← Book details Triplets Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 126

Sashe 3

Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Fusata iya fusata Yusuf ya fusata da abun da Jehan ta musu yarinya yar karama zata tsaya tana faɗa musu magana cikin kunan rai yace "Yaya Sadiq muje dan Allah idan ba haka ba zan iya sumar da yarinyar nan" kallon banza Jehan ta watsawa Yusuf ba tare da tayi magana ba, juyawa Sadiq yayi yana kokarin yin magana, Mum ta fito dan duba su tun da taji shiru shiru gashi har an gama sallar mangariba, ganin mum yasa Sadiq ya ɗan sunkuyar da kan sa kasa dan tun da yaga Jehan ya ji ya fara jin kunyar mum "Mama wallahi mun duba bamu ga yarinyar nan ba" Salati Mum tasa tana kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa "They are lying Mum ina zata je da za suce basu gan taba" Yusuf ji yake kamar ya kwashe ta da mari dan haushi ita kuwa sai kallon rai ni take musu ko shakkan su babu a idon ta bare tsoro "Bayin Allah ina ne police station na ku bari na kai Report tun wuri, cikin nitsuwa da girmamawa Sadiq yace "Mama kiyi hakuri zuwa da safe sai muje amma da zakiji shawara ta da baki je police station ba dan last 2 weeks aka sace wata yarinya a nan kin san zaɓe ya kusa haka iyayen ta sukayi ta yawon zuwa police station ƴan sanda suna anshe musu kuɗi basa masu aiki kin dai san yadda kasan nan ya zama yanzu sai a hankali ba talakawan ba ba masu kuɗin ba kowa baya son gaskiya mafi yawancin su kan su kawai suka sani amai ma kon ki kwashi kuɗi ki kai wa yan sanda gwara ki ɗau kuɗin ki kai masallaci a sayi buta ayi sallah ayiwa yar ki addu'a sanna ki biya kuɗi a miki saukan Qur'ani mai girma dan Allah shi ka ɗai ne mafita, a yan kwana kin nan an sace yara zasu kai 3 a layin nan" Jin haka yasa hankalin Mum ya kara tashi sosai dan atunanin ta Rimsha sai dai ta kauce hanyar gida ta sauya hanya bata taɓa tunanin za'a iya sace ta ba amma jin bayanan Sadiq yasa hankalin ta yayi mugun tashi cikin ruɗu da fargaban in da Rimsha take tace "Yaro muje yanzu nan afara yi mata addu'a ka kai ni in da malaman ku suke mu baki ne a garin nan bamu san kowa ba" "Mama ki bari sai da safe mu kara dubata zuwa azahar tun da ku baki ne tayu ba sace ta akayi ba ɓata hanya tayi idan mun dubata gobe zuwa azahar bamu ganta ba sai mu fara rabawa malamai kuɗi su fara addu'a" shiru Mum tayi kamar mai tunani zafafan hawaye ne suka fara bin kuncin ta da yake wajen ya fara duhun mangariba su Sadiq basu lura da hawayen da take ba, ita dai Jehan sai kallon ban za take musu a duhu tana yamutse fuska tare da ɗage dogon hanci tan nan dan bata gane abubuwan da su Sadiq ke tattaunawa da Mum ba dan ba wani jin Hausar kirki take ba sama sama ta iya shi ma sai idan ita tayi kayan ta take gane me take faɗe idan Hausa ta wuce zo tafi zauna ina zuwa zansha ruwa da sauran kananan word to ba wani ganewa take ba. Da kyar mum ta iya cewa Sadiq "Bawan Allah ya sunan ka? kuma inane gidan ku dan gobe nazo muje neman nata tare" Murmushi Sadiq sarkin murmushi yayi kafin yace "Ga gidan mu can mai kofar kwanon nan sunana Sadiq wayan nan biyun kanne nane Yusuf da Sha'aban Yusuf Maman mu ɗaya Sha'aban kuma ɗan kanin Baban mu ne" "Na gode kwarai da gaske Babana dan sunan babana gare ka Allah ya biyaku da gidan Aljanna" murmushi Sadiq yayi yana faɗin "Ba komai Mama sai da safe" ya kai karshen maganar tare da juyawa suka bar wajen, Hannun Jehan Mum ta riko dan su koma cikin gida "Where are we going mum?" harara cikin duhu Mum ta wurga mata kafin tace "cikin gida" "Mum which kind cikin gida kuma? Where is Rimsha what about her?" Shiru Mum tayi dan bakin ciki ji take kamar ta wanke Jehan da mari haka Allah ya kaddara amma ko mai ya faru Jehan da Goggo ne sila "Mum please talk to me now" "Jehan wallahi ki fita ido na idan zaki rabu da wanna shegiyar yaren turawan ki kama Hausa gara miki ki kama yaren ki kina yar fulani shuwa arab Daddyn ku cikakken bafulatani ni cikakkiyar shuwa arab amma dan iskanci baki iya yaren mu ko ka ɗan ba sai aron yare ki bi ki addabi mutane to wallahi tun wuri ki fita harkan yaren yahudawan nan ki kama yaren uwar ki da uban ki kai kaji min ƴa" "Mum what are you saying? why are you shouting anytime everyday" Dogon tsaki mum taja ba tare da ta sake magana ba ta ja hannun ta suka wuce cikin gida dan tasan idan ta biyewa Jehan haukata ta ta zatayi.
A tsakiyar gida suka isko Goggo na alwala sallar issha sakin hannu Jehan Mum tayi tare da wucewa ɗaki abun ta kallon Goggo Jehan tayi tace "My Goggo please where is Rimsha" da sauri Goggo ta ɗago kai tana faɗin "What are you saying Jehan? You mean up til now they didn't see Rimsha?" gyaɗa mata kai Jehan tayi ba tare da tayi magana ba ta nufi cikin ɗaki "Jehan kizo kiyi alwala" cewar goggo "No goggo ba yanzu zan yi sallah ba sai an jima" daga cikin ɗaki mum tace cikin harshen turanci "Wannan ne kuma wane uwar ki baki isa ba wallahi ko ki wuce kije kiyi alwala kizo kiyi sallah a gaba na ko kuma na fito na same ki a wajen" Shiru Jehan ta tsaya ta kasa cigaba da tafiya dan mum bata taɓa mata magana a irin wanna sigar ba juyowa tayi ta kalli goggo "Ni ma dai Jehan awan nan gabar ba zan bi bayan ki ba duk wanda baya sallah bai da wata amfani a duniya da kuma lahira sanna idan baki sallah a kan lokaci idan kin mutu kunama da maciji ne zasu yi gadin ki a cikin gabari ki kuma wutar jahannama zaki tafi saɓanin mai sallah akan lokaci da Mala'ikun rahma ne zasuyi gadin sa a kabarin sa su buɗe masa kofar aljanna ya rinƙa shakan kamshin aljanna sanna ya shiga aljanna" Ta kai karshen maganar tare da mikewa ta wuce ɗaki.

ÆŠaki Jehan ta shiga ta É—auko wayar ta kirar iPhone 14 ta kunna wutar wayar ta dawo tsakar gida ta É—auki buta tana bin butar da kallo aranta tana faÉ—in "Disgusting gaskiya ba zan iya wannan rayuwa ba dole na koma asalin gidan mu" kitchen ta nufa ta É—ebo ruwa a butan ta dawo wajen da goggo tayi alwala, ita ma tayi alwala ta wuce É—aki tana turo baki kamar biro tana kunkuni.
Chapter 3 · 0% Book details