Sashe 7
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
washegari haka su mum suka tashi cikin kunci da jimami a kwana biyu da ɓatan Rimsha har mum tayi mugun rama saboda tunani.
Yauma kamar kullun zaune suke tsakar gida saman tabar ma sunyi jugum jugum kamar wayan da aka aikowa da sakon mutuwa Jehan na zaune daga ɗan gefen su saman yar ƙaramar kujera tana rike da wayar ta tana kokarin yin posting na hoton Rimsha a shafin ta Facebook. Tana gab da ɗora hoton sai maganar mum na jiya ta faɗo mata a rai in da take cewa Aunty A'isha kin san dai Alhaji Shitu ya gargaɗe mu kan zuwa police station ko, tuna hakan yasa gudun karta jawo wata matsala yasa ta ɗago ta kalli mum murya cike da damuwa tace "Mum ina son in shearing hoton Rimsha ya shiga duniya ko Allah zai sa in samu wan da ya gan ta" waro ido waje mum tayi kafin tace "Ki dai tona mana asiri ina ga Jehan kin gaji da zaman duniya ne shi yasa" cikin sauri goggo tace "Karki kuskura kiyi wan nan ganganci yanzu duk wani old account naki na media ma ki sauke sa ki buɗe sabo kuma karki kuskura kiyi posting na face na ki dan kin san dai ba wan da bai san face naku ba a kasar nan" jiki ba kwari Jehan ta sauke hoton Rimsha ta fasa ɗaurawa tayi shiru tare da buga takumi tana tunanin yar uwar ta "Jehan ki tashi ki ɗauki bokiti kije gidan su Sadiq ki ɗebo mana ruwa mu ɗaura girki dan yau duk gidan nan ba mai cash ko biyar" cewar goggo, a sukwane Jahan ya ɗago kai tana kallon goggo mamaki ma ya hana ta magana sai tambayar kan ta take a cikin ran ta "Wai shin mafarki nake ne ko da gaske ne ni Jahan zanje ɗebo ruwa ya Allah idan mafarki nake kasa nayi gaggawar farkawa" ganin tayi shiru ne yasa goggo tace "Jehan dake fa nake ki tashi mana" a kule tace "Wai goggo mafarki kike yi ne? Ni Jahan ɗin ne zanje ɗebo ruwa kina jin me kike faɗe kuwa goggo?" Tayi maganar cikin harshen turanci Kallon ta da kyau goggo tayi kafin tace "Kiyi hakuri Jehan kinga kuɗin hannun mu ya kare ne yau duk gidan nan ba wanda ta tashi da ko sisi" "To goggo ba akoi kuɗi a Account ba? Ai bani ATM zaku yi naje na ciro muku" "A'a Jehan yanzu kuɗin da suka rage manan nan lallaɓasu zamuyi ɗan su ɗan rike mu na wani ɗan lokacin kafin muga me Allah zai yi yanzu duk abun da bai zama dole ba ba zamu rinƙa fitar da kuɗi dan sayan sa ba" Cewar mum "Maryam wai nawa ne ma ya rage a account nakin?" Cewar goggo "Aunty A'isha kuɗin ba yawa kinga mun saya gidan nan mun sayi gado da sauran kayan buƙata bai fi 300k bane ya saura a ciki kinga idan muka ce komai saya zamu yi a yadda zamanin nan ya zama komai ta ninka kuɗin sa wallahi kafin nan da next week kuɗin zai kare" "Hakane Maryam shi yasa nace tun da akoi rijiya gidan su yaron nan Sadiq sai Jehan ta rinƙa ɗebo mana ruwan aiki ko?" Gyaɗa kai mum tayi tana faɗin "Haka ne Aunty A'isha kuma ruwan rijiyar tasu ba laifi wallahi maman Sadiq na da tsabta sosai" mum na rufe baki Maman Sadiq ta shigo da sallama ɗauke a bakin ta a tare mum da goggo suka haɗa baki wajen amsa mata sallama, ita dai Jehan ta buga tagumi tana tunanin yar uwar Rimsha duk wan nan zancen da su mum suke baya shiga kunnen ta, saman tabarmar da suke Maman Sadiq ta zauna suka gaisa cikin girmama juna san nan tayiwa mum jaje tare da fatan Allah ya bayyana Rumsha "Jahan ɗin dady ki tashi ki je mana" cewar goggo kallon sama da kasa Jehan tayiwa goggo kafin tace "Wai ke meyasa goggo baki son zaman lafiya ne? Wai da gaske kike ni zan je ɗiban ruwa?" Tayi maganar cikin harshen turanci goggo na kokarin yin magana mum ta riga ta da cewa "To shike nan Jehan tun da ba zaki je ba bari ni na tashi naje da kai na" ta kai karshen maganar tare da miƙa wa ta nufi kitchen ta ɗauko wata yar bokiti baki na roba ta fito ta ɗauko mayafi a ɗaki, ta na kokarin nufan hanyar fita Jehan tayi saurin miƙewa ta rike bokitin tana faɗin "are you serious mum? yanzu daman da gaske sai kije ɗiban ruwa da kan ki? Haba mum wai me yasa kuke yin hakane okay let me go and withdraw money from my account sai na sawo ruwan ko?" Kallon ta da kyau mum tayi tana mugun tausayawa yaran nata rayuwar da baka saba da ita ba rana ɗaya ka tsinci kan ka a ciki akoi wahalar ɗauka cike da tausayi mum ta fara magana cikin harshen turanci "Jahan bana son ki sake taɓa kuɗin Account na kin nan kinji? Kinga bamu san in da dadyn ku ya ke ba kuma kin san muna cikin haɗari a gaban ki Alhaji Shitu ya faɗimana komai kin san komai kin san meke faruwa kina dai ji Alhaji Shitu cewa yayi mu ɓoye kan mu karmu bari a san in da muke idan muka kashe kuɗin hannun mu waye kike tunanin zai bamu a wan nan wahalar rayuwa da ake ciki ko so kike mu fita nema har a ganmu a kashe mu ne eh? Ina son ki zama mai godiya ga Allah a duk halin da kika tsinci kan ki kin ji ko? Wan nan rayuwa da muke yanzu ma wata aya Allah ya nuna mana da muna zaune cikin daular dukiya da jin daɗi bamu taɓa sanin halin da yan kasan nan suke ciki ba amma kin yanzu ko ba komai mun samu karuwa munga halin da talakawa suke ciki idan Allah ya bayyana dadyn ku kuma Allah ya cika masa burin sa ya ci zaɓe kinga ai zamu faɗa masa halin da talakawa ke ciki ba sai na kusa da shi sun rinƙa masa karya ba" shiru Jehan ta ɗan yi hawaye na bin kuncin ta da kyar ta iya buɗe baki ta fara magana cikin harshen turanci "Mum yanzu shike nan dady ba zai dawo ba wai ma ina yaje ne mum kinga kafin ya fita fa yace min yana zuwa zai dawo da wuri kuma naji da uncle yazo yana ce miki bayi da tabbacin dady zai iya kuɓuta mu dai mu gudu Please mum ki faɗa min meke faruwa menene gaskiya abun da ya faru da dady na ko dai dady ya rasu ne?" "No Jehan ban san in da dadyn ku yake ba amma koma me ina da tabbacin bai mutu ba kuma ina sa ran zai dawo gare mu zai nememu ina jin hakan a jiki na" ta kai karshen maganar tare da sanya hannun ta ta gogewa Jahan hawayen dake bin kumatun ta tana faɗin "Ya isa kukan haka kiyiwa dadyn ku da Rimsha addu'a kin ji ko? In sha Allah zasu dawo gare mu komai zai wuce" rungume mum tayi tana faɗin "Mum ba zan iya dai na kuka ba sai dai na tsagaita" ɗan bubbuga bayan ta mum tayi tana faɗin "Hakane Jehan na san ba zaki iya dai na kuka ba dan uba da yar uwa ba wasa ba amma addu'a shine best thing da zaki rinƙa yi musu yanzu dai ansa bokiti kije ki ɗebo mana ruwa muyi abinci kin ji" ba musu ta ansa bokitin ta saki mum tana goge hawaye ta nufi hanyar fita "Jehan ki dawo ki ɗauki hijabi kin ji ko?" Cewar mum ɗin girgiza kai Jahan tayi kafin tace "No mum ni ban son hijabin nan gaskiya" "Jehan nan fa ba Abuja bane" Cewar goggo shiru Jahan tayi kamar bata ji me suka ce ba ta fice daga gidan kan ta ba hijabi sai wani ɗan karamin ɗankwali mai kama da handkerchief ta ɗaura a kan ta haka ta fice. Sai da ta fita san nan tace "bismillahi tawakkaltu alallah wala haula wala kuwata illa billah"
Ø¨ÙØ³Ù’Ù…Ù Ø§Ù„Ù„Ù‡ÙØŒ تَوَكَّلْت٠عَلَى Ø§Ù„Ù„Ù‡ÙØŒ وَلاَØÙŽÙˆÙ’Ù„ÙŽ وَلَا Ù‚Ùوَّةَ Ø¥Ùلَّا Ø¨ÙØ§Ù„لهÙ
kallon goggo mum tayi kafin ta dawo kusa da maman Sadiq ta zauna tana faÉ—in "Jahan kenan" murmushi maman Sadiq tayi tace "Ai yara sarakuna ne" da yake cikin harshen turanci mum da Jahan suka yi magana hakan yasa maman Sadiq bata ji me suka ce ba girgiza kai kawai mum tayi bata sake magana ba shiru wajen yayi kamar ba mutane dukkan su sun shiga duniyar tunanin.