Sashe 48
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wurgi tayi da wayar gefen ta kamar zata yi kuka tace "Wai wan nan wace irinyar musifa ce" gyara zama Aafia tayi cikin nitsuwa ta fara magana "Umaisha kar ki ɓoye min ki faɗa min gaskiya kina son yaya Akil?" Ɗago ido Umaisha tayi tana kallon Aafia kafin tace "Eh ina son shi, amma bana son abubuwan da yake min, shi fa ba ruwan sa da wani soyayya umarni kawai ya iya bayarwa, sai shegen masifa da izzan na banza" dariya Aafia ta kwashe da shi har da riƙe ciki, a kule Umaisha tace "Me abun dariya kuma?" Cikin dariya Aafia tace "No wonder shi yasa mana kike bin umarnin nasa kuma kika nitsu ashe dan kina son shi ne, hhhhh lallai Umaisha nayi mamakin yadda kike masa biyayya kike biye masa ashe ashe, to zan baki shawara tun da har kina son shi so mai tsanani, dan wan nan so mai tsanani kike masa wadda yake sanya ki jure duk wani haukar da zai miki, to shawarar dai a nan shi ne a hankali ki rinƙa shi gar masa da kalaman soyayya a kan sa ki dai na zama shiru idan kuna waya ki rinƙa yi masa shagwaɓa In Sha Allah zai zo ya fara biye miki yana mayar miki da martani" shiru Umaisha ta ɗan yi kamar mai tunani
Can kuma ta ɗauko wayar ta cikin hanzari tana faɗin "Bari na gwada wani abu mu gani ko zatayi aiki" zuba mata ido Aafia tayi tana kallon ta, layin Akil ta kira, amma bai ɗauka ba sai ya katse kiran nata ya kirata, yana kira ta ɗauka cikin zumuɗi tare da shagwaɓe murya tace "Hello" "Lafiya kika sake kirana?" Ya jefo mata tambaya still dai da wan nan voice na shi mai kamar faɗan, kara shagwaɓe murya tayi kamar wata yar baby tace "Kai yaya Akil to na kira ne naji muryan ka, naji ina kewar kane" da sauri yace "Ke me kuma ya samu voice naki ban fa son munafurci ki ware murya ki min magana hai" zaro ido waje tayi tana kallon Aafia da ta zuba mata ido tana jiran taji ko zasu yi nasara ta ɓangaren shagwaɓa, tunani Umaisha ta shiga yi "wai shi yaya Akil shagwaɓar ma bai sani bane shi dai ko mai da karfi karfi ya sani innalillahi wa inna ilaihir rajiun" tayi nisa cikin tunani ya daka mata tsawa "Ke zaki faɗa min me yasa kika kirani ne ko kuma na kashe waya ta dan ina da abun yi!!" Haɗe rai tayi ciki ciki tace "Sai da safe" bai jira ta karisa ba yace "Idan kika sake kirana babu wani dalili sai ran ki ya ɓaci, dan ba aikin ki nake ba, da zaki rinƙa kirana babu dali kina ɓatamin lokaci bayan ina da abun yi!!" Ya kai karshen maganar tare da katse kiran, ɗaura wayar tayi saman bedside drawer ta kwanta kamar zata yi kuka, tun da Aafia ta ga yanayin face nata tasan basu dace ba dan haka ba sai ta tambaye taba ta kwanta a gefen ta kawai, suka jawa kan su bargo suka lukkuɓu, ba jimawa barci ya ɗauki Aafia ita kuma Umaisha ta jima tana tunanin Akil kafin daga baya barci ya ɗauke ta, asuba ta gari.
________________________________
*KANO*
Kamar dai kullun zaune Jelly take saman mirror chair daddy na gyara mata gashin kan ta, ya mata make up a fuskarta, ba laifi wan nan karon kam make up É—in ya É—an yi kyau, dan ya fara iya make up É—in yanzu, sai murmushi take shi kuma daddy kallo É—aya zaka masa kasan yana cikin matsanancinyar damuwa da tashin hankali duk ya rame ya sauya kamar ba shi ba, ya shiga tunani da damuwa, abubuwa biyu sun haÉ—u masa waje guda, abu farko contract da ya samu dole baban Muneer yace ya ajiye, Abu na biyu kuma baban Muneer yace dole duk abun da yake so shi za'a gudanar a filman na daddy, ma'ana company daddy, sosai daddy ya shiga damuwa a kan hakan dan yasan shi kenan time na rushewar company sa yazo, tun jiya ya rubutawa gomnati takarda a kan ba yason contract É—in nan amma har yau babu reply, yana kuka yana rubuta later, duk ya rame yayi duhu kamar ba shi ba, babban abun da yafi damun sa ya ja masa raman nan, shi ne zina da a ka sashi yayi, wa iya zubilla san nan kuma har da video a ka É—auke sa jama'a suna girmama shi suna kallon sa da mutunci, Allah ya sani shi mutumin kirki ne bana banza ba, yanzu idan video nan ta fita yake nan, innalillahi wa inna ilaihir rajiun wan nan tunanin yasa shi yake ramewa ya shiga damuwa over.
"Daddy what are you thinking?" Jelly ta tambaya tana kallon hotuna a wayar sa dake hannun ta, kakalo murmushi dole yayi wadda yafi kuka ciwo yace "My Jelly ina tunanin kalar kitso da zan miki gobe ne" dariya tayi zata sake magana idon ta ya sauka kan hoton wani kyakkyawan puppy dog dake wayar daddy fari kal da shi, yar kara ta saki tare da furta "wow daddy I love this puppy dog please will you buy for me?" Kallo hoton daddy yayi kafin ya dawo da kallon sa kan face nata, sai zuba murmushi take hakwarar ta kamar gonar audiga saboda hasken su tas suke
ganin murmushi da ke kan face nata yasa shi jin sassauci a ransa yaji sanyi a zuciyar sa cike da so da kauna yace "Yes I will my Jelly" juyowa tayi ta rungume sa tana dariya, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da shafa kan ta, yana mai tausaya mata ya zata ji idan ta girma by mistake taji abun da baban ta ya aikata,
Da tunani cike fal ran sa ya É—auke ta cak suka wuce wajen drawer kayan su, ya ciro mata wasu riga da wandon jeans, sauri sauri ya shirya, tsab suka wuce palo, dan cin abinci.
Already su Zuwaira sun gama shirya musu komai zama yayi ya ɗaura ta saman cinyar sa ya fara bata abincin a baki, tana ci tana wasa haka ya rinƙa biye mata har ta koshi san nan yaci na shi, sai da ya koshi san nan ya miƙe suka koma saman sofa ya jawo system nashi dake saman sofa table ya kunna musu suka fara buga game kamar yadda suka saba, shi dai buga game ɗin kawai yake ba wai dan hankalin sa na wajen ba, baya ma sanin me yake taɓa wa ba, kawai yana yi ne dan jelly taji daɗi tayi farin ciki, ita kuwa sai murmushi take abun ta.
________________________________
*KADUNA*
Cikin dare yinwa mai tsananin gaske ne ya tada Hajiya daga barci, tayi kokarin ta danne yinwan tayi barci, amma ina abun ta ci tura dan yin wa sosai take ji fiye da tunanin mai tunani
kamar zatayi kuka haka ta taso ta kunna wutar É—akin, ba karamin tsorata tayi ba ganin Abba a zaune a tsakiyar gadon
"Alhaji lafiya?" Tayi maganar murya na rawa, kamar zai yi kuka yace "Yinwa nake ji Hajiya" shiru Hajiya ta É—an yi kafin tace "To muje palo muci abincin mana" kasan san cewar sun manta komai ne yasa basu damu ba suka jera a tare suka nufi palon.
Ko da suka isa palon wutar a kunne babu komai shiru palon, kai tsaye table É—in cin abincin suka nufa, suka zauna,
sai bayan sun zauna suka lura da abincin dake saman table É—in
zaro ido waje sukayi suna kallon abincin, kayatattun girke girke ne masu bala'i kyau ga daddaɗar kamshin da abin cin ke dubawa, ga fruits kala kala an yayyanka su an jera a plate ga gasassun gaji sun ji kayan kamshi, wani abincin ma basu taɓa ganin irin sa ba, duk girman table ɗin nan sai da a ka shake sa tab da abinci na alatu masu kamshi da haɗuwa, har da gasassun pig (Alade) gasu ɓera da zomo duk an gashe su sai turirin zafi suke,
Hajiya ce ta fara fasa ihu tana kokarin miƙewa, wayan nan dodannin suka bayyana a sauran kujerun table ɗin suka mai da Hajiya suka zaunar da ita, shi kam Abba daman ban yi yunkurin rashi bama
Nan take Hajiya jikin ta ya fara kerma, ta rintse idon ta bata son haÉ—a ido da dodannin bata son kallon su, dan fuskokin su babban tashin hankali ne sai mai irin zuchiyar Sahabbai zai iya ganin su ma'ana sai mai karfin imani
Kamar daga sama Abba da Hajiya suka ji an fara É—ura musu abincin a baki, a sukwane Hajiya ta wari idon ta, kai tsaye idon ta ya sauka kan mummunar hannun É—aya daga cikin dodannin nan yana dunbutso shinkafa yana danna mata a baki, kallon hannun nasa tayi da kyau, bakin kirin kamar gawayi ga hannun duk datti sai bala'i wari yake ga hannun nasa da girma kamar samudawa
Wage baki Hajiya tayi zata fasa ihu, kamar jira dodan yake, tana waje baki ya danna mata shinkafa a baki, wadda ya sata ba shiri ta haɗi saboda daya danna mata shinkafar ya toshe mata hanci, hakan yasa tayi saurin haɗiye abincin dan ta samu tayi mumfashi, yau ga ɗuren dole, haka dodannin nan suka rinƙa yiwa su Abba ɗuren abinci da wan nan mummunar hannun nasu kamar kwata.
Da sauri Imran ya shigo palon daga Part nashi yana faÉ—in "Abba kune daman a palon? Sai jin motsin nake ina É—aki shi ne nace bari nazo na duba" wage baki Hajiya tayi tana ihu dan Imran yaji ya taimake su amma ina Imran baya jiyo komai, shi ma Abba sai magana yake wa Imran amma Imran baya jin komai, sai ganin bakin su yake suna motsi "Abba lafiya kuke motsa baki kuma baku magana? Ko nazo ne" Imran ya faÉ—a da mamaki a face nashi, ya kai karshen maganar tare da kallon saman table É—in, zaro ido waje yayi yana faÉ—in "Abba me nake gani hakan? Ya naga kamar É—an yen nama da kwari kuke ci?" Ya kai karshen maganar tare da karasowa wajen, sai magana su Abba ke masa shi kuma baya jin komai