Sashe 74
Triplets Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Dogon tsaki taja kafin ta ɗauki kiran tare da kara wayar a kunnen ta tana faɗin "Hello" daga ɗayan ɓangaren Akil yace "Ina kika yasar da wayar kin tun safe nake kira?" Hararar wayar tayi kamar tana gaban sa, san nan tace "In school ne shiyasa" "A School ba'a picking call ne?" "Kayi hakuri to" shiru ya ɗan yi kafin yace "Umaisha ni sa'an wasan kine? Har zaki ga call na kiki ɗauka" shiru ta masa batayi magana ba sai faman hararar wayar take kamar yana gaban ta "Okey ba zaki yi magana ba kenan?" Turo baki tayi a kule tace "Kayi hakuri" "Good ya miki kyau next month ina dawowa ki shirya ina zuwa zanzo na ɗauke ki na kawo sadaki" kamar zata yi wata magana kuma sai ta fasa tace "Ok sai kazo ɗin" yasha ruwan mamakin amsar da ta bashi, ita da a baya kullun ita ke tambayar sa yau she zai dawo, idan yace mata ba rana har kuka take masa amma yau yace mata ga ranar da zai dawo ko ajikin ta sai dai tace masa wani ok kawai, tun daga nan ya fahimci a koi matsala amma bai bari hakan yayi affecting na tunanin saba kasan cewar yana da Exam a gaban sa, sai ya tattara komai ya ajiye a kan sai ya dawo kawai ya ɗauki mataki da ya dace, da haka sukayi sallama yana cike da mamakin ta, yayin da ita kuma take ta faman jan tsaki tana faɗin "ɗan damuwa kawai ni zaka cewa zakazo ka ɗauka, hmmm yaro mankaza kazo ka ɗauke ni ɗin mu gani tun da uban ka ya haifa maka ni" sai suruntan ta take yayin da ita kuma Aafia ta sanya Bluetooth a kunnen ta tana jin waka, hankalin ta baya kan Umaisha ɗin ma kwata kwata, bata jin me Umaisha ke faɗe ba.
💞KANO💞
A ɓangaren daddyn Jelly kuwa duk ya rame ya fita hayyacin sa ya sauya kamar ba shi ba, gashi ba wani information da ya samu a kan Jelly, da kyar ya iya samu ya ci abinci, shima yaci ne saboda yinwa dake kokarin yi masa illa, kullun tun safe idan ya fita baya dawowa sai 1 na dare, ya daina zuwa office ban da yawon neman Jelly cikin garin Kano ba abun da yake,
sai neman layin sa Imran keyi amma a kashe kasan cewar wayar tasa ta fashe bai kuma kai ta gyara ba, haka zalika baban Muneer sai neman layin sa yake a kan batun auren Jelly da Muneer dan Muneer na takura masa a kan batun auren, amma ina layin daddy baya tafiya, yazo gida yafi a kirga amma baya samun daddy kasan cewar daddy na can wajen yawon neman Jelly, duk in da baban Muneer yasan zai samu daddy yaje amma shiru ba labari, haka ya hakura ya fara bincike ko dai daddy ya gudune yabar Kano, daddy kuwa yana can cikin wahalar gararin neman Jelly, tun kayan da ya sanya ranar da Jelly ta ɓace bai samu damar wanka ba bare ya canza wasu, dan kwata kwata baya tuna komai sai Jellyn sa.
💞KATSINA💞
ga idon nashi jawur kamar jini manya manyan, kai da gani kasan wan nan yana shaye shaye over, ganin shi ba karamin tsorata mum tayi ba nan take numfashi ta ya ɗauke ta zuɓe kasa sumammiya, su kuwa ko a jikin su, suka danno hasken torchlight na su mai kashe karfin ganin idon ɗan Adam saboda haske, kai tsaye saman gadon suka haska da mamaki sai basu gane Jehan ba kasan cewar tasa fake face, tsawa Nasir ya dakawa gwaggo tare da sanya kafar sa yana taka ta "Ke tashi ki faɗa mana ina Jehan Nawazudden" a firgice gwaggo ta miƙe zaune tana zaro ido
ganin kartin maza a ɗakin su ne yasa ta fara salati tana ambato sunan Allah "ke ina Jehan Nawazudden?!!!" Nasir ya sake tambayar gwaggo, hannu gwaggo tasa tana mutsuke idon ta dan ta samu damar ganin su wanene da kyau, hakan yayi dai dai da farkawan Jehan daga barci saboda hayaniyar da tajine ya farkar da ita, miƙewa tayi zaune tana goge idon ta, kallo ɗaya Nasir ya mata ya gane ita ce Jehan saboda yanayin jikin ta, sai dai yayi mamankin ganin face ɗin ta ya sauya kamar ba ita ba
ÆŠaya daga cikin abokan Nasir É—in ne yace "Ba zaku faÉ—a mana in da Jehan É—in take bane sai mun muku yan kan rago" sai lokacin Jehan ta fahimci meke faruwa
babu ko tsoro a idon ta tace "Ni ce Jehan sai a kayi yaya, uban me kuka zo nema waje na? Ko kun ban ajiya ne?" Tashin sense da mamaki dukkan su suka zuba mata ido yar karama da ita da irin wannan karfin hali haka, to ko dai akoi abun da ta takane, sai yiwa kansu tambayar da basu da amsan shi suke, shi kan shi Nasir yasha jinin jikin sa ya tsorata, gani yake anya ba wani abun da Jehan ta taka kuwa, su kan su su Fadil dake ɓoye a bayi sun tsorata sosai gani irin karfin hali irin na Jehan ko tsoron wayan nan kartin maza bata jiba
Ita kuwa ganin sun mata shiru suna mamaki ne yasa tace "Idan kun tashi faÉ—a min uban da kukazo yi gidan nan sai ku tashe ni dan barci nake ji" ta kai karshen maganar tana komawa ta kwanta, tashin sense ba'a sa maka date
a fusace ɗaya daga cikin su yace "Tafiya dake mukazo yi ma'ana kidnaping naki mukazo yi" kwashewa da dariya gwaggo tayi kafin tace "Amma dai ku mahaukatane ko? Jehan ɗin kukazo kamawa to gata ku ɗauke ta" miƙewa tsaye Jehan tayi tana faɗin "Haba dai dirty Boyz ni zaku yi kidnaping? To muje mana gani nan ai" ta kai karshen maganar tare da dirowa kasa daga saman gadon, sosai Nasir ya kara tsorata, yanzu ya kara tabbatar wa kan sa akoi abun da Jehan ta taka, dan haka kawai ba zata ce su kama ta ba, in kaji makaho yace muyi wasan jifa to dutse ya taka, hakan yasa ya fara ja da baya da baya, yayin da Jehan ke tin karosa tana faɗin "Muje ko" ba shiri suma abokan Nasir ɗin suka fara ja baya baya suna bin Nasir "Gwaggo ɗauko waya kicewa DPO su kariso yanzu" cewar Jehan ɗin
jin haka yasa Nasir ya kwasa a kuje yayi waje, wandon sa na faÉ—uwa ya haye saman katanga kamar biri ya dira waje, yayin da suma abokan nasa suka rufa masa baya
Fadil na ganin su Nasir sun yi waje shima ya fito a guje dan kar DPO yazo ya kama shi, a É—ari suma suka haye katanga suka dira waje.
Suna fita Jehan ta kwaso a guje ta haye saman gadon ta rungume gwaggo tana faÉ—in "wayyo na shiga uku ni Jehan" ita kan ta gwaggo kirjin ta sai dukan uku uku yake, yau taga abun da yafi karfin ta, ashe duk wannan cika baki da suke kirjin su sai dukan uku uku yake a tsorace suke, kawai karfin haline ,irin na Jehan da gwaggo kamar wasu wayan da suka taki wata tsiya ashe duk bogene tsoro cike fal ransu
Kuka Jehan tasa tana faɗin "gwaggo dan Allah mu bar gidan nan kar su sake dawowa wlh tsoro nake ji" rungume ta gwaggo tayi tana faɗin "Ni kai na saura kaɗan nayi fitsari a wando saboda tsoro kawai karfin haline innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah mun gode maka da ka kuɓutar damu daga wannan masifa" jin gwaggo tayi zancen fitsari yasa Jehan ta taɓa jikin ta da sauri dan lokaci da su Nasir ke magana ita ma ji tayi kamar zatayi fitsari a wando saboda tsoro, ashe ta yi fitsarin ma bata sani ba ga kayan barcin ta a jike, kara rungume gwaggo tayi jikin ta sai kerma yake tana haɗa zufan wahala, while ita ma gwaggo sai zufan take haɗawa gashi tana jin fitsari amma tsoron fita take, an kasa samun wanda zai iya miƙewa cikin su ya rufe musu kofar ɗakin saboda tsoro, ga mum kuma kwance a bakin kofa a sume basu sani ba.
Haka a zaune rungume da juna suka kwana, sun kasa rintsawa saboda tsoro gani suke kamar su Nasir zasu dawo, yau sunga bone, ko sallar asuba sun kasa tashi suyi a lokacin da ake kiran Sallah, dan suna ganin kamar su Nasir na waje, har sai da gari yayi haske sannan Jehan ta iya samun dama ta saki gwaggo
jikin su sai kerma yake suka fito waje, ba karamin tsorata sukayi ba ganin mum kwance a kasa, ga hannun ta nan da zanen shatin kafar mutun, da alama a garin gudune É—aya daga cikin abokan Nasir ko shi da kan sa Nasir É—in suka takata a hannu ta.