Sashe 18
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Lokacin da Aafia ta dawo gida babu ko sallama ta shigo palon Auntyn su na zaune saman sofa mai zaman mutun 3 tana kallo a makeken Tv plasma dake sama TV stand sanye take cikin doguwar riga na dakakkiyar shadda blue color yasha aikin daga sama har kasa ta yi ɗaurin ture kaga tsiya tayi kyau sosai reras da ita tana zaune tana jiran Abbi ga kayan fruits a gaban ta time to time tana ɗauka taci, kallon sama da kasa Aafia ta mata cikin mutunci Aunty tace "Sannun ki da dawowa Aafia" dogon tsaki Aafia taja ta nufi bene tana faɗin "Babu a house ba dole a ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya a na ɗurawa ba dan ba tsoho ke nemowa ba" ta kai karshen maganar tare da wucewa ta nufi ɗakin su babu ko sallama ta banko kofar ɗakin tashige tana jan tsaki Umaisha na kwance saman gado har tayi wanka ta sauya kaya zuwa wando mai ɗan faɗi kamar palazo da yar riga mai karamin hannu kanta babu ɗankwali tana riƙe da wayar ta tana chatting, ta tada kai da pillow "Ke Umaisha yau kin yi magana da Yaya Irfan ne?" Aafia ta tambaya miƙewa zaune a tsakiyar gadon Umaisha tayi tana faɗin "A'a bamu yi magana da shi ba me ya faru?" Wurgi da jakar hannun ta Aafia tayi a saman gado tare da ɗaura key din motar ta da wayar ta saman bedside drawer ta nufi toilet tana faɗin "Babu komai naji kishin kishin kamar zai dawo ne" waro ido waje Umaisha tayi tana faɗin "who told you?" "I'm on my way coming back to hause Abbi called me dan yaji mun koma gida ne or not nan yake ce min wai kamar yaya Irfan zai dawo" da sauri Umaisha tace "Allah yasa karya dawo yanzu" daga cikin toilet Aafia tace "A'a karma ya dawo gaba ɗaya" "Haba Aunty Afi ya zaki ce karya dawo kuma?" "Eh mana Umaisha karya dawo, uban me yake mana idan ya dawo in ba ya takura mana ba ya samu sanya katon hijabi muje School gashi sai ya samana ido ya hana mu sanya attachment a kai ya hana mu sanya eyelashes wai shi ustaz duk wani jin daɗi na rayuwa sai ya hana mu shi yasa nake masa fatan karma ya dawo yayi zaman sa a can dan ni dai bana bukatar sa" taɓe baki Umaisha tayi tace "A'a ni kam ina son ya dawo amma ba yanzu ba sai mun samu hutu" dogon tsaki Aafia taja dai dai lokacin da take shiga cikin baf na wankan tayi shiru bata sake ce da Umaisha komai ba ita ma Umaisha komawa tayi ta kwanta ta ci-gaba da chatting da take yi
💞💞💞💞💞💞💞💞
KANO
💞💞💞💞💞💞💞💞
KANO