← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 126

Sashe 82

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wannan shi ne ba É—aya kanin biyu, ba gida kuma ba kuÉ—i sannan ba yiwa mum aiki, tashin sense, muje zuwa yanzu wasan zai fara, karki bari a baki labari.

👹Daular mutuwa👹

Rimsha bata sake fita ba tun ranar da abun nan ya faru tsakanin ta da duna, yau kwana biyu kenan.

Yauma kamar kullun suna zaune cikin ɗakin su, sunyi jugum jugum, ita Rimsha sai faman kokarin ɗaure dark black curly hair ta take, gashin nata na da tsantsi sosai yaki ɗauruwa, ita kuma bata son barin sa a sake haka saboda ƙuran dake ɗakin nasu. Cikin sauri Ayla tace "La Meesha muje mu gaishe da baba, kwana biyu ban je ba" juyo da dara daran sleeping eyes nata Rimsha tayi kan Ayla kafin tace "waye kuma baba?" Miƙe wa Ayla tayi tana faɗin "Zo muje ki gan shi" miƙa wa Ayla hannu Rimsha tayi, Ayla tajata ta miƙe tana faɗin "Meesha kin fini quality fa" shiru Rimsha ta mata ba tayi magana ba, mukowa Ayla hannu itama kausar tayi, Ayla ta kama, ta miƙar da ita.

A tare suka jera suka fita a É—akin, suna fita suka hango Mustapha a bakin kofar É—akin sa yana É—aure takalmin sa da igiya, da yar fara'ar su suka karisa wajen sa, suka gaida shi, shima da fara'a ya amsa musu tare da tambayar ina zasu je, Ayla ce ta sanar da shi wajen baba zasu je "to kuje nima ina zuwa bari na É—an gama aiki na" to suka amsa masa da shi kafin su wuce su shiga É—aya daga cikin É—akunan dake wajen, yanzu sosai Mustapha ke sake musu fuska suyi hira, tun ranar da Rimsha ta masa magana, shi kenan sai suka zama É—aya.

Kusa da wani tsohon mutumi suka je suka zauna, tsoho ne sosai, ya manyan ta, gashi fari tas kamar bature ga dogon hanci da dara daran ido, duk da tsufa da wahala da yake ciki, hakan ba zai hana kaga kyan saba, ga gashin kan nan nasa da ya zama farin saboda tsufa kwance luf mai tsantsi har goshin sa, Rimsha ta sha mamakin ganin mutumin nan, ji take kamar ta san shi, lokaci guda taji kaunar tsohon ya shiga ranta.

Ayla ce ta fara gaishe sa, ya amsa cike da kulawa yana tambayar ta kwana biyu ina ta shiga ta dai na zuwa wajen sa suyi hira, nan take bashi labarin su Rimsha, sosai ya jajan ta musu, kafin suma su gaishe shi ya amsa, sai kallon shi Rimsha keyi tana tunanin ina ta san wannan fuskar, amma ina ta kasa tunawa, amma dai koma me tabbas tasan wannan fuskar.

Suna zaune suna hira har Mustapha shima yazo nan suka ci-gaba da hiran su, baba na basu labarai suna dariya, a nan wata yarinya tazo ta same su, suka ci-gaba da hira..

Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞Star Lady💞

TRIPLET'S💞

*THE BEGINNING*

💞STAR LADY💞

WhatsApp me for more information 09162620621

Episode 25

Kai tsaye *Florida avenue* James ya nufa sai sharara gudu yake da motar sa a saman shinfiɗaɗiyar titin da zata sada shi da*Florida avenue* ya sanya kiɗa na tashi yana tuƙi yana tunanin yadda zai yi da ogan su, dan yanzu sun dawo masa da zancen kashe GAR sabo, kuma sun matsa masa a kan maganar sosai, saboda sun san duk cikin yaran su shi kaɗai ne zai iya yi musu wannan aikin cikin sauri, kan sa ya kulle sosai ya shiga damuwa neman mafita.

Bai ankaraba ya buge wani mutumi da yazo tsallaka titin, a sukwane ya ja wata mahaukaciyar birki har sai da kansa ta bugu da jikin glass ɗin motar, wani irin jiri ya gani lokacin guda, da sauri ya fito daga cikin motar, duk da kan sa sai faman sara masa yake haka ya karisa wajen mutumin da ya buge ɗin, kwance yake saman titi, sai dai da alama bai wani bugu sosai ba, bai ji ciwo sosai ba amma da alama ya samu karaya a kafa, da sauri James ya duƙa duk girman mutumin haka ya ɗauke shi cak, ya sanya shi cikin mota, kasan cewar unguwar na masu kuɗi ne hakan yasa ba hayani ya ba mutane kowa na cikin gida, tunani ya fara yi ina ya kamata ya kai mutumin nan.

Daga karshe dai ya yanke shawara ya wuce da shi gida duk da ya san zai fiskanci matsala daga Michael da Romeo amma bashi da zaɓi dole ya kai shi gida, haka ya ja motar sa da gudu ya juya motar ya koma gida.

Yana yin parking a parking space na gida ya fito ya ɗauki mutumin ya nufi hanyar shiga cikin gida, a guje jinga jingan sojojin dake tsakar gidan suna gadi, suka nufo shi, har suna rige rigen ansan wannan mutumin daga hannun sa dan su taimaka ma shi, ba musu ya miƙa musu dan dama bai son su Romeo su gan shi ya ɗauko mutumin zasuyi mamaki kasam cewar sun san shi da lalaci.

Haka suka shiga palon, a sukwame TGA ya miƙe tsaye yana mamaki, wucewa sojan da ya ɗauko mutumin yayi, yaje ya kwantar da mutumin saman sofa 3 seater sannan ya fice daga palon.

"James who is this man? What happened to him?" Tga ne ya jerowa James wannan tambayar, a takaice James ya faÉ—a masa abun da ya faru na buge mutumin da yayi, nan take Tga ya É—aure fuska sosai, a fusace yace "carry him out from this house!!!" zaro ido James yayi yana kallon ikon god, yana jinjinawa karfin hali irin na Tga, sai kace gidan sa to ko Romeo mai gidan ma ai ba zai ce a fita da mutumin nan lokaci guda ba tun da ni na bugesa da mota, sai ya bari mun masa jinya.

James yayi nisa cikin tunanin da zancen zuci da yake, sai ji yayi Tga ya daga masa tsawa "James I'm I not talking to you?" Yar firgigit James yayi kafin yace "I can't uncle" zaro ash eyes ɗin sa Tga yayi kafin ya wuce ya nufi waje, James na tsaye yana mamaki hali irin na yan uwansa su kwata kwata basa son baki a rayuwar su, inma mace ko namiji duk su basa so, basa son kowa ya raɓe su, sun fi son suyi rayuwar su su kaɗai, gaba ɗaya gidan haka suke ba mai son wani yazo cikin su, basa son mutane musamman Romeo yafi kowa tsanar wasu suzo kusa da su, daga shi sai Michael da Tga sun tsani baki.

Sai tunanin ta yadda zai kare da Romeo a kan mutumin nan yake, gashi mutumin yana sume baya cikin hayyacin sa, zuba masa idon James yayi yana kallon sa.

A fusace Tga ya dawo cikin palon tare da sojoji biyu jibga jibga masu jini a jika, kai tsaye mutumin Tga ya nuna musu yana faɗin "carry this man out from this house" kallon sojojin James yayi suna kokarin ɗaukan mutumin cikin tsawa James yace "Are you mad, get out from here!!!" Cikin fushi Tga yace da sojojin "i said take this dirty man out" kafe su da ido James yayi kafin yace "Okey carry him let me see" shiru sojojin suka tsaya sun rasa maganar wa za su bi, dan duk wanda suka karyawa doka to zasu rasa aikin su, Tga ogan sune a wajen aiki, while shi kuma James sanyin idanniyar ogan kowa a gidan ne wato Romeo, sun gwammaci suki bin umarnin ogan su wato tga a kan su ɓatawa James rai dan gwara musu hukuncin Tga a kan na Romeo, dan haka sai suka juya suka fice daga palon dan sun san halin Romeo a kan yan uwansa sam baya adalci kuma zai iya yin komai a kan Triplets ɗin sa.

Ganin sojojin sun juya sun fice ne yasa Tga ya nufo mutumin da kan sa da nufi ya ɗauke sa ya fitar da shi, yana kai hannun sa zai ɗauki mutumin, a fusace James ya damki hannun nasa tare da turesa gefe guda, rai a matukar ɓace Tga yayi kan James da nufin dukan sa, nan fa James yace bai isa ba, kamar wasu zakuna haka suka fara faɗa.

Da karfi Tga ya kaiwa James duka a gefen ciki wadda hakan ya masa mugun zafi sosai, lokacin guda James ya sauya idon sa sukayi jawur nan fa ya riƙiɗe ya zama tamkar mayinwa cin zaki wadda yayi shekara biyu babu abinci ya fito farauta, nan yafara farauta Tga, a fusace ya sanya dukkan karfin sa ya ɗaga Tga yayi wurgi da shi gefe saman glass table na tsakiyar sofa milk color, nan take table ɗin ta tarwatse, gadan gadan James ya haye kan Tga ya fara kai masa bugu ta ko ina yana gurnanin ɓacin rai, ran maza ya ɓaci gaba ɗaya jijiyoyin kan sa dana wuyar sa sun miƙe sai dukan Tga yake sosai, da dai yaga duka da hannun ma bata masa ba sai ya ɗamko wuyar rigar Tga ɗin ya miƙar da shi tsaye, yana kokarin kai masa naushi a ciki, Tga ya riƙe hannun sa tare da kwashe kafafun James ɗin ya zube kasa, nan fa Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka shima

Kasan cewar James ya samu horon faÉ—a sosai wajen ogannin sa, hakan yasa ya san dabarun faÉ—a sosai, cikin dabara ya juyar da Tga ya haye kan sa ya fara kai masa duka.

kamar wasu mayinwatan zakuna haka suka rinƙa farautar junan su, sai dai Tga yaci karfin James, dan shi horon soja ya samu daga wajen Romeo, hakan yasa yayiwa James duka duk ya farfashe masa jiki da fuska, da kyar James ke mumfashi, amma Tga idon sa ya rufe duka kawai yake kai masa ta ko ina.

Zuciya ta jasa yana neman kashe James ba tare da ya sani ba.
Chapter 82 · 0% Book details