Sashe 10
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sa bai da karfi daman bai da karfi rike mata biyu kawai jaraba ce ni kaɗai ɗin ma da kyar yake iya ciyar da ni sau biyu a rana amma haka ya rufe ido ya kara Aure, Sadiq yana iya bakin kokarin sa wajen ganin ya kula dani da kanin sa muna a haka har maman Hanan ta samu cikin Hanan yarinyar nan dake tuyar awara a kofar gidan mu, ita ma tun daga kan Hanan bata sake Haihuwa ba sai dai abun mamakin ita Hanan tana da hali mai kyau ba kamar maman ta ba, muna cikin wan nan wahalar yazo mana da wata zance wai an bashi mata wata yar mai kuɗi ce ta ganshi tace shi take so dan haka Aure zai kara a lokacin nayi kokarin nuna masa illar hakan yaki yarda dana matsa yace to na tafi gidan mu jin hakan yasa nayi shiru na kyale sa kasan cewar bani da uwa mahaifiyata ta rasu kuma ba zan iya tafiya na bar su sadiq ba, yarinyar da yace zai aura yarinya ce karama bata wuce Sa'a Sadiq ba dan bata wuce 23 years ba Sadiq ma ya ɗan girme ta na nuna masa illar abun amma ya rufe idon sa yaki shi yaga kuɗi daman gidan da muke cikin nan gidan hayane alokacin sanadiyar Auren yarinyar baban ta ya sai masa gidan ya dawo mallakin sa yarinyar nan tun da tazo shikenan baban Sadiq ya tattara mu daga ni har maman Hanan ya watsar daman ni ya dade da watsar da ni ya tattara ya koma ya tare a gindin yarinyar sai abun da tace ya keyi ko waje idan tace karya fita tofa baya taka ko ina daman ba wani sana'a yake ba itace yake sayarwa a ɗan bayan layin mu baban yarinyar ya saya masa kaya dayawa da abubuwan amfani san nan ya gyara ma yarinyar ɗakin ta an mata ciki da palo har da fenti gashi yarinyar tazo da abubun ta dayawa har da su kayan kallo da su gas da kayan abinci na zamani kullun zata girka kaji da shinkafa bata taɓa tsanmana ba sai dai taci ta ragewa baban Sadiq ya fito waje idan ba wuta yana cin ragowar ta yana washe baki ni ko ajiki na dan Sadiq yana iya kokarin sa wani lokaci idan ya samu kuɗi a garejin su sosai har kaza nima yake sawomin gasashe muci da shi da Yasuf mu ɗebawa maman Hanan da Hanan ɗin ta, maman Hanan ma ta kasa jurewa shi ne suka fara sana'ar awara a kofar gida ɗan su ciyar da kan su baban Sadiq ya sallama mu ba ruwan sa da mu baya bamu ci baya bamu sha bare sutura ko idan bamu da lafiya ya nema mana magani kwata kwata ba ruwan sa da mu damu da babu duk ɗaya ne awajen sa daga ni har maman Hanan ya fita sabgar mu, ko mutuwa zamu yi mu mutu shi ba ruwan sa kullun yana wajen amaryan sa gashi yarinyar bata da kunya ga masifar bala'i idan rashin Kunyar ta ya motsa sai Sadiq na min wanki kaya na sai ta kwaso nata ta zuba masa tace ya wanke idan yaki sai ta sa baban shi, shi kuma gudun ta sanya babansa yasa sai ya ansa wankin nata ya wanke mata Yusuf ne dai baya ɗaukan iskancin ta shi yana da zafin rai sosai ga saurin fushi sau biyu baban sa na korin sa daga gidan saboda ita sai naje na bawa amarya hakuri san nan tasa babansa ya hakura ya barsa ya dawo gidan sau biyu wallahi yana korin sa ni kuma ba zan iya ganin sa yana yawon neman wajen kwana gidajen abokai ba gwara dai duk wuya ya zauna a gaba na ina kallon sa yadda rayuwar yanzun nan ya lalace yaro na gaban ka ma ya kacika bare baya ganin idon ka shi yasa ma bana damuwa nake zuwa na zube a kasa na roki amarya ta sa babansa ya hakura ya bar shi ya dawo, Sadiq da kuke ganin nan sai dai in ce Allah ya bawa yaron nan aljanna wan nan murmushi dake kan fuskar sa kullun dan dole yake yin ta idan kuka tona ciwon dake zuciyar yaron nan sai kunyi masa kuka" ta kai karshen maganar tare da goge hawayen dake idon ta "Tab ɗijam lallai maman Sadiq kina cikin jarabawa to Allah ya baki ikon ci, wannan wani irin zalunci ne duniya ina zaki da mu ya za'ayi ba zamu rinƙa fuskantar fushin Ubangiji ba irin wan nan zalunci har ina, ace mutun sai son abun duniya ka haifi yara ba ruwanka da su ba ruwan ka da cin su shan su suturan su bare tarbiyyar su ka zubar da su har ma da matan ka wan nan wani irin abu ne wan nan zamani Allah ka kawo mana sauki" cewar Mum "Amin" maman Sadiq ta amsa da shi ita dai gwaggo shiru tayi abun duniya sun taru sun mata yawa akai shiru wajen yayi ba wanda ya sake magana ita kuma Jehan tana ɗaki tana latsa waya.