Sashe 9
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gefen Jehan kuwa tana shiga gidan su Sadiq tayi karo da kanwar Sadiq a bakin kofa zata fito hannun ta rike da murhun da take suyar awara a kofar gida ɗan baya kaɗan yarinyar tayi tana faɗin "Sannun ki da zuwa" ko kallon in da take Jehan bata yi ba ta wuce ta shige cikin gida. Tana shiga ta tufar da yawu ganin gidan caɓa caɓa da ruwa shiru ta tsaya kusa da rijiyar ta kasa ɗibar ruwan dan bata iya ba kuma taga abun ɗiban ruwan yana da girma shiru tayi tana karewa gidan kallo tana kwaɓe fuska. Tana tsaye Amaryan baban Sadiq ta fito daga ɗakin ta shirye cikin atamfa doguwar riga tayi kyau ba karya kallon sama da kasa Jehan ta mata kafin tace cikin harshen turanci "Ke zo ki ɗiba min ruwan" waro ido waje Amaryan baban Sadiq tayi ta ɗan juya baya dan taga ko dai ba da ita Jehan take ba akoi wata a bayan ta, ganin ba kowa ne yasa ta dawo da kallon ta kan Jehan kallon banza Jehan ta mata tana faɗin "Ke dake nake ai kizo ki ɗiba min ruwa nace" kallon uku goma amaryan baban Sadiq ta mata kafin tace cikin harshen turanci ita ma tace "Ke kina da hankali kuwa ni kike cewa na ɗiba miki ruwa kin san wace ce ni kuwa?" Dogon tsaki Jehan taja kafin tace "Thank God ashe dai akoi masu ɗan jin English a kauyen nan ke ni ban tambaye ki ke wace ce ba kuma ban nemi sanin ke wace ce ɗin ba, ruwa kawai nace kizo ki ɗeba min ban son hayani ya" a fusace Amaryan baban Sadiq ta nufo Jehan da nufin wanka mata mari dan ta mata rashin kunya zuba mata ido Jehan tayi tana mata kallon mahaukaciya har ta ƙariso wajen, ganin babu alamar tsoro a face ɗin Jehan ne yasa Amarya taja birki tana kallon ta dai dai lokacin Sadiq ya shigo gidan, da sauri ya kariso wajen yana faɗin "Amarya lafiya?" Kallon sama da kasa amarya tayiwa Sadiq ɗin kafin tace "Ban sani ba" san nan ta juya harshen cikin harshen turanci tace da Jehan "Ke ɗauki bokitin ki, ki bar gidan nan kuma daga yau karna sake ganin kafar ki wai da sunan kinzo ɗiban ruwa gidan nan kina jina ko?" Guntun tsaki Jehan taja kafin tace "Da ba a son rai na nazo ɗiban ruwan nan ba amma tun da kika ce haka to ki sani daga yau kullun sai nazo ɗiban ruwa in ga uban da ya isa ya hanani" ganin Jehan bazata daku a hannun ta bane yasa ta juya fuuu ta wuce ɗaki tana masifa "Wallahi bari shi ma baban Sadiq ɗin ya dawo dole ya hanaki zuwa gidan nan har kaman ni ina faɗa yau wata tana bani amsa ni da duk gidan nan shakka ta ake nasan maganin ki" kallon Sadiq Jehan tayi kafin tace "Who is she?" "Kin mantane nace miki bana jin turanci" sadiq ya bata amsa guntun tsaki taja kafin tace "waye ne ita" murmushi Sadiq yayi yana faɗin "Cewa zaki yi wace ce ita" kallon sama da kasa ta masa kafin tace "To koma me tun da ka gane nufi na just amsa me kawai" "ita ma maman mu ne" waro dara daran idon ta waje Jehan tayi ta sanya hannu ta tana gwada tsawon Amarya a iska tana faɗin "How? Za ace wan nan yar Small yarinyar ta zama maman ku ba ma sister ku ba" hannu Sadiq yasa ya ɗauki guga ya fara ɗiban mata ruwan yana faɗin "Eh matar baban mu ne itama da ita da maman yarinyar da take waje tana tuyan awaran nan dukka matan baban mu ne" "Why baban ku zai Auri wan nan small girl ɗin I think fa ka girme ta ko?" "Eh na girme ta kawai dan iyayen ta na da kuɗi ne sai tace baban mu take so shi ne aka aura masa ita bana jin yana son ta amma dai ni ban sani ba tun da ba shiga har kan su nake ba" ya kai karshen maganar dai dai lokacin da yake juye mata ruwa gugan karshe a bokitin nata, Shiru Jehan tayi dan ba abun da ta gane a zancen Sadiq bayan cewa Amarya maman su ne matar baban su. Ɗaukan mata ruwan yayi yana faɗin "Muje na kai miki gida" wucewa gaba tayi da sauri ta fice daga gidan tana tufar da yawu bayan ta Sadiq ya bi yana mai farinciki ko ba komai yau Jehan ta masa magana, ko da ta fito duk matasan dake buga kwallo da Sadiq ɗazun basa nan sun watse kowa ya kama kan sa wuce wa tayi abun ta tana hararar masu wucewa a hanya Babu ko sallama ta faɗa cikin gida yadda ta bar su mum da goggo da maman Sadiq haka ta dawo ta same su saman kujerar da ta tashi ta koma ta zauna tana turɓune fuska "Jehan ina ruwan kuma?" Cewar mum turo baki tayi kamar biro kafin tace "wan can dirty boy ɗin yana kawo wa" ruƙe haɓa goggo tayi zata yi magana Sadiq ya shigo bakin sa ɗauke da sallama da fara'a mum ta amsa masa tana mamaki yanzu daman Sadiq Jehan ke cewa dirty boy oh Allah "Mama ai na zan juye muku ruwan?" Sadiq ya tambaya kakalo murmushi dole Mum tayi kafin tace "Ajiye min a kitchen babana" da azaman sa ya karisa cikin kitchen ɗin ya ajiye ruwan ya fito dai dai lokacin goggo ke tambayar Jehan "Wai babyn dady me ya faru kike ta ɓata rai haka ne?" Murmushin Sadiq yayi yace "Ita da Amarya ce ban dai san me ya haɗa su ba na shigo na samu amarya ta nufo ta zata bugeta" mum na kokarin yin magana goggo ta rigata a kule tace "Wace amarya kuma? Giya ta sha ne da zata ce zata bugi baby Jehan?" Kallon maman sa Sadiq yayi kafin yace "Kiyi hakuri gwaggo" miƙewa gwaggo tayi tana faɗin "Ba wata zancen hakuri sai naji dalili, akan me zata ce zata bugi Jehan" shiru maman Sadiq tayi ita kuwa mum mamaki take wai duk wahalar da suka shiga gwaggo bata sauya ba akan Jehan, cikin sanyin murya mum tace "Aunty A'isha kiyi hakuri mana tun da bata bugetan ba" a fusace gwaggo tace "A'a gaskiya ba zan hakura ba idan na barta gobe ma zata sake yunkurin tabata ne gwara na dakatar da abun tun yanzu kai Sadiq muje in ga wace isashiya ce wan nan" "Matar baban mu ne" Sadiq ya bata amsa yana kallon maman sa "Dan matar baban kune sai ta yi yunkurin taɓa Jehan tana da hankali kuwa?" Shiru suka yi gaba ɗayan su ita dai mum idan da sabo ta saba da halin gwaggo da Jehan dawo da kallon ta kan maman Sadiq gwaggo tayi tana faɗin "Zan hakura ne kawai saboda mutuncin ki da kirkin ki amma ku faɗawa baban Sadiq ya jawa matar sa kunne idan ta kuskura hannun ta ya taɓa jikin Jehan to zata yi danasanin mai girma a rayuwar ta" ta kai karshen maganar tare da komawa ta zauna tana ɗaure fuska "Mum zan iya tafiya ko in karo muku ruwan?" Cewar Sadiq girgiza kai mum tayi tana faɗin "A'a babana ya isa muna godiya sosai Allah ya albarkaci rayuwar ka" "Amin mum amma dan Allah mum idan kuna buƙatar ruwa ku kirani zan ɗebo muku ban son Jehan ta rinƙa zuwa gida dan amarya bata da mutunci ko kaɗan gashi duk gida ba wan da ya isa ya mata magana dan tana takama baba zai iya komai akanta zai iya koran kowa a gidan saboda ita shi yasa take abun da ta ga dama" ya kai karshen maganar tare da wucewa ya fice daga gidan kallon maman Sadiq da kyau mum tayi damuwa ne karara a bayyane a kan face ɗin ta Allah sarki gata mace mai hakuri da kamala "Maman Sadiq abun da Sadiq ya faɗa haka ne?" Gyaɗawa mum kai maman Sadiq tayi kafin tace "Haka ne" miƙewa Jehan tayi ta wuce ɗaki a ranta tana faɗin "Ko me su gwaggo kuma suke cewa oho" "Maman Sadiq me ya sa hakan to? Ba kece uwar gida ba? Ko dai akoi wata ce kafin ke?" Cewar gwaggo shiru maman Sadiq ta ɗan yi kafin ta fara magana a nitse "Da farko ni ka ɗai ce a wajen baban Sadiq daga baya ya auro maman Hanan lokacin da tazo gidan ba irin cin kashin da bata min ba shi kuma baban Sadiq yana biye mata ranar girkin ta zata yi girki ta hana ni, ni da Sadiq haka ina ji ina gani idan na masa magana sai yace to shi ina ruwan sa na ansa da kai na mana ni ba mace bace kuma yana sane ba iya faɗa da ita zan yi ba dan tafini tsawo da kiɓa wani lokaci Sadiq idan yaga abun da take min yayi yawa sai ya shiga ɗaki yayi ta kuka dan yana tsoron yin magana yasan halin baban sa zai iya korin sa daga gidan shi ba korin sa da za'ayi ne damuwar sa ba a'a tafiya da zai yi ya barni bai san me zai iya faruwa da ni ba gwara masa ya zauna yana kallo na idan wani abun da yafi karfi na yazo sai ya tare min, haka muka ci gaba da rayuwa cikin wahala ga talauci har ta kai ta kawo baban Sadiq ya dai na bani abinci ya dai na shiga ɗaki na ya dai na kulani kwata kwata, saboda haka Sadiq ya ajiye makarantar sa daga class 5 ya fara koyan aiki a garejin bayan layin nan yana aiki idan ya samu kuɗi yana ciyar da ni Allah da ikon sa Allah ya bani ciki na sake haifan Yusuf daga nan ban sake samun Haihuwa ba har yau dan tun daga lokacin har izuwa yanzu baban Sadiq bai sake kusan tata ba, shi ma Yusuf haka ya taso cikin wahala da ukubar maman su Hanan tun yana yaro take bashi wahala har Allah yasa ya girma gwara Sadiq ma ya samu karatu kaɗan zuwa class 5 shi Yusuf ko kaɗan bai samu ba kasan cewar baban