zasu yi labarai a kan sa sai su ɗaura wannan short ɗin video nasa karki ga jama'ar dake followed na Account na guy ɗin dake posting na shi a tik tok ɗin nan sunan sa Johnson yana da followas sama da 10 millon duk kuma saboda posting na TGA da yake yi kuma karki ɗauka kullun yake posting na shi a'a wani lokaci yana yin sati bai yi posting na TGA