Sashe 70
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Almost 30mins suna haka, sannan Rimsha ta samu sauki daga shakan da a kayiwa wuyar ta, a hankali murya ciki ciki tace "Wayyo na shiga uku na" da sauri suka rirriƙeta suna mata sannu, shiru ta ɗan yi kafin ta iya furta "Zan sha ruwa" a takaice yarinyar da suka samu a ɗakin tace "kullun sau ɗaya suke kawo min abinci da ruwa, kuma already sun riga sun kawo na yau na cinye sai kuma gobe dan haka kiyi hakuri kawai" shiru Rimsha tayi tana mamakin me ya hana ta iya kiran sunan Allah kuma gashi tana iya faɗi a ranta amma a fili ta kasa faɗe.
Kallon yarinyar da a ka kawo ta tare da Rimsha yarinyar da suka samu a ɗakin tayi tace "Ya sunan ki?" Da sauri yariyar da aka kawosu tare da Rimsha tace sunana Kausar" yanayin yadda tayi maganar ne yasa yarinyar tace "amma ke ba bahaushiya bace ko?" Gyaɗa mata kai kausar tayi kafin tace "Eh ni bayarbiya ce" jinjina kai yarinyar tayi kafin tace "Ni kuma sunana Alia amma mamana tana kirana da Ayla so kawai ku ma ku kirani da Ayla ɗin koba komai zan iya samun damar in rinƙa tuna mamana" sai lokacin Rimsha ta sanya musu baki a cikin maganar da suke tace "how many days have you being here" girgiza kai Ayla tayi kafin tace "Good 3 years" zaro ido waje Rimsha tayi ta ma kasa magana tayi shiru ta koma ta jingunu da jikin bangon ɗakin tana jin matsanancin ciwon ciki saboda yinwa, haka ta dafe cikin ta da hannun ta dukka biyu tare da runtse idon ta gam tana matsar kwallan dole, zuba mata ido kawai su Ayla sukayi basu da wani hanya da zasu iya taimaka mata fa ce su zuba mata ido kawai, dan suma taimakon suke nema
ba abun da Rimsha ke tunawa sai mum dad gwaggo da Jehan sune duniyar ta, yayin da time to time tunanin GAR yana ratsa tunanin su Jehan a cikin ƙwaƙwalwar nata, haka suka zauna jugum jugum, sai matsar kwalla take wadda a halin yanzu sai tayi da gaske ma kwallan ke fitowa daga idon ta.
_KANO_
Time ɗin ɗaukan Jelly a school yayi daddy ya ajiye duk wani aikin sa ya nufi School nasu dan ɗaukan ta, nan ya ji tashin hankali da bai taɓa jin makamancin sa,
uncle's É—in su Jelly sun shaida masa Jelly bata zo school ba yau, lokaci guda yaga duniya na juya masa dafe kan sa yayi ya fara neman layin su Zuwaira dan yaji ko dai ta koma gida.
Bugu ɗaya Zuwaira ta ɗauka murya sa har rawa yake sai haɗe words yake wajen tambayar ko Jelly ta dawo gida, cikin girmamawa Zuwaira tace masa "A'a bata dawo ba" sake wayar yayi ta faɗi kasa ta tarwatse a wajen, dafe kan sa yayi yana tuna irin rabuwar da suka yi da safe tabbas akoi matsala, kasan cewar shi daddyn Jelly ƙaramin abu yake iya birki tashi hakan yasa numfashin sa ta ɗauke ya zube kasa, kafin ya kai kasa uncle's ɗin su Jelly suka riƙe sa suna faɗin innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
Da sauri suka yayyafa masa ruwa, dogon numfashi yaja tare da saukewa a hankali, ba tare da ya buɗe ido ba ya fara sambatu kamar zararre "why Jelly? Why zaki wa daddyn ki haka, daman tun da naga irin yadda muka rabu da safe na tafi gaba na na faɗuwa naje office ina ta tunanin anya lafiya kuwa ashe dai ba lafiya ba, dan Allah Jelly ki dawo nayi alkawarin sai dai komai ya faru da ni amma ba zan taɓa aura miki wanda baki so ba, dan Allah ki dawo tabbas na miki alkawari Imran zan aura miki" haka daddy yayi ta sambatu, sosai uncle's ɗin su Jelly suka tausaya masa tare da lallaɓashi da bashi baki.
Da kyar suka samu yayi shiru amma ya kasa miƙewa ma bare kuma a je ga tukin mota, wani uncle ɗin su Jelly ne ya jasa a mota suka wuce gida, dan ko magana daddy ya kasa yi, yana bala'i son jelly fiye da tunanin duk wani mai tunani, ita kaɗai garesa saboda ita yaki raɓar kowa, kuma yaki yin wani aure Ita ce duniyar sa ita kaɗai yake ɗaga ido ya kalla yaji daɗi a rayuwar sa itace farincikin sa komai nasa, baya jin zai iya rayuwa a duniyar nan idan har bai gan taba, sai fita da sauri sauri numfashin sa ke masa har suka isa gida.
Fita motar ma ya kasa sai uncle ɗin ya taimaka masa har zuwa bedroom na sa, ya kwantar da shi a saman gado, uncle ɗin na kokarin gyara masa pillow kenan suka ci karo da farar wasika da Jelly ta ajiyewa daddy, cikin sauri Uncle ya ɗauko takardan ya buɗe tare da miƙa wa daddy, daddy jiki har kerma yake wajen ansan takardan ya fara karantawa kamar haka "i love You my dad I love You my world" dogon numfashi daddy yaja da kyar ya iya cewa "ina wayata" da sauri uncle ɗin yace "wayar ta fashe ai tana cikin mota" shiru daddy ya ɗan yi kafin yace "yanzu na tabbatar da zargina, da gaske guduwa Jelly tayi ba sace ta akayi ba, tun da har wasiƙa ta ajiye min" shiru uncle yayi yana mugun jin tausayin daddy, dan tun Jelly na da 5 years uncle yake karantar wa a School ɗin nasu yasan irin soyayyan dake tsakanin daddy da Jelly, yasan irin son da daddy ke wa Jelly.
Sunyi shiri dukkan su Uncle yana son ya koma amma ya kasa faɗa wa daddy zai koma saboda tausayin da daddy ya bashi, suna cikin wannan halin kenan dolly ta shigo ɗakin tana yar kuka saboda ita ma tasan lokacin dawowar Jelly daga school yayi shiyasa tazo mata oyoyo, ba karamin karawa daddy tashin hankali dolly tayi ba, lokaci guda yaji karfi yazo masa cikin hanzari da kuzari ya miƙa ya nufi waje, ba karamin mamaki uncle yasha ba ganin yadda daddy ya miƙe da kuzarin sa kamar ba shi ba.
Da sauri uncle ya miƙe yabi bayan daddy, daddy da kan sa yaja motar kai tsaye sai police station,
yaje ya shigar da report a kan batar Jelly ɗin san nan ya wuce ya sauke uncle a school, ya zarce gidan Radio suma ya sanar da su, daga nan ya fara neman ta da kan sa a cikin garin Kano, gashi wayar sa ta fashe bare ya nunawa jama'a hoton ta, wani zuciya nace masa ya sanar da Imran wani zuciya kuma yace masa a'a ya kyale sa tun da Exam suke kada ya hana shi rubuta Exam nashi, gashi kuma Exam na karshe suke karya samu matsala gwara kawai ya kyale sa tun da sun kusa dawowa sai sun dawo kawai, haka yarinƙa sake sake a ransa yana yawon neman Jelly a cikin Kano bai taɓa kawowa a ran sa ta fita garin Kano ba shi yasa bai yi wani yunkurin neman ta a wajen Kano ɗin ba.
*KADUNA*
A kawo driver ya sauke su Jelly, nan fa Jelly taga duniya dan ko da ta fito daga motar ta kasa gaba ta kasa baya ta tsaya shiru a bakin hanya, ita daman a nata tunanin idan tazo Kaduna kawai gidan su Imran zata gani sai ta shiga amma sai taga a kashin hakan,
Tana tsaye tana ta kallon jama'a dake ta harkan gaban su har rana ya iso in da take, ganin rana ya iso in da take ne yasa ta tsallaka titi ta fara tafiya da kafar ta wadda bata san ina ta nufa ba, tana rungume da School bag É—in tana tafiya.
Sosai tayi tafiya tsakanin ta da kawo har ta fita daga cikin jama'a ba tare da ta ankara ba, tafiya kawai take bata san in da ta dosa ba, bata fargaba sai jin tayi an damki jakar dake hannun ta ta baya, da sauri ta juyo tana kallon su, natasane su biyu, cikin tsawa wanda ya riƙe jakar yace "kawo ta nan" yan waige waige tayi sai lokacin ta lura da tabar cikin mutane, rai a ɓace ga yinwa na damun ta tace "bag ɗin kane da zaka ce na kawo" matasa ne biyu tsaye kai da ganin su kaga yan buguwa dan bakin nan nasu bakin kirin kamar gawayi sabida shaye shaye, san nan ga wani askin yan iska dake kan su sun bar dada a tsakiyar kai.
Wanke ta da wani wawan mari ɗaya daga cikin su yayi, ɗayan kuma ya fisge jakar suka hankaɗe ta ta faɗi kasa suka kwasa a guje suka bar wajen, kuka ta sa mai sauti tana faɗin "wayyo Allah daddy na" da kyar ta iya miƙewa zaune tana kuka tana kiran daddyn ta, yayin da shi kuma daddy ke can Kano yana haukan neman ta lungu da sako.
A wannan halin wani babban mutun mai É—an yawan shekaru yazo wajen ya sameta, irin mazan tashan nan ne marasa mutuncin nan dan kallo É—aya zaka wa face nashi ka gane hakan
kallon tsab yayiwa Jelly nan take ya fara washe baki, kusa da ita yazo ya tsaya yana faɗin "Yan mata me kike yi a nan kuma?" Cikin kuka da muryan shagwaɓa tace "wasu ne suka kwace min School bag ɗina" murmushi mugun ta yayi yana faɗin "ayya sannu ko? Yanzu dai to tashi muje gidana na baki wani jakar" jin yace zai bata wani jaka yasa ta yunkura tana kokarin muƙewa, cikin sauri yasa hannu yana kokarin ɗaga ta, a sukwane ta ja baya cikin tsiwa tace "Don't touch me" ko a jikin sa bai damu ba yace "Okey to tashi da kan ki" ba musu ta miƙe sai shagwaɓe fuska take tana turo baki, shi kuwa mutumin sai murmushi irin na yan bariki yake, ya nuna mata hanya wani yar lungu yace suje, ba musu ta wuce yabi bayan ta sai washe baki yake, yana murmushi irin na yan bariki.