Sashe 11
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KANO
da sallama Dr ya dawo palon, jelly na zaune a wajen da ya barta rungume da dolly har barci ya fara ɗaukan ta, jin sallamar tasa ne yasa tayi saurin waro idon ta waje tana faɗin "Welcome Uncle" murmushi ya sakar mata kafin yace "Yauwa jellyn dady" ya kai karshen maganar tare da zama gefen ta ya sanya hannu ya ansa dolly ya haɗa allura ya fara mata, kuka jelly tasa tare da runtse idon ta tana faɗin "Wayyo Allah na" da sauri dr ya ɗago kan sa yana faɗin "Lafiya jelly?" Cikin kuka tace "Uncle dan Allah kayiwa dolly allura a hankali kaji? Nasan yanzu tana jin zafi" kallon ta da kyau yayi tsabar haushi kamar ya kwashe ta da mari a ransa yana faɗin "Wallahi ba dan cameran dake palon nan ba da kin sha mari yan iskan yara iyayen ku sun lalata ku dan rashin aikin yi irin na iyayen naku yanzu uban ki ya sa kuɗi ya sawo wan nan hauka ga talakawa can suna kwana da yinwa ba irin kuɗin da baya kashe wa kan wan nan ɗan iskan karen duk saboda ke, shigiya da wani fuska kamar anyi ɓarin kunu a cikin kasa" da sauri ɗayan ɓangaren na zuciyar sa yace "A'a Sadiq kai kan ka kasan Jelila kyakkyawa ce ajin farko" tsaki yaja a ransa tare da danna alluran da karfi yayiwa dolly har sai da ta fasa ihu da sauri jelly ta miƙe jin kukan dolly idon ta a rufe ta nufi staircase tana kuka tana faɗin "Uncle idan ka gama ka kirani" yana kokarin jan tsaki sai ya tuna akoi camera a palon hakan yasa yayiwa dolly aiki mai kyau ba dan yaso ba.
Bayan ya kammala komai ya sake dolly da gudu ta haura sama tabi bayan Jelly tana yar ƙara miƙewa dr yayi ya fice daga palon yana jan tsaki a ransa yana tunano irin kyan jelly.
Ita kuwa jelly tana shiga bedroom ɗin dadyn ta, ta haye katafaren gadon sa ta kwanta tana kuka tana yiwa dolly addu'a, bata san lokacin da dolly ta shigo ɗakin ba sai jin ta tayi a jikin ta cikin sauri ta buɗe ido tare da miƙewa zaune nan take murnushi ya kubce mata ta rungumi dollyn ta suka kwanta tare tana murna da murmushi a face nata har barci ya ɗauke ta.
KADUNA
zaune suke cikin wani katafaren palo na alfarma mai ɗauke da manya manyan sofa set masu numfashi, set 2 launin Ash da milk palon ya kawatu iya kawatuwa yaji komai da ake buƙata idan nace zan tsaya zayyana muku kyan palon nan to zamu kwana mu wuni bamu kammala ba, tsala tsalan yan mata ne su biyu kamanin su ɗaya, sai dai babban farace tas karamar kuma chocolate color ce jikin su jikin hutu ne suna sanye cikin shiga iri ɗaya wandon jeans baki da t-shirt pink color kayan sun matse su babban cikin su zata kai 20 years ta zuba kitson uban attachment kanana a kan ta wadda yazo mata har bayan ta, ita kuma ɗayan bazata wuce 18 years ba bata yi kitso ba ta tara gashin ta ɗaure a tsakiyar kai ba laifi tana da gashi har bayan wuya ga gashin nata bakin kirin mai tsantsi da sheki dukkan su ba ɗan kwali a kan su babban cikin su na rike da wayar ta kirar iphone 13 ita kuma karamar tana rike da Samsung A72 suna zaune saman sofa mai zaman mutun 3 ko wacce kan ta na kan wayar ta tana latsawa, da sallama wata yar matashiyar mata ta shigo palon ta sauko daga sama bene tana sanye cikin wata dakakkiyar lace blue da ratsin fari ɗinki bubu gown wuyan ta da hannun ta sanye suke da dankareriyar sarka da abun hannu mai matukar kyau da kyalli tayi kwalliyar ta sosai ta fita ras yar cakwai da ita wankan tarwaɗa ce matar a shekaru bazata wuci 24 years ba kafar ta na sanye cikin takalma flat shoe fari duk in da ta taka sai takalmin yayi kwas kwas har ta kariso cikin palon kai tsaye ta nufi saman katafaren dining table dake shirye da kayan abinci kala kala tana faɗin "Aafia kuzo mu fara breakfast Abbin ku na fitowa yanzun nan" ko kallon in da take basu yi ba suka ci gaba da latsa wayar su suna turɓune fuska idan da sabo ta saba bata damu ba, dan basu tanka taba ta wuce ta zauna saman ɗaya daga cikin kujerun table ɗin tana kokarin buɗe kulolin abinci wani kyakkyawan mutun ya sauko daga saman benen mai ɗan jiki kaɗan fari tas da shi kamar balarabe gashi da kwantatciyar saje da gemu mai ɗan tsawo yana da manya manyan ido kamar bull ga dogon hanci, kaman sa ɗaya da wadda aka kira da Aafia, suna ganin ya sauko suka miƙe da gudu suka nufe sa suna faɗin Abbi oyoyo rungume su yayi tana faɗin "Good morning my Angle's" "Good morning Abbi how was your night?" Cewar Aafia kafin ya amsa cikin shagwaɓa Umaisha tace "Abbi I'm feeling hungry let's go and eat" shafa lallausan gashin kanta yayi kafin ya riko hannun Umaisha suka nufi table ɗin Aafia tabi bayan su lokacin Aunty su ta gama zubawa kowa abincin sa a plate ɗin sa ta zauna tana jiran su kariso, cikin nitsuwa Abbi ya zauna saman kugeran dake kusa da Auntyn su yana faɗin "Amarya barka da safiya har kin tashi?" Turɓune fuska Aafia tayi a kule tace "Ke Umaisha ni zan zauna kusa da Abbi fa" turo baki Umaisha tayi a shagwaɓe tace "Wallahi ba zan yarda ba ai nice karama" taɓe baki Abbi yayi yana faɗin "Ke Aafia baga waje kusa da ni ta ɗayan gefen nan ba ki barwa Umaisha gefen daman tun da itace karama" kallon gefen ido Aafia tayiwa gefen hagu na Abbi in da yake nuna mata ta zauna kara turɓune fuska tayi a ranta tana faɗin "Allah ya kiyaye na zauna kusa da wan nan stupid ɗin" ganin tayi shiru yasa Abbi yace "Umaisha na yi hakuri kizo ki zauna ta site ɗin nan kinji? Ki bar mata nan ɗin" ba musu Umaisha ta dawo ta gefen hanun nasa kusa da Auntyn su ta zauna ita kuma Aafia ta zauna gefen daman sa
a tare su suka jawo plate na abincin su gaban su ita da Umaisha shi ma Abbi ya jawo na shi a nitse ya ɗauki spoon Aafia sai satar kallon sa take ta kasan ido, yana kai abincin bakin sa a sukwane ya miƙe tsaye tare da fitar da abincin yana faɗin "A uzubillahi Halima menene haka?" waro ido waje Aunty tayi tare da miƙewa tsaye ita ma tana faɗin "Me ya faru?" Cikin fushi yace "Tambaya ta kike ki ɗan ɗana abin cin mana kiji yau shi ne ranar ki ta farko da kika fara girki a gidan nan a matsayin ki na amarya mai makon ki farantawa mijin ki rai shi ne zaki min wan nan shirme? Idan kin san baki iya girki ba tun farko me yasa kikace min baki son masu aiki sumin girki zaki min kamar abun kirki eh? Wannan wani irin abune buhun gishiri nawa kika zuba a cikin abincin nan saboda Allah?" Hannu na rawa Aunty ta sa hannu ta ɗauki spoon ta ɗebi abincin dan ta ɗan ɗana taji tana kai wa bakin ta ta fitar a sukwane tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun me hakan kuma wallahi Abbi Ni bansaka gishiri ba a girkina kwata kwata" a fusace Abbi ya juya ya bar palon ba tare da ya sake magana ba miƙewa Aafia tayi cike da rashin kunya tace "Ke idan kin san baki iya girki ba me zaki wani ce zaki yi eh? Yanzu duba asarar abincin da kika yi fa wato dan baki san darajan abincin bako? Dan ba tsohon ki ke nemowa bako? To wallahi kibi a hankali bazaki zo nan kimana shirmen ƴaƴan talakawan nan ba daman ance ku baku iya samun waje ba to ki shiga hankalin ki, ki nitsu ki dai na rawan jiki dan kinga abinci Available a nan babu a house kizo ki fara mana ɓarna kamar wata rat" zuba mata ido Aunty tayi tana kallon ta idan da sabo ta saba da rashin kunyan Aafia sai dai a sati ɗaya da tayi a gidan Aafia bata taɓa mata rashin kunya mai muni da zagi irin na yau ba kasan cewar iyayen ta basu da karfi talakawa ne yasa take hakuri da rashin kunyan Aafia dan kar taje ta kulata Abbi ya sake ta dan tun kafin suyi Aure ya sanar da ita akan ƴaƴan sa zai iya komai saboda sune ma yasa ya jima bai yi Aure ba,
Fuuu Aafia ta wuce ta haye saman bene tana surfa masifa, miƙewa Umaisha tayi ta nufi saman bene tana faɗin "Sorry Aunty sarkin iya girki" ta kai karshen maganar tare da kwashewa da dariya ta haye sama, shiru Aunty tayi ta kasa motsawa daga in da take tsaye tunani take yaza ta ɓullo wa matsalar gidan nan waye kuma ya zuba mata gishiri a girki ita dai tasan kwata kwata ma bata sanya gishiri a girki ta ba, tana tsaye a wajen har Aafia ta fito sanye da wandon jeans ja da riga fari mai dogon hannu ta ɗaura wani ɗan karamin handkerchief a kan ta wadda ya tsaya mata iya goshi kawai ta zubo kitson huɗu gaba biyu ta gefen nan biyu ta gefen nan ta sanya high heel fari a kafar ta tana riƙe da makullin motar ta da jakar ta da waya tazo ta wuce Aunty ta fice daga palon taje ta shiga dan kareriyar motar ta kirar discussion continue ta figi motar da gudu ta bar gidan,
Share fisabilillah ðŸ‘
💋Star Lady 💋
💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞
https://chat.whatsapp.com/DOMGC0F7nAm6qQt6zWFwcf
STAR 🌟 LADY..âœï¸
*💋The beginning💋*
Episode 4