Sashe 21
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Jehan na komawa gida babu ko sallama zata wuce ɗaki Mum tace "Come here" ba musu ta koma ta zauna kusa da mum tana faɗin "here I am" kallon tsab mum ta mata kafin tace "Whare is your fake face?" Sai lokacin Jehan ta tuna da furkar roban da ta sawo hakan yasa ta miƙe da sauri ta shiga ɗaki ta ɗauko ta dawo ta zauna kusa da mum dai dai lokacin gwaggo ta fito daga wanka ta zo ta wuce su ta shiga ɗaki dan shiryawa, mum da kan ta, ta taya Jehan sanya fuskar roban tana faɗin "Ko barci zaki yi karki yarda ki cire kinji" gyaɗa mata kai Jehan tayi, mum ta sanya mata fustar nan take kamannin Jehan ya ɓata, baka taɓa cewa ita ɗin bace, abinci mum ta zuba mata tuwon shinkafa da miyar ɗanyen kuɓewa ta tura mata gaban ta tana faɗin "Dauka ki ci" girgiza kai Jehan tayi kafin tace "Mum I can't eat this food, the food will not be delicious" kasa kasa mum tayi da murya cikin sigar rarrashi tace "My Jehan kina son farincikina na?" Gyaɗa mata kai Jehan tayi ala'amar eh "To buɗe bakin ki kici abincin nan kin ji ko? Idan kika ci I will be happy, idan kuma baki ci ba I will not be happy", a hankali Jehan ta buɗe ɗan bakin ta mum ta sanya mata abincin ji tayi kamar zata yi amai haka ta daure dan farincikin mum ta fara taunan abinci tana yamutse fuska ita kan ta mum tasan Jehan bata saba cin irin abincin nan ba kullum bata da abinci sai kayan zaki da snacks shinkafa ma sai jefi jefi take ci, haka ta rufe ido mum na bata abincin tana tauna kamar mai cin magani, har ta kai ta fara hawaye tana cin abincin, mum na ganin ta, amma ta kawar da kai dan tana son ta saba mata da rayuwar daɗi da wahala, suna wan nan hali gwaggo ta fito shirye cikin atamfa Holland mai matuqar kyau da tsada ɗinkin zani da riga ta ɗaura ɗankwalin atamfar a kan ta, gwaggo na zama Jehan ta faɗa saman jikin ta tare da sakin kuka mai tsuma rai sai lokacin gwaggo ta gane ashe Jehan ce ta sanya fake face ta sauya kamar ba ita ba "Why are you crying baby Jehan?" Sarai gwaggo tasan me takewa kukan, da gangan taki biye mata dan ita ma tana son Jehan ta saba da rayuwar da suke ciki yanzu.
Da kyar gwaggo ta rarrashe ta, tare da lallaɓata, haka ta hakura ta ci abincin har ta ƙoshi, sosai mum taji daɗi cin abincin da Jehan ɗin tayi a ranta ta rinƙa godewa Allah tana addu'ar Allah yasa ta ɗore a haka kullun ta rinƙa ci
Cikin shagwaɓa tace "Mum gobe zanje na wanke kai na a saloon" shiru mum ta ɗan yi kafin tace "A'a da safe zan wanke miki" kwanciya kan cinyar gwaggo Jehan ɗin tayi kamar za tayi kuka tace "My gwaggo ina kewar yar uwata ina so ganin ta ina take? Wani hali take ciki yanzu? Taci abinci ne? Ko bata ci ba Ina daddy na yake? Na san dukkan su shi da Siha na suna kewata suna son ganina su ma" ta kai karshen maganar tare da sakin kuka mai tsuma rai "Jehan ashe baki manta sunan da daddyn ku ke kiran Rimsha ba siha" cewar mum ita kuwa gwaggo hannu tasa tana gogewa Jehan hawaye ta tana kokarin danne nata hawayen kar su zubo ita kan ta mum dannewa take Jehan ta fama mata babban ciwo mai tsanani dake zuciyar ta, sosai Jehan ke kuka tana jero sunan da daddy ke kiran Rimsha idan taci mark ko wani gift a school "My siha My misha My sima My Rasha ina kike a halin yanzu? Me kike yi? Baki san muna kewar ki bane? Da ba zaki dawo gare mu ba haba my Rashi ki dawo ko zafi zai ragun min a rai" da sauri mum ta miƙe ta bar wajen saboda hawayen da take riƙe wa sunfi ƙarfin ta ba zasu riku ba ita kan ta gwaggo hawayen cubce mata su kayi suka fara bin kuncin ta, Jehan ta fama musu ciwon dake zuciyar su, sosai Jehan ta sha kuka na kin ƙarawa, da kyar gwaggo ta iya sai ta nata kukan ta rarrashi Jehan ɗin, ita ma mum sosai ta murji kukan ta a cikin ɗaki har ya isshe ta, kiraye kirayen sallar mangariba ne yasa mum fitowa idon ta duk sunyi ja sun kunbura saboda kukan da tasha haka ta wuce su Jehan ta ɗauro alwala ta shinfiɗa dadduma ta tada Sallah, da kyar gwaggo da Jehan suka iya miƙe wa dan yin alwala jikin su duk ya mutu saboda kukan da suka sha, a tare suka yi alwala har lokacin hawaye bai dai na bin kuncin Jehan ba, haka tana Sallah tana kuka zuciyar ta na mata tsananin zafi kamar zai fashe ya fito waje tana matukar kaunar yar uwar ta sosai.
Bayan sun idar da sallah suka zauna saman dadduma sukayi addu'a sosai san nan sukayi karatun Al Qur'ani mai girma har a ka kira Sallar issha sukayi Sallah san nan suka naÉ—e daddumar Jehan ta É—auka da hijaban su ta mai da É—aki daga nan ta haye gado tana hawaye ta runtse ido tana tuno rayuwar su a baya sosai ta kara shiga damuwa, su mum kuma da kyar suka tsakura abincin sama sama suka ci mum ta tattara sauran abincin ta mayar kitchen, yau ba wani hira da suka yi saboda tuna musu da daddy da Rimsha da Jehan tayi, gwaggo taje ta rufe musu kofar gida kowa ya wuce É—akin sa zuciya ba daÉ—i,
Ko da gwaggo ta shiga É—aki ganin idon Jehan a runtse yasa tayi tunanin ko tayi barci dan lokaci ta dai na hawayen, hayewa gadon gwaggo tayi ta musu addu'a san nan ta kwanta gefen Jehan É—in tare da kashe wutar wayan nata, duk abun da take Jehan na jin ta dan bata yi barci ba kuma bata jin alamar barci ko kaÉ—an kawai tayi shiru ne tana tunanin yar uwar ta.
💞💞💞💞💞💞💞💞
RIMSHA